Sashe 29
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Mariya na kallon Hajja tayi kasa kasa da murya tace "Don girman Allah Hajja in zaki koma gida kice mata ta bi ki ku tafi, kin dai san halin Mama Ladi" Hajja tace "Haba ai kwa bari ko kwana daya tayi ko Mariya, hanya fa ta biyo tun asuba" Aunty Mariya tace "Wllh tana wuce yau a gidan nan ina me tabbatar maki babu inda zata je har sai an gama bikin nan Hajja, ke kadai ce zaki gaya mata taji, kice mata baƙi sun fara yawa a nan kawai ta fito ku tafi gidanki" Hajja tace "Toh amma dai za a bari tayi wanka ta ɗan huta ta ci abinci tukunna ko?" Aunty Mariya tace "Aa dama ai sai ta ci abinci Hajja, ba yanzu nake nufi ba, ba sai in Maheer zai maida ke gida sai ki mata dubara ki tafi da ita" Hajja tace "Toh babu damuwa" Aunty Mariya ta mike ta wuce kitchen don hada ma Mama ladi abinci, mikewa Mayraah tayi ta wuce sama, Hajja na kallon Badiyya dake danna wayarta tace "ke sakko ki karasa zuge akwatin sarkokin nan kada wani abu ya ɓata masu a shiga uku, da ganinsu kasan masu tsada ne, basu yi kama yan kasar nan bane" A takaice Badiyya tace "Ban ga zan iya ba" Hajja ta buda baki tana kallonta, can tace "Toh Allah ya baki hakuri, abinda dai da yatsuna ni ba kuturwa ba, ai ni sai in rufe meye a ciki" Tana fadin haka ta mike tana kokarin rufe akwatin da kyau, Hajja ta ci gaba da cewa "Wani ma ba sai yace hassada kike ma kanwar taki ba, ji fa tun da ake bude kayan nan babu wanda kika yaɓa a ciki balle kice Allah ya sanya alkhairi kema Allah ya dora ki a danshinta, sai wani nukurci da murtuke fuska kike, wannan dai ba yi bane in gaya maki gaskiya, in zaki canza halin ki tun wuri ki canza wllh" Wani fitsararren kallo Badiyya ke ma Hajja kamar zata rufeta da duka, Hajja dai ko damuwa bata yi ba, ta koma ta zauna tana cewa "Dama duk wanda ma zai zo ba sai an sake fito masa da Gwal din ba, ido ba kyau, gwara a fada da baki ace gashi an sa gwal kawai shikenan...." Nan da nan facial impression din Badiyya ya canza jin Hajja ta ambaci gwal, gwal? Wato har da gwal a lefen, Hajja ta ci gaba tana cewa "Gwara a adana sa kawai, kar a sake fitowa da shi, ba a san zuciyar wani ba" Badiyya ta hadiye wani abu da kyar, tana sake bin duk akwatunan da kallo, yanzu har da gold cikin akwatin nan wai? Hajja ta kwalo ma Aunty Mariya kira, Aunty Mariya ta fito daga kitchen tace "Gani Hajja" Hajja tace "Dama cewa nayi kar a kuma fito da gwal din nan a nuna ma kowa don Allah" Aunty Mariya tace "Haba tun ranan da aka kawo kayan ba a sake fitowa da shi ba sai yau da kika zo ai Hajja" Hajja tace "To da kyau, hakan yafi, amma sai nake ga bai ma kamata a bar sa a akwatin ba, wani fa ba don Allah yake zuwa ganin kayan ba sai don ya tafka halin bera" Aunty Mariya tace "Ai ba ciki suke ba dama, na kai sama yana cikin jakata tun ranan, zuwanki ne yasa na fito da shi" Hajja tace "Toh madallah, gwara haka" Juyawa Aunty Mariya tayi ta koma kitchen, Ammi ta sauko downstairs tana kallon Badiyya tace "Badiyya tafi kitchen ki hado ma Mama Ladi shayi, tace shayi da kwai da bread zata ci, akwai full bread a kitchen ba a taɓa ba, sai ki soya mata kwai hudu, Madara da Milo kuma ki kai mata gwangwanin gaba daya, tana nan dakin Mayraah" Badiyya ta mike tace "Toh" Hajja tace "Banda abun Ladi cikin zafin nan me zata yi da shayi kamar shugaban mayu, ga dai tuwo da taushe me kyau anyi nima har na ci" Ammi tace "Gwara dai a kai mata, idan ya so anjima sai a kai tuwon" Badiyya ta nufi kitchen ta sanar ma Aunty Mariya abinda Ammi tace, Aunty Mariya tace "Ita kuma me zata yi da shayi da ranan nan haka?" Badiyya dai bata ce komai ba ta kunna gas zata daura ruwa, Aunty Mariya tace "Toh sai ki soya mata kwai, anjima idan za su tafi sai a zuba mata tuwon a Warmer su tafi da shi" Daga haka ta fice daga kitchen din, Badiyya har ta mance yaushe rabon ta kunna gas, kullum Hajja ce ke masu girki a gida, hatta ruwan zafin nan idan tana bukata yana cikin flask zata tarar Hajja ta cika mata dam, don haka babu hadinta da gas, ta bude fridge ta fiddo kwai hudu ta fasa, ta dau maggi cube biyu ta marmasa a ciki, ta saka gishiri, sai kuma ta dinga kalle kallen kitchen din tana tunanin sai kuma me za a saka a kwan? Ta nufi inda taga Scotch bonnet da albasa ta dau wuka ta fara yanka albasan, da kyar ta gama yankawa don sai hawaye take kamar an buda pampo alamar rashin sabo, ta zuba tarugun manya uku a blender da albasan ta markada su sannan ta juye a kwan ta kada da kyau, tunawa tayi bata sa curry ba tayi maza ta fara duba inda curry yake a kitchen din har ta gani sannan ta zuba a kwan, ta kara beating dinsa, minti biyar ta dauka tana soya kwan, sai da taga kamar konewa yake yi ta maza ta juye a plate, cikin few minutes ta gama hada komai a katon tray sannan ta fito daga kitchen din, Aunty Mariya tace "Sai kace me soya kwai crate daya Badiyya" Badiyya bata ce komai ba ta wuce sama tana murguda baki, tana shiga dakin Mayraah ta tarar da Mama Ladi zaune kasan carpet tana ta mulka Vaseline a jikinta da fuska, sai wani naso take kamar an tsomata a man gyada a fiddo, Mama Ladi tace "Sannu er nan, Allah maki albarka har da kwan aka soyo ko?" Badiyya tace "Ehh bari in dauko gwangwanin Madara da Milon" Mama Ladi ta washe baki tace "To yi maza" Badiyya na fita ba a dau lokaci ba ta dawo ta ajiye ma Mama Ladi gwangwanayen sannan ta zauna gefen gado tana kallonta tace "Wannan Vaseline din da kika lafta fa Mama Ladi?" Mama Ladi tace "To ai ji nayi kamar hunturu kar inje in fara bushewa kamar an tono ni a rami..." Badiyya tayi dariya tace "AC fa aka kunna maki ba wani hunturu ake ba" Mama Ladi tace "Au too, ni dai naji sanyi ba kakkautawa sai nayi zaton hunturu ake a nan" jawo cup tayi ta fara hada shayin, Badiyya ta dawo kusa da ita tayi kasa da murya tace "Mama Ladi kinsan me naji Aunty Mariya na ce ma Hajja?" Mama Ladi ta kalleta da sauri tace "Aa" Badiyya tace "Wllh wai ce ma Hajja tayi don Allah in zata tafi ta tafi dake gidanta su baza su iya da halinki ba gaskiya" A hankali Mama Ladi ta ajiye flask din hannunta tace "Ita Mariyar ce tace haka a kaina?" Badiyya tace "Wallahi, nufinta ke fitinanniya ce baza ki zauna masu a gida ba Hajja ta tattara ki ta tafi dake idan zata koma gida anjima, amma fa bana son ki ce masu komai, kawai dai idan Hajja tace ki tashi ku tafi kice mata a'a ke gidan biki kika zo babu inda za ki" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "Ka ji shegiyar da naci kashinta na ci fitsarinta, a lokacin fa gashin kanta yanda kika san hammatan ɗan iska ba kyan gani, gashi bata da aiki sai kirba kashi a wando ta bar ni da wanke mata, shine take fadin haka yau a kai na? Ni Mariya take cewa a kora a gidan nan sabida ta auri ɗan gwangwan ya kai ta makka?" Badiyya ta fara zare ido tace "Don Allah ni dai kiyi shiru, sirri na zo na gaya maki fa kina neman aji a waje, sannan na riga na gaya maki amsan da za ki basu idan Hajja tace ki bi ta, shikenan kawai ki bar zancen, don Allah kar ki ce na gaya maki wannan maganar Mama Ladi" Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Sai kace wata yarinya zan ce ga abinda kika gaya min, ki tafi kawai ki hada min shayin, madaran cokali shidda zaki zuba min haka nake sha a gida" Badiyya ta hada mata shayin ta ajiye a gabanta, Mama Ladi ta yanko kwai ta kai baki, tana fara taunawa ta maza ta tofar kan farantin tana yamutsa fuska a gigice tace "Wani azzalumin ne ya min suyan kwan nan?" Badiyya tayi tsuru tsuru tana kallonta, Mama Ladi ta mike tace "Na shiga uku na lalace, Badiyya wace shegiyar ce ta soya min kwan nan a gidan nan?" Badiyya ta ɗan daure fuska tace "Me ya samu kwan ne wai?" Mama Ladi tace "Ki ɗan dana ki ji mana er nan, ga uban gishiri ga yaji, wacece tayi min wannan aika aikan, ko dai Mariyar ce?" Badiyya ta ɗan tabe baki tace "Me aikin gidan ce" Mama ladi tace "Mu je ki nuna min ita, to ko dai Mariyar ce ta sa ta tayi min wannan walakancin?" Badiyya ta zaro ido tace "Na shiga uku, don girman Allah ki rufa min asiri Mama Ladi, kar fa kije kice masu ga abinda nace in shiga uku, ke ba a sirri dake ne?" Mama Ladi tace "Yo ni ina ruwana da abinda kika zo kika gaya min, ki ɗan dana kwan nan kiji don Allah" Ammi ce ta shigo dakin tace "Kin idar Mama Ladi" Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Ammi taho ki ga abinda mai aikinki ta soyo ta kawo min saboda ta ga ni ba er birni bace, amma abinda bata sani ba nima ai a birnin aka haifeni" da mamaki Ammi tace "Me aiki kuma, Badiyya ce fa na sa ta hado maki shayin ta soya kwan Hajja" Mama Ladi ta juya tana kallon Badiyya da mamaki, Badiyya ta wani dauke kanta, Mama Ladi