Sashe 117
Mayrah Complete Hausa Novel · about 5 min read
har sannan bata san Maheer ya dawo gidan ba tunda bai shigo da mota ba, Badiyyah ta gani tsaye corridor tana kwankwasa kofar dakin Maheer, Haseenah ta koma gefe tana kallon ikon Allah thinking yaushe Maheer ya dawo, Maheer ya bude kofar yana kallon Badiyyah, Badiyyah ta wani narke murya tace "Yaya don Allah subscription zaka min, nawa ya kare kuma abu ake koya min a WhatsApp for my exams" Haseenah da zuciyarta ya hau tafarfasa ta dinga kallonsu da mamaki, wai dama Maheer ya dawo gidan nan, to ko dai tare ma suka dawo tana can kitchen bata sani ba, Maheer na kallon Badiyyah yace "Ohk, kamar na nawa kike so?" Ta washe baki ta jingina da bango tana wasa da hannun rigarta tace "Yaya ko na dubu goma ne kawai kayi min nagode" Maheer yace "Ohk, naga kin kara haske wani mai kike shafawa ne haka?" Haseenah taji brain dinta ya tsaya cak for some minutes, Badiyyah tayi wani er siririyar dariya tace "Wallahi dama yaya cream din ma ya kare da soap, haka ma turarena sun kare" Yace "Sai a siya maki ai, zan je gidan Hajja yanzu ki shirya sai mu fita tare daga nan sai mu je supermarket din..." Badiyyah na wani blushing tace "To yaya bari in shirya, nagodeee yayana" Daga haka ta shige dakinta da sauri, Maheer ya kulle kofar dakinsa duk suka bar Haseenah wajen a tsaye kamar an dasa ta, tsabar yanda abun ya bugi Haseenah a haka Maheer da Badiyyah suka fito suka sameta tsaye har lkcn kamar statue, Maheer ya wuceta without looking at her, Badiyyah ta kulle dakinta da makulli ta saka makullin cikin jakarta sannan ta yafa ɗan iskan gyalenta ta bi bayan Maheer tana kallon Haseenah tace "Kawata sai mun dawo" Haseenah ta bi ta da kallo har taga sun fita daga parlor, dakinta ta shige da sauri ta xauna gefen gado ta jawo wayarta ta fashe da matsanancin kuka tayi dialing number cousin sister dinta Ramlah, Ramlah na dagawa Haseenah ta kara rushewa da kuka sosai tace "Ramlah wallahi na gaji, na gaji, ji nake kamar xuciyata zai fashe Ramlah, sai yanzu na gane gwara min Mayraah sau dubu a gidan nan tun da ita bazata min wannan abinda Badiyyah take yi a gidana ba kuma shi ma bai wani kula Mayraan a gabana, Ramlah kin ga abinda nake gani a gidana kuwa?" Daga daya bangaren Ramlah tace "Dalla ba wani gwara, ke dai nace ki kwantar da hankalinki ba dai mu mun san abinda muka shirya ba?" Cikin kuka Haseenah tace "Tsoro nake kada tsinanniyar kakan nan tasa tace ya auri Badiyyah tun da an ga suna shiri yanzu, kar ita ma Badiyyar ta zo ta fara sonsa tunda ba hankali isasshe gareta ba, wallahi ina ji a jikina at anytime komai zai iya faruwa idan ban kawo karshen wannan abun ba cikin gaggawa, gashi har yau Maheer yaki kulani" Ramlah tace "Kin ga ni bana gida yanzu haka Haseenah, tun da dai nace ki kwantar da hankalinki ki kwantar da hankalinki kawai, auren nan sai kace bamu yi ba mun fito, Mun fa san kan ko wani tsiya, wallahi Badiyyah da kafarta zata bar maki gida yanda ita wannan mara asalin ma ta bar gidanki" Haseenah na shessheka tace "Amma fa na gaya maki yanda kakar nan tasu ke ji da Badiyyar nan, don ita ce ma ke control dinta wallahi, ni dai wallahi gwara min Mayraah a gidan nan da Badiyyah, Ramlah da na sani da ban hada Badiyyah da malamina ba, kullum da fargaban haka nake kwana nake tashi" Ramlah tace "Kinga ni don Allah zan kiraki in na koma gida" Daga haka ta katse wayarta, Haseenah ta dinga kuka a ranta tana tunanin menene yasa ita dai komai nata bai tafiya dai dai a rayuwar nan, daga wannan sai wannan, ga Maheer ya juya mata baya aure ko wata daya bai cika ba amma sai reto auren nata yake. Throughout daren yau Mayraah bata yi wani bacci ba kasancewar washegari za su fara exams, she is trying by all means taga tayi covering din course din da suke da shi da safe, ita kanta tasan she is not fully prepared for the exam, to amma ta rasa ta yanda zata yi karatun ya shiga kanta, it seems her brain is just weak, a haka dai ta shiga makaranta karfe bakwai da rabi for the exam, rabonta da makarantar tun last week monday, Mayraah ta nuna ma wani lecturer dinsu dake tsaye bakin hall din da za su yi exams ID card dinta sannan ta shiga ciki, seat din da ya nuna mata ta nufa, tana zaunawa sai ga Badiyyah ma ta shigo ta zauna kujeran dake gefen na Mayraah don nan aka nuna mata ta zauna, sai dai akwai ɗan tazara tsakaninsu, a haka aka fara raba masu answer sheet, kamar ance Mayraah ta daga kai taga Musharraf tsaye at the far end of the hall yana danna wayarsa, ta dauke kanta da sauri bata sake kallon side din ba, a haka har suka fara exams din, Mayraah ta dinga kallon questions din that look strange in her eyes, tunani ta fara yi ko dai ba handout din ta karanta ba, though the questions look familiar but she is just confuse, just few minutes da fara jarabawan Mayraah ta sunkuyar da kanta trying to calm herself down, ta lura Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, Mayraah ta kalli side dinta, sai da gabanta ya fadi ganin wayarta take lullubewa da hijab bayan ta ciro shi daga bra dinta, duk da how strict the invigilators where haka Badiyyah ta dinga satan amsa da wayarta cikin dubara tana yi tana keeping serious face, Mayraah gabanta ya dinga faduwa don in dai lecturer ya kamata to kora ne direct bbu wani corner corner, after like 30 minutes Dr Musharraf ya karaso gaban Badiyyah yana kallonta, tayi saurin cusa wayar tsakanin cinyoyinta, can ya ɗan kalli colleagues dinsa ko kadan bai son attention dinsu ya dawo wajen, hakan yasa ya ɗan fara zagaye zagaye a wajen, sai kuma ya tsaya dab da ita, yayi kasa da murya yace "Bring the phone Badiyyah" Badiyyah jikinta ya fara rawa, ta ciro wayar gabanta na mugun faduwa, kawai ya kai hannu ya karba without letting anyone notice them ya saka a aljihu ya bar wajen, Badiyyah ta sauke ajiyar zuciya, Mayraah ta bi Musharraf da kallo.....