← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 145

Sashe 39

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami was speechless, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi, banda kallon Alhaji Mansur babu abinda take, Alhaji Mansur ya ci gaba yace "Don haka mun sanar masa za aje karbo mana duk wani kaya da aka kai gidan da sunan aure, kudin da muka kai kuma Faisal zai koma ya amso su" Mami ta girgiza kai cike da damuwa tace "Ba sai an amso komai ba Alhaji, mu bar masu ko don...." Ya wani hade rai ya dakatar da ita a fusace yana kallonta yace "Akan me zaki ce ba sai an amso komai ba? Mu bar masu saboda muna tsoronsu? Mutanen da basu san mutunci ba, mutanen da suka yaudaremu suka maida mu yan iska, ai basu cancanci ko tsinke a bar masu ba wlh, komai sai sun fito da shi idan ba haka ba hukuma ta rabamu da su" Mami dake masa wani kallo ta kasa jurewa tace "Ku ko ina sai kun nuna wannan halin naku na karanta? Idan shi wanda ya siya kayayyakin da kudinsa yace a bar masu fa?" Alhaji Mansur ya mike yace "Shi wanda ya siya kayan ya ci kaza kazansa, ai ba shi ke da iko da kansa ba, Kuma wallahi wallahi kin ji rantsuwan musulmi ko? To sai an amso kayan nan gaba daya, yanzun nan za a tura su Halima tunda dama su suka kai, don haka su za su koma su amso, aikin banza kawai" Yana kai wa nan ya fice daga parlon yana muzurai, tashin hankalin Mami ya kashi biyu yanzu ta ma rasa wani tunanin zata yi in particular, babban damuwarta na farko Musharraf, she don't know how he will take this and cope don ta ga yana son yarinyar, na biyu kuma ita a rayuwarta bata son taga an ci ma mutum mutunci, she detest that, babu tantama tasan an tara jama'a gidansu yarinyar nan, a haka su Halima za su je su gwada halinsu na rashin tarbiyya da rashin mutunci cikin taron jama'a, mikewa tayi ta dauko wayarta tayi dialing din number Alhaji Saminu wanda shine babba a family din and he resides in kaduna, kuma duk suna shakkarsa suna jin maganarsa, yana picking bayan sun gaisa ta fara masa bayanin abinda ke faruwa, ya katse ta yace "Duk na san da batun nan an kirani an gaya min komai, ashe kananun mutane ne makaryata, kinga kuma baza mu bari ɗan mu ya auro warce bata da asali ba, dama an san su waye iyayen nata ne to da sauki, kinga kuwa ai baza mu yarda a kawo mana irin wannan cikin zuri'ar mu ba" A hankali Mami tace "Haka ne, amma yanzu Alhaji Mansur ya bar nan wai za a tura su Hajiya Halima su je can gidansu yarinyar su amso kayan aure da aka kai, ni kuma naga hakan bai kamata ba tunda nasan wacece Hajiya Halima nasan kuma me zata je ta aikata a gidan, kasan cin mutunci bashi da dadi Alhaji" Alhaji Saminu yace "Shikenan shi Faisal da zai koma amso kudin auren sai ya karbo har akwatunan, zan kirasu in sanar masu kada a tura kowa in ba shi Faisal din ba" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, Mami ta ɗan ji hankalinta ya kwanta don baza ta so a walakanta kowa ba a kan Musharraf, kara kiran layin Musharraf tayi for the countless time amma still a kashe, she felt so disturb and worried for him, ta zauna saman kujera ta dafe kanta.... Ammi ta kasa nutsuwa tun bayan da ta shigo parlon baƙi ta dalilin kiran da Abba yayi mata a waya, Abba ya bi ta da ido har ta nemi waje ta zauna tana kallonsa ita ma, da kyar tayi karfin halin cewa "Lafiya dai ko Yallabai?" Abba ya kasa ce mata komai ya dauke idonsa daga kallonta, nan taji hankalinta yayi mugun tashi don kana ganin Abba kasan he is not himself, Ammi ta kasa jurewa tace "Don Allah ka gaya min abinda yake faruwa Yallabai ko yaron cewa yayi ya fasa auren ne??" Abba ya kasa bata amsa don a duniya baya son duk wani abu da zai daga mata hankali sanin condition dinta, but he have no choice dole zata sani, Ganin yanda Ammi ta rikice masa yayi ta maza yace "Haka ne" Ammi was shock, ta dinga kallon Abba ko kiftawa babu, lokaci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Kana nufin ya fasa auren?" Abba ya gyada mata kai, Ta fashe da kuka tace "Meye dalilinsu Yallabai? Sai ana gobe daurin aure an tara jama'a za su zo yau su ce sun fasa, me aka masu haka?" Kuka take sosai tana kallon Abba da ya kasa cewa komai don zuciyarsa ya gama karaya, he is just trying his possible best to be stable, yasan in dai ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan sai ta fadi kasa yanzu, she won't be able to take it ya sani... Abba ya dake yace "Ya isa haka Hajara, dama Allah ya riga ya rubuta Mayraah ba matar yaron nan bace, shi yasa kika ga hakan ya faru ana gobe daurin auren, kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, duk abinda Allah yayi mana dai dai ne kada mu masa butulci, sai dai bana son ki sanar ma kowa an fasa auren nan tukunna" Cikin kuka sosai Ammi tace "To me ya rage yallabai, gobe ne fa auren? Meye amfanin boye boye, ba gwara a sanar ma kowa ya kama gabansa ba? babban damuwata halin da Mayraah zata shiga idan ta samu wannan mummunan labarin don ban ga alamar ta sani ba..." Ammi ta kasa controlling kanta a parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, Jikin Abba ya kara sanyi, he wish yaron nan bai sanar ma Mayraah ya fasa auren ba da kuma dalilinsa na fasawar don duk abu da ya taɓa Mayraah yasan shi ya taɓa, shi kansa bai san irin son da yake ma Mayraah ba, bai taɓa mata kallon ba shi ya haifeta ba, Abba yayi kasa da murya yace "Na dai ce maki kar ki ce ma kowa komai, kuma kin manta daurin auren biyu ne? Ai akwai na Maheer, so for now kiyi shiru don Allah, and pls ki kwantar da hankalinki ki koma ki ci gaba da sabgogin ki" Sai da Ammi ta ci kukanta na kusan minti biyar a parlon sannan ta share hawayenta ta mike a hankali ta fita a sanyaye, Abba da gaba daya tunaninsa ya dagule ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ransa, waye wannan da yasan da batun ba su suka haifi Mayraah ba har ya je ya sanar ma family din Musharraf?? Waye yayi wannan danyen aikin, baya tunanin zai taɓa yafe ma kowa waye wannan, da zai san waye sai ya sa an dauresa even if da last card dinsa ne, asalin Mayraah abu ne wanda su kansu are still very surprise ta yanda suka ajiyesa babban sirri a zuciyoyinsu for almost 22 years now, ko da wasa basa tada zancen tsakaninsa da Ammi, sai dai in ya siya kaddara da sunan Mayraah ya bata ta ajiye sai yaga mood dinta ya canza don hakan na tuno mata da cewar ba fa su suka haifi Mayraah ba sannan Mayraah bata da gadonsu, ita ce ma ta kawo masa shawaran dinga siyan property da sunanta tun yarinyar na shekara sha biyu, duk sanda kuma Abba yayi hakan takan kwana ta yini cikin damuwa a zuciyarta ranan, ya san duk son da yake ma Mayraah bai kama kafar na Ammi ba, don Ammi ta dauki son duniya ta daura mata, yanda ta saka Mayraah a rai ko su Maheer bata saka haka ba, kawai Allah yayi Mayraah bazata sangarce ba saboda su Maheer da Usman da basu bada space din haka ba especially Usman that was so strict on her, Abba ya kasa ci gaba da zama ya mike ya dinga safa da marwa a parlon, shi dai yasan a garin Kano babu wanda yasan da cewar Mayraah isn't their Biological daughter, a takaice ma bayan shi, Ammi, Hajja, sai iyayensa kafin rasuwarsu, sai kilan ko Aunty Mariya babu wanda yasan da wannan secret din, ko da kuwa cikin abokansa da yan uwansa maza, Ammi ma yasan hatta kawayenta basu san ba ita ta haifi Mayraah ba, Abba ya kusa minti sha biyar yana zaga parlon, bai taɓa shiga damuwa da rudanin da ya shiga a wannan moment din ba, abu ne da ya zo unexpected kamar daga sama, Daga karshe ya dau wayarsa yayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa Maheer ya daga, amma bai ce komai ba, Abba yace "Kayi hakuri ka dawo mu yi magana Maheer, we need to talk pls" Abba bai jira jin me Maheer zai ce ba ya katse wayar, komawa yayi ya zauna yana ta sake sake a ransa har Maheer ya shigo parlon, Abba ya bi sa da kallo ganin yanda duk ya dawo wani iri a cikin ɗan kankanin lokaci, har ya samu far end of the parlor ya duka kasa ba tare da ya bari sun hada ido da Abban ba, Abba felt so guilty a moment din nan, in ma basu gaya ma kowa ba bayan wasu shekaru da suka ga Maheer ya mallaki hankalin kansa ai da shi sun sanar masa basu boye masa ba, Abba ya ma rasa ta inda zai fara, Shi dai Maheer ya sunkuyar da kansa bai yarda ya kalli Abba ba, kana ganinsa kasan ya shiga damuwa sosai ba kadan, it's something that hit him so hard kamar a mafarki, Abba yayi kasa da murya yace "Ina son ka fahimce mu Maheer, mun yi abinda muka yi ne for the Sanity of Mayraah, muna son ta taso like every other child cikin so da kauna, ta yaya za a so yarinya kamarta ta taso da damuwar ba mu ne iyayenta ba? How will she cope with that? Sannan wllh mu kan mance ba mu muka haifeta ba tsabar yanda muka dauketa...." Shi dai Maheer bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, Abba ya ci gaba yac "Maheer ban kiraka a yanxu don gaya maka yanda muka samu Mayraah ba, duk da nasan dole a yau
Chapter 39 · 0% Book details