Sashe 110
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Usman bai siya mata ba na abinci barin wanda yasan ta fi so irin su junk food da drink, suna tsaye duk ta shiga da su cikin hostel din, Usman na kallonta bayan ta dawo yace "Meye babu a kayan?" Ta girgiza kai tace "Ba komai" yace "Ohk, if u need anything ki kirani" Ta gyada masa kai tace "Nagode" motarsa ya koma ya bar su tsaye da Maheer ya wuce, Maheer bai bar wajen ba sai kusan karfe shidda. Gidan Hajja ya nufa, bayan yayi parking a kofar gida sae da yayi sallan magrib a masallacin dake layin sannan ya shiga cikin gidan, ya kai minti daya tsaye bakin kofar Parlon don bai ma san me zai tarar ba idan ya shiga, can dai daga karshe ya bude kofar ya shiga da sallama, Hajja na zaune parlon ga Badiyyah kwance a gefenta tana mata fiffita tana jero mata sannu, Haseenah ma na zaune parlon tana zuba madara a cup zata hada shayi, kallon Ammi dake zaune kan darduma ta idar da sallah yayi, tana ganinsa kuwa ta tamke fuska, ya zauna kan kujera yana kallon Hajja a hankali yace "Ina yini Hajja?" A takaice Hajja tace "Lafiya lau" yace "Ya mai jikin?" Hajja tayi banza da shi, Haseenah ta kallesa tace "Ina yini" Yace "Lafiya" Ya sake kallon Ammi cikin sanyin murya yace "Ina yini Ammi?" Mikewa tayi ta shige dakin Hajja ta kulle kofa, Hajja dae ta kyabe baki ta ci gaba da yi ma Badiyyah fifita don ba wuta a gidan, Haseenah ta mika ma Hajja shayin da ta hada cikin ladabi tace "Bari in je inyi sallah Hajja" Hajja tace "Toh Allah maki albarka er nan" Haseenah ta ɗan yi murmushi tace "Ameen Hajja" Daga haka ta mike ta shiga dakin Badiyyah ta kulle kofa, Maheer yayi kasa da murya yace "Don Allah Hajja ku yi hakuri da abubuwan nan da suka faru, wannan duk sharrin shaidan ne ba wani abu ba" a fusace Hajja tace "Ae shaidaniyar na nan tare da ku, babu wani shaidan sae ita, daga abun arziki sae ya juye ya zama na tsiya? Kai tun da kake ka taɓa ganin ubanka da uwarka sun samu sabani har ya daga mata murya? To kaga kuwa ae shaidaniya ce yarinyar nan, a kanta kai har kasan ka saki matar ka ta sunna wanda duka duka yau sati nawa da auren, dubi er uwarka ta jini halin da take ciki duk a kanta, to wallahi da mun san haka gari zae waye in na bari Ammi ta riketa shegiya nake, da mutum na sanin gaibu wllh da babu abinda zae sa mu fara shigo da ita zuri'ar mu...." Maheer felt so bad akan accusation din da Hajja ke ma Mayraah, don nan da nan yaji zuciyarsa na tafarfasa, amma dae ya dake yace "Abinda zae faru ya riga ya faru Hajja, kuma Mimi bata ma gidan yanzu haka, tunda Abba ya ga ran Ammi ya ɓaci ya sa aka kai ta gidan kawu Lawali, so Ammi zata iya komawa gida yanzu don Allah ki bata hakuri Hajja" Hajja tace "Ba ruwana wallahi, ae rufe ido yayi ya ci mata mutunci a gaban surkarta duk akan yarinyar da muka tsinta da kyakkyawar manufa, da kuma yake zakalkalewa kan Mayraan ance maku yyi niyyar riketa ne da farko?? Har da ku a kwayewa uwar ku baya a kan wannan yarinyar?" Maheer yace "Hajja wannan duk ya wuce, ki ba Ammi hakuri ta koma gida don Allah" Hajja tace "Ni nayi mata laifi da zan bata hakuri?" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya mike ya tafi dakin da Ammi ta shiga yaji ta sa makulli, dawowa parlon yayi duk jikinsa yayi sanyi, ya zauna yana kallon Hajja, Hajja tace "Babu abinda zaka gaya mata yanzu da zata saurareka, kawai ka dau matarka ku tafi gida sai da safe" a hankali Maheer yace "Amma don Allah ki kara bata hakuri, gobe in sha Allah zan zo da safe" Hajja tace "Dauki matarka nace ku tafi sai da safe, ka bar mu muji da abinda ya tsaya mana a rai" Tana fadin haka ta mike ta je kira masa Haseenah da ta shige daki, suna fitowa parlorn Maheer ya tashi ya isa inda Badiyya take kwance yana kallonta yace "Ya jikin naki?" Pretending tayi kamar tana bacci, ya kalli Hajja yace "Ko za mu tafi gidana tare da ita saboda in dubata har ta samu sauki?" Haseenah ta juya ta kallesa da sauri, Hajja tace "Taje tayi me a gidanka Maheer? Ba zuwa gidan naka da tayi bane yasa aka kusa illata min ita? Aa babu inda zata je nasan ko hada baki ku ka yi da ɗan iskan kanin naka ku karasa kasheta??" Yayi kasa da murya yace "Ki bar wannan zancen don Allah Hajja, wannan ai saboda lafiyarta yasa nace mu je da ita ba wani abu ba" Badiyyah dake sauraronsu, ta mike zaune tana wani mitsike ido tace "Zan je" Hajja tace "Zaki iya taka kafafuwan ne da kike cewa za ki je?" Tace "Zan daure" Ita duk saboda yin waya da Malamin da Haseenah ta bata numbersa yasa take so ta bar gidan, don tasan definitely Ammi a dakinta zata kwanta bazata ce zata kwanta dakin Hajja ba, shkkn yanzu kuma bata da privacy tunda Ammi na gidan ba damar waya, ga shi daki biyu kadai ne a gidan, sannan tun jiya da daddare yace ta kirasa kafin abun nan ya faru har yau kuma bata kira ba babu privacy duk da yanda take fama da kanta, don duk jikinta ciwo yake mata ba na wasa ba, ga kafafuwanta don dai likitoci sun ce ba karaya bane amma ita sai take jin kamar sun karye ne kawai, hannunta daya ma mugun ciwo yake mata aka ce targade ne shine aka gyara mata a asibitin ko amfani bata iya yi da hannun har sannan, tana kallon Hajja da kyar tace "Hajja ki sa min kayana kala uku a jaka" Hajja tace "Ba fa inda za ki je nace su je su karasa ki, ke wai baki da zuciya ne, ko da kudi idan aka ce ki koma gidan Maheer sai ki koma?" Badiyyah ta wani hade rai tace "To wai ke ina ruwanki Hajja, in zaki hada min kayan ki hada in kuma baza ki hada ba in tashi inyi da kaina" Haseenah dai na tsaye taki cewa komai, Hajja tace "Toh, Allah dai ya ga na fita hakkin ki, dama so nayi ki zauna nan in maki duk abinda ya kamata" Daga haka Hajja ta mike ta shiga dakin Badiyyah, ba a dau lokaci ba ta fito da jakar kayanta ya hada mata kala uku, Maheer ya amsa yana kallon Badiyyah yace "Zaki iya tashi ai" Da kyar ta mike tsaye tana dingisa kafafuwanta da suke mata azababben ciwo, ya kama hannunta suka nufi kofa yace "Sai da safe Hajja" Hajja dai taki cewa komai don har ranta bata so Badiyyah ta sake komawa gidan ba to amma ya zata mata tunda taki ji, can ciki Haseenah tayi ma Hajja sai da safe ta bi bayansu fuskarta babu walwala, back seat ya bude ma Badiyyah ta shiga da kyar da kyar tana washh washh yana mata sannu, ya ajiye jakar kayanta a booth, Haseenah ta bude gaba ta shiga ta zauna, shi ma ya shiga motar suka bar anguwan, sai da suka yi nisa yace "Me za ki ci Badiyyah?" Badiyyah da ta kwanta bayan motar kamar er yarinya ta marairaice tace "Ai bana iya cin abinci" Yace "Toh bari a siya maki kaza da yoghurt, kilan appetite dinki ya dawo" Haseenah ta juya ta ɗan kallesa, ya samu inda zai siya ma Badiyyah abinda yace, yayi parking sannan ya sauka daga motar, bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da leda daya tal, ya bude back seat ya ajiye ma Badiyyah, nan da nan kamshin kazar ta gauraye mota, ya koma driver seat ya tada motar suka kama hanyar gida, suna isa gida a kofar gida yayi parking, duk tunanin Haseenah zai koma ne su ma ya siyo masu kazar, ya bude ma Badiyyah back seat ta lallaba ta sauko tana rike da ledan kazarta da yoghurt, ya ciro jakanta a booth, all this while ko kallo Haseenah dake ta bin su da ido bata ishesa ba, a haka dai suka shiga cikin gidan Haseenah na tafiya a hankali tana biye da su fuskarta a daure, ya bude ma Badiyyah wani spare room ba wanda Mayraah ta zauna ba, fuuu Haseenah ta shige dakinta ta zauna gefen gado ta cire hijab dinta don wani mugun zafi ta dinga ji, can dai ta kasa ci gaba da zama ta fito corridor ta gansa ya dauko plate da cup ya shiga dakin da Badiyyah take, da ido ta bi sa har ya fito daga dakin ya fice daga gidan gaba daya, mota ya shiga ya kama hanyar inda Mayraah take don tun dazu hankalinsa gaba daya na kanta, kaza ya siya mata da drink din da yasan tafi so me sanyi, yana isa ya tadda motar Usman a kofar gate din hostel din, Mayraah dake zaune kan wani dakali tare da Usman dake danna wayarsa ta bi motar Maheer da kallo, tun da Usman ya zo after magrib basu yi maganar da ya wuce na minti biyu ba ya fara danna waya, lkci lkci dai zai daga kai ya kalleta, ita dai kawai tana zaune gefensa tayi nisa tunanin da take har ta hango motar Maheer.