← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 145

Sashe 40

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko gobe kowa zai san wacece *MAYRAAH* kuma ya aka yi ta shigo rayuwarmu har muka ga gwara mu boye ma jama'a, don yanzu babu wani batun boye boye kuma, amma Maheer ina son ka sa a ranka Mayraah isn't ur Biological sister, er uwarka ce kawai ita in islam, baya nan babu wani alaka ta jini tsakanin ku, kuma ka sani cewar da aure tsakaninku...." Maheer ya daga kai da sauri ya kalli Abba jin furucinsa na karshe, bai san sanda ya mike ba yana girgiza kai yace "Abba har abada babu aure tsakanina da Mayraah, kuma har gobe zan ci gaba da yi mata kallon kanwata ta jini ne warce muka fito ciki daya, bayan wannan bazan yi ma Mayraah wani kallo ba, she still remains my blood" Shiru Abba yayi yana kallonsa don gaba daya ya gama discouraging dinsa akan abinda ke zuciyarsa, bayan few seconds Abba ya sauke kansa kasa yace "Haka ne, And i am happy u said this..." Maheer yace "Kuma tunda aka fasa aurenta nima a daga nawa kawai, dan i won't have the rest of mind of getting married tomorrow bayan damuwar da nasan kanwata zata shiga" Abba ya girgiza kai yace "Baza a daga naka ba, in sha Allah gobe ne daurin auren ka babu fashi" Aunty Mariya ta dinga salati a rikice a dakin Ammi bayan Ammi ta kirata ta sanar mata abinda ke faruwa, Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a saboda wani dalili yace ya fasa? Mun shiga uku" Cikin kuka Ammi tace "Ni dai kawai Alhaji ce min yayi an fasa amma ban san dalili ba" Aunty Mariya da har hawaye ya cika idonta tace "Da kyar in ba yan uwan nan nasa da suka kawo lefe ne suka lalata auren nan ba, kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu ta ina za a fara Ammi? Ina Mayraah din, anya ma ta san abinda ke faruwa kuwa?" Hankalin Ammi ya kara mugun tashi da ta tuna Mayraah, ta yaya zata dau wannan lamari, Ammi ta kalli Aunty Mariya cikin kuka tace "Ban san ko ya gaya mata ba, amma dai sun cutar min 'ya ta, kuma Allah ya saka mata" Aunty Mariya ta share hawayen dake sauka nata idon ta mike ta fita daga dakin, can dakin Mayraah ta tafi ta bude kofar, ganin su Hamidah kadai ne a dakin tace "Ina Mayraah?" Hamidah tace "Kilan tana dakin Yaya Maheer, waya take yi ta fita saboda hayaniya" Aunty Mariya da jikinta yayi sanyi ta juya ta bar bakin kofar, dakin Maheer ta tafi, ta gansa shi kadai a dakin nasa zaune gefen gado ya dafe kai, Aunty Mariya ta karasa cikin dakin ta kulle kofar cikin damuwa sosai tace "Maheer amma me yasa suka ce sun fasa? Wani laifin aka masu ne?" Ya dago kansa yana kallon Aunty Mariya da idanuwansa da suka kada sosai yace "Aunty...." Sai kuma yayi shiru, Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai ita ma duk zuciyarta ya karaya, Cike da karfin hali Maheer ya ci gaba yace "Aunty wacece Mayraah?" Sosai gaban Aunty Mariya ya fadi, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, and u can see the shock a fuskarta, Bakinta na rawa tace "Ban gane ba Maheer, wani irin tambaya ne wannan kuma?" Mikewa yayi trying his possible best to control his emotions yace "Aunty dama ba Ammi da Abba suka haifi Mayraah ba?" Aunty Mariya bata san sanda ta nemi waje ta zauna ba don sai da taji zuciyarta ya tsinke, da kyar tace "Maheer? Where did u hear this from?" Maheer ya hadiye wani abu da kyar yace "Dalilin fasa aurenta kenan...." yana fadin haka ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mun shiga uku" Kasa kwakkwaran motsi tayi daga inda take zaune tsabar yanda ta girgiza, bayan kusan minti goma ta mike kamar warce ruwa ya cinye tana tafiya a hankali ta fita daga dakin, dakin Ammi ta koma ta bude kofar a hankali ta samu Ammi zaune gefen gado tayi tagumi hawaye sai sauka yake a idonta, Aunty Mariya ta tabbata Ammi bata san abinda ke kasa ba, kasa karasawa cikin dakin Aunty Mariya tayi ta juya ta fita, ta tafi dakin Usman ta dau Hijab dinta da purse ta fita direct sai gidan Hajja, tafe take hawaye na sauka idonta tana tausayin halin da Ammi zata shiga idan tayi find out dalilin fasa auren Mayraah, ba a ma maganar Mayraah din, to ta ina wannan boyayyen maganar da bai fi su hudu kawai suka sani bane ya fita? Waye ya fitar da wannan sirrin na shekara 22, haka ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un har ta isa unguwan Hajja bata sani ba sai ji tayi mai adaidaita sahun na cewa "Hajiya mun shigo layin" Tsabar gigicewa kawai ta sauka ta fiddo dari biyar ta basa ta karasa har karshen layin da kafarta, tana shiga parlon Hajja ta zauna nan kasa tana kallon Hajja da Mama Ladi dake gwada tsohon breziyar Badiyya tana baɓɓaka dariya kamar tababbiya ita a dole ta samu breziyar da zata sa da biki, dama Badiyya ba dai manyan kirji ba shi yasa Bra dinta yayi ma Mama Ladi ciff, Hajja na kallon Aunty Mariya ganin yanayinta tace "Lafiya Mariya?" Nan da nan wasu sabbin hawayen suka shiga sakkowa idanuwanta cikin rawan murya tace "Hajja an fasa auren Mayraah" Caraf a kunnen Badiyya dake shiryawa zata je gidansu Haseenah ta mata rashin mutunci don ta kirata har taji babu dadi bata dagawa daga karshe ma wayar sai ta ji sa switch off, Ba Hajja ba har Mama Ladi sai da ta mike tsabar gigicewa, Mama Ladi na zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, aka fasa auren Mera?" Hajja da ita ma ta rude lokaci daya tace "Ban gane an fasa auren Mayraah ba Mariya, me ke faruwa?" Aunty Mariya ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, Mami Ladi tace "Dama ana fasa aure haka kawai babu dalili? Ki gaya mana me ya faru aka fasa auren, ko wiwi mijin ya sha da zai ce ya fasa aure ana gobe daurin aure, Ga ire irena da suka zo daga wata uwa duniya saboda bikin nan, me yake nufi da mu kenan mun yi tafiyar banza? Ai zama bata gan mu ba mu tafi can gidan ayi komai a gabanmu, amma Allah ya tsine ma mijin nan albarka dai dai gwargwado" Hajja da ta kasa zaune ta kasa tsaye ta dau Hijab dinta ta nufi kofa, da ganinta kasan a gigice take, Mama Ladi ta figi mayafinta ta yafa kan breziyar jikinta ta bi bayan Hajja suka bar Aunty Mariya zaune sai hawaye take, Tsabar farin ciki Badiyya bata san sanda ta dare saman gado ba ta dinga tikar rawa tana karkade kirji, ta rasa inda zata saka kanta don murna, tunda ta fito duniya bata taɓa shiga farin ciki da murna irin na yau ba, Jin an banko gate alamar fitar su Hajja da Mama Ladi Aunty Mariya ta mike da sauri ta bi bayansu, Badiyya ta leko parlor bayan da taji shiruuu alamar babu kowa a gidan, takalmanta ta sa har wani ɓari jikinta yake ta tafi gidansu Haseenah tayi mata breaking news din nan me dadin ji, tana fita kofar gida ta hango Hajja, Mama Ladi da Aunty Mariya can saman layi sun yi nisa, sai da ta jira ta daina hangosu kafin ta canza hanya ta samu ɗan sahu direct sai gidansu Haseenah. Haseenah na zaune dakinta cikin kawayenta abun duniya ya mata yawa ta rasa tunanin da zata yi, gashi ko kawayen nata bata gaya masu abinda ke faruwa ba na ɓatan gold din cikin jakanta don cousin din nan nata Jamila na dakin, kuma in dai tayi magana a gabanta to kamar Mummy ta ji ne, Haseenah ta kalli agogo dake nuni da karfe biyar da rabi na yamma duk da damuwar da take ciki hakan bai sa ta rike cewar Maheer bai kirata ba tun bayan da ya ajiyeta dazu da safe, dama line biyu gareta, kuma Badiyya guda daya kawai gareta bata da dayan, da Badiyya ta isheta da kira sai ta cire sim din ta ajiye, Haseenah ta sauke ajiyar zuciya ta jawo wayarta tayi dialing number Maheer kilan in taji muryarsa hankalinta zai kara kwantawa, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no Answer, bude kofar dakin aka yi ta juya a tsorace don da taji an bude kofa Badiyya take expecting gani, ai ko taga Badiyyar ce ta shigo ba ko sallama kamar an hankadota, nan da nan Haseenah ta dake ta hade rai tana tunanin karyar da zata lafta mata, Badiyya na zuwa ta kamo hannun Haseenah bakin nan nata har kunne tace "Taho kawata labari da dumi duminsa..." Haseenah ta mike ganin farin ciki ne kaca kaca fuskar Badiyya ta bi ta suka koma dakin me aiki, da mamaki Haseenah tace "Lafiya naga kamar an maki albishir da aljanna wannan farin ciki haka?" Badiyya ta saki wani guda tace "An fasa auren Mayraah da Dr Musharraf" Haseenah ta zaro ido tace "Keee don Allah??" Badiyya tace "Wallahi kawata, yanzu Mama Mariya tazo gidan Hajja ta sanar mata" Haseenah tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, kai amma na taya ki murna wllh, what next kenan yanzu?" Badiyya tace "Sai in fara shooting shot dina, in gaya maki babu zancen aure dai kam, yanzu haka so nake in ga idanuwar er iskan nasan suna can sun kumbure" Haseenah ta rike haɓa tana kallon Badiyya lokaci daya kuma tana jinjina makircinta, Haseenah tace "Amma don Allah kawata ki bani labarin yanda kika yi wannan abun, ni fa na fara tsoronki yanzu wllh" Badiyya tayi wani dariyar bosawa tace "Breaking news kawata, dama nace bazan gaya maki ba sai nayi accomplishing mission dina, Ashe dai duk wannan abun da ake ba Ammi da Abba bane suka haifi Mayraah, Mayraah dai er tsintuwa ce mara asali warce kila ma cikin shegenta aka yi aka jefar da ita a titi, ni kuma tun da na samu information din nan shine na bibbi dangin Dr Musharraf na sa aka rubuta letter aka kai masu one by one, har gidansu Musharraf din an
Chapter 40 · 0% Book details