← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 145

Sashe 122

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 [7/8, 1:41 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan Magrib Mayraah ta fito kofar gida ta dalilin kiran da Maheer yayi mata, har a sannan bata gama recovering daga shock din abinda Badiyyah tayi mata dazu a school ba, gaba daya a sanyaye ta yini ranan, ɗan shayin da take iya sha ma idan ta dawo daga exams yau duk bata sha ba, haka nan ta wuni sai dai ta sha ruwa, ta zauna inda ta saba zama duk sanda yayyin nata suka zo, Maheer dai sai kallonta yake, cikin sanyin murya tace "Ina yini?" Maimakon ya amsa sai cewa yayi "What is it again Mimi? You look disturbed" Cike da damuwa yayi tambayar, nan da nan hawaye ya kawo idonta, for almost 4 weeks now bai ga hawayenta ba duk da a sati hudun nan bai fi sau biyar ya zo wajenta ba, hankalinsa ya tashi ganin hawayen nata, yayi facing dinta a rikice yana tambayarta me ya faru, cikin rawan murya tace "They caught Sis Badiyyah with Mal-practice in exam hall today, shine da taga haka sai ta jefa min takardan da take expo din" Bai san sanda ya mike tsaye ba yana kallonta babu ko kiftawa, ta fashe da kuka tana goge hawayenta da hijab din jikinta, Da wani expression yace "Ta wurga maki takardan? Ta wurga maki as in how? And what happened afterward?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "A security lady saw when she did that, da kuma Coursemate dina dake bayana, duk sun ga sanda tayi haka sai suka gaya ma lecturers din" Maheer ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya zauna, bayan few seconds yace "Amma kin gama exams din Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "Ko baki gama ba?" Cikin sanyin murya tace "I did what i can remember, amma fa yaya an cika mata Mal-practice form don ta bar ID card dinta ta gudu daga hall din, is there nothing they can do about that so that baza a koreta ba? Kasan expulsion ne fa idan an kama mutum yaya" Maheer ya mata wani kallo yace "To ke ina ruwanki in an koreta din? Da bata samu tayi implicating dinki ba shine kika samu bakin magana? What if babu wanda ya ga sanda tayi hakan kin zata ke ma baza a sa ki cike form din ba a kore ku tare? ni dama tun farko nace school is never for Badiyyah, ban san me yasa aka dage sai tayi karatu ba, going to school was neva her calling, kilan yanzu da aka koreta for the 4th time kowa zai hakura da cewar sai tayi karatu a fara nema mata wanda za a lallaba ya aureta" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, yace "Nasan baki ci abinci ba" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, ya mike yace "Mu je in siya maki abun da za ki ci" Tace "Ai Ummi bata dakin tana school, the door is open" Yace "Ba ta baki spare key din dakin ba, just close it, mu je mu dawo yanzu...." Mayraah ta mike ta wuce ciki ta kulle kofar sannan ta fito, zaune ta samesa cikin mota yana jiranta, ta karasa ta bude front seat ta shiga motar, har suka bar area din Maheer na jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, shi bai taɓa ganin shaidaniya in human form kamar Badiyyah ba she can go to any extent don yi shaidanci kanta tsaye, ya girgiza kai cike da takaici, can ya juya ya kalli Mayraah da tayi shiru tana tunani ita ma, yace "Wato tana ganin an kamata sai ta fita da gudu daga hall din?" Mayraah bata sanda tayi murmushi ba bayan ta tuna yanda Badiyyah ta gudu daga hall din, Maheer har ya mance rabon da ya ga murmushinta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, he wish she will continue smiling like this forever, Mayraah ta kasa controlling kanta ta fashe da dariya tana kallonsa tace "Yaya u need to see how she jumped and ran out of the hall, Kuma fa first day da muka fara exam din wannan Dr Musharraf din ya kamata da waya tana satan amsa amma yayi covering dinta ya amshe wayar without anyone noticing" Maheer dake sauraronta yace "Akan wani dalili yayi covering dinta? He saw her with expo kuma yayi covering dinta wani irin lecturer ne shi?" Mayraah dai tayi shiru, Maheer yace "Toh ke me yasa ma ku ka zauna waje daya da ita at the first place?" Mayraah ta kallesa tace "Kawai tun first day da muka fara exam din naga ta zauna gefena, shine kullum take zama side dina" Maheer ya girgiza kai yace "Sai taje ta gaya ma wa enda suka dage sai tayi karatu abinda ta aikata on her final paper, it's better she go and learn tailoring in dai ba a samu wanda zai aureta ba yanzu" Mayraah tace "Ai kai ma zata gaya maka abinda ya faru yau" Yace "Saboda me zata gaya min?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ba ka maida ta gidanka ba yanzu, kaga kai zata fara gaya ma kafin kowa ma" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, lokaci daya ya maida idonsa kan titi cike da mamakin yanda tayi tasan Badiyyah na gidansa, bayan some seconds yace "Wa ya gaya maki tana gida na?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "To ai ba wani abu bane don tana gidanka tun da yar uwarka ce, she is ur blood" Maheer bai ce mata komai ba cause he don't want to talk about that again, yayi parking inda yake son siya mata abincin sannan ya juya ya kalleta, a hankali yace "Mu je" Ta girgiza kai tace "I will wait here Yaya" yace "Saboda me?" Ta jinginar da kanta jikin kujeran motar tace "I am tired" ya gyada mata kai yace "To me zan siya maki?" Tace "Anything" Bude motar yayi ya sauka, ya wuce ciki ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, ignoring din maganarta na karshe da yayi ya mata ciwo sosai, shirun da yayi mata ya nuna Yes Badiyyah blood dinsa ce. Karfe tara saura Maheer ya ajiye Mayraah a hostel, ta bude motar ta sauka rike da ledan abincin da ya siya mata, a hankali tace "Sae da safe" ya gyada mata kai yana kallonta don tun da suka baro wajen siyan abinci ta zama so silent, zata juya ta wuce ciki yace "Wait Mimi" juyowa tayi ta kallesa, yayi kasa da murya yace "How about ur project?" Tace "Na gama, on Monday zan yi submitting" yace "Ohk, kar ki kashe wayarki zan kira ki anjima" ta gyada masa kai sannan ta juya ta shiga ciki ya ja motar ya kama hanyar gida... Maheer na isa gida ya tadda Badiyyah kadai zaune a parlor, har ya shigo tsakiyar parlon bata sani ba don tayi nisa cikin tunanin da take, ta saka wancan ta warware wannan duk nan neman solution take ma chakwakiyar da ta jefa kanta yau, she just can't imagine ace yau da gaske an koreta a school, tare suke zaune da Haseenah a parlorn, amma Haseenah na jin shigowar motar Maheer ta ruga dakinta da gudu wai zata je tayi wanka don tun safe bata yi wankan ba, Maheer ya gyara tsayuwarsa yana kallon Badiyyah ganin alamar bata san yana tsaye kanta ba yace "How was ur exams?" Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, ta juya da sauri tana kallonsa, ta ɗan sosa kai tana murmushin yake tace "Sannu da dawowa yaya" Yace "Sannu, ya exams din?" A hankali tace "Alhamdulillah" yace "Shikenan kun gama kenan ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba, kana ganin yanda take muzurai kasan bata da gaskiya, yace "To Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku sa'a, ya baku cleared pass gaba daya" Badiyyah dai taki cewa komai sai sosa kai take, dakinsa ya wuce, yana shiga ya kulle kofa.... Badiyyah ta mike ta wuce nata dakin ta shiga ta kulle ta zauna kasa ta fara shesshekan kuka ta daura hannu a ka, tun dazu ta kasa cin komai tsabar tashin hankali ko ruwa ta kasa sha, bata taɓa shiga damuwa irin na yau ba, ga Haseenah is not helping matters at all don duk shawaran da Badiyyah ta kawo a matsayin mafita sai Haseenah ta kyabe baki ta gwale shawaran tana girgiza kai tace ai fa nace maki ko da uban wa kike yawo kin riga kin koru a makarantar nan kawai, wannan kalman ke kara rikita Badiyyah ya sa tashin hankalinta ya ninku, gashi har yanzu bata samu Malam Dauda a waya ba balle ta gaya masa abinda ke faruwa, ta kirasa har ta gaji da kiransa, wayarta ne ya fara ring ta dauka da sauri taga Malam Dauda da take ta kira ne ya biyo ta yanzu, hannunta na rawa ta daga kiran ta kai kunne ta fashe da matsanancin kuka ta hau gaya masa abinda ya faru, daga karshe tace "Kuma Malam kai fa kace min ko da katon littafi na shiga babu wanda zai kamani, gashi da yan kananun takarda na shiga aka kamani" Sai da suka yi minti goma sha biyar suna waya daga karshe ta ajiye wayar bayan sun yi sallama, nan kuma ta fara tunanin inda zata samu dubu arba'in din nan da yace ta bada ayi aiki, ita dae ta shiga uku, ko dubu ashirin babu a account dinta yanzu haka, gashi yace tana turowa cikin daren nan zai fara aikin rufe bakin duk lecturers din dake nan sanda abun ya faru, hakan zae sa a kasa koran nata, zumbur ta mike ta fice daga dakin tayi hanyar dakin Maheer, ta tsaya jikin kofar dakin tana tunanin abinda zata ce masa, can dai ta kwankwasa kofar a hankali, dae dae nan Haseenah ta fito daga dakinta sanye da kayan bacci ta baxa uban turare a jiki, tana ganin Badiyyah ta hade rai ta tsaya tana kallonta daga sama har kasa, Badiyyah dai ko kallon inda take bata yi ba ta sake kwankwasa kofar dakin, bude kofar Maheer yayi ya kalleta sannan ya kalli Haseenah dake tsaye ta wani murtuke fuska, ya maida dubansa kan Badiyyah
Chapter 122 · 0% Book details