← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 145

Sashe 20

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki dawo 2.1, your performance is dropping terribly..." Mayraah dai bata dago kanta ba, yace "Idan ma kina son ki zauna gidanku bayan anyi bikin har zuwa sanda za ku gama exams din it's okay by me" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh ka bari in zauna gidan namu har in gama exams din" yace "Consider that done" Ta sauke kanta tace "Thank you so much" Ya sakar mata Murmushinsa me kyau underneath his breath yace "My pleasure" Tace "Yaushe za mu yi test dinka?" Yace "Gobe" ta dago da sauri tana kallonsa duk da ta san gobe ne amma tunaninta zae ɗaga masu, yace "I know u can do it Dear" Ta marairaice tace "Plss sir ka bar shi on Wednesday mana" yace "Ae bana zuwa Wednesday, beside i will be going to Abuja that day" tayi shiru tana kallonsa, ya shafa beard dinsa yace "Zan tura maki AOC, and u can forward to ur colleagues a group dinku na WhatsApp, kinga su ma sun ci albarkacinki kenan" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "To mun gode Sir" Yace "Sai bayan biki zaki daina ce min Sir din nan?" Ta ɗan saci kallonsa amma taki cewa komai, Ya lumshe ido ya bude, yace "Kinsan Friday za a kawo lefen ki?" Mayraah da sai da gabanta ya fadi tayi shiru bata basa amsa ba, yace "Yeah, on sunday sae in kaiki ki gaida Mamina with her sisters, they are all around" Mayraah dai ta kasa cewa komai, yace "We have just this week, daga next week bazan samu lokacin kai ki ba" Jin she is quiet yace "You are not saying anything Wife" Ta yi gathering courage tace "Allah ya kai mu lafiya" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "It's almost time for isha, zan tafi yanzu" Washegari Mayraah na zaune class tare da sauran Coursemates dinta ko wanne da sheet of paper a gabansa da question paper, ita dai sai juya pen din hannunta take, she looks so confuse cause ta yi karatu jiya da daddare don sai da ta kai kusan karfe daya kafin ta kwanta, but ji tayi kamar bata bude handout din ba kwata kwata, ga wani ciwon kai da ya sa ta gaba, ta daga kai ta kalli Dr Musharraf dake tsaye hall din wearing a sparkling white shirt, baƙin glasses ne a idonsa so she can't tell where he is looking in particular, ta ɗan bi hall din da kallo, Zaune taga Badiyya tare da clique dinta ta dage sai kwafan na Amira take da gefen ido, tun last week rabonta da school sai yau, bayan kusan minti talatin Mayraah ta mike kawai ta linke takardanta, Hamida sai kallonta take da mamaki ganin fa bata ga tayi rubutu ba, ta dinga mata alamar ta tsaya kar taje tayi submitting amma tuni Mayraah ta nufi inda Dr Musharraf ke tsaye, tana kallonsa tace "Where can i submit sir?" Ya mika mata hannu ta basa takardan, zata juya ta bar wajen as if in a whisper yace "Wait" ta tsaya ba tare da ta kalli fuskarsa ba, bude takardan yayi yaga sunanta kawai ta rubuta sai course da code, ya dinga kallonta kafin ya mayar mata da takardan yace "Go back and sit my friend" Ta amshi takardan ta juya a hankali ta koma, Badiyya dake kallonsu ta wani tabe baki ta ci gaba da satan answers din Amira da gefen ido, kusan sai da duk yan class din suka yi submit suka fita har Badiyya da clique dinta, ajin ya rage few students sai Mayraah dake ta juya pen dinta, zuwa sannan dai ta samu ta tuna solution din second question din kuma ta rubuta, yana cewa 5 minutes more amsan number 1 ya dira kanta in full speed, within that 5 minutes ta amsa question din ta kusa cika fullscap, dama questions hudu ne, to ta samu ta amsa biyu, zuwa sannan su hudu ne kawai a ajin da basu gama ba, ta mike ta tafi ta basa takardan ta ya amsa yana kallonta, ta juya ta fita daga class din ya bi ta da kallo ta cikin glass... Gun Hamida ta nufa, Hamida ta mike ganinta tace "What happened, baki yi karatu bane Mayraah, ina ta daga maki script dina kiyi rubutu amma baki kalla ba" Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema kinsan bazan iya ba, but na samu nayi answering guda biyu...." Hamida tace "To Allah ya bamu sa'a gaba daya" Wani Coursemate dinsu Nasir ne ya nufo su, yana kallon Mayraah yace "Dr Mu'azzam na kiranki Mayraah" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Ni kuma?" Yace "Eh" Ta kalli Hamida da sauri tace "Me na masa?" Hamida tayi dariya tace "Ke dai kije ki ji, ba munyi test dinsa ba last week, kilan he is impressed with your performance" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi don kaf department din nan babu wanda bai san Dr Mu'azzam da masifarsa ba, kusan kowa shakkarsa yake, babu wanda yake son encounter ya hada su, nan dai ta sa Hamida ta rakata sama zuwa office dinsa, Suna isa bakin kofar Hamida ta kara gaba ta bar ta da sauri kafin ma ya ganta, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faduwa tayi knocking kofar office din a hankali, sai da ta sake knocking aka amsa sannan aka mata izinin shiga, ta bude kofar ta shiga ciki ta rufe yana zaune office din tare da wani prof wanda shi ma lecturer dinsu ne, lkci daya gabanta ya tsananta faduwa don tsoron encounter ya hadata da lecturers din department din nan nasu take, ta risina ta gaishesu gaba daya, cikin fada Dr Mu'azzam yace "Ke what is wrong with u this semester with poor performances up and down, wani abu yana damun kanki ne?" Mayraah ta hadiye wani abu da ya tsaya mata da kyar ta girgiza kai tace "No sir" ita ihunsa kadae gigitata yake, Prof Habibu yana kallonta yace "Madam sai a final semester dinki zaki fara wasa? Are you okay? Or do you have any family issues u are handling?" Cikin fada Dr Mu'azzam yace "If not that she is one of our best student i won't waste my time looking for her, to ina ruwanmu idan student ya zama unserious, Prof kasan shi fa student yana da mentality din cewar yana shiga final semester ya ma gama karatun gaba daya, sai yayi ta abinda yaga dama, ke me yake faruwa dake haka? Ko Dr Musharraf ne ke damunki da baki iya maida hankali a karatunki yanzu?" Mayraah ta kasa cewa komai kanta a kasa, Prof ya kalli Dr Mu'azzam a bit surprise yace "Wani Musharraf din?" Dr Mu'azzam yace "Dr Musharraf dai da ka sani, ae fiancee dinsa ce, ba a kai maka IV office ba?" Prof Habibu ya kara kallon Mayraah yace "Ohh dama ita ce zai aura? Maa sha Allah, naji rumors wai a department din yarinyar take ashe haka ne...." Dr Mu'azzam yace "Gaskiya da alama Dr Musharraf na damun yarinyar nan kuma zai sa ta samu matsala, ke bari in gaya maki idan baki yi wasa ba zaki dawo 2.1 ne with the way i am seeing ur performance this semester" Prof yace "Kira min Musharraf din yanzu" Dr Mu'azzam yace "Ai na masa magana da nayi marking script dinta tun ran friday, i even showed him the script" Prof yace "Gaskiya ya bar yarinya tayi graduating da first class dinta, har muna tunanin zata breaking mana record din department din nan after 15 years" Dr Mu'azzam yace "That is my main concern wallahi prof, first class that she has been retaining tun daga level 1 sai yanzu a level 5 zata yi wasa da shi" Dr Mu'azzam ya kalleta yace "Madam leave my office, gwara tun wuri ki maida hankalinki" da kyar Mayraah tayi masu godiya ta juya ta nufi kofa, lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita kanta bata san me ke damunta semester din nan ba, abinda Musharraf din ma sae yayi sati biyu bai je gidansu ba sae dai su hadu a school ko kuma su yi waya, Tana kulle kofar office din sae ga Dr Musharraf, taki yarda su hada ido ta juya ta bar wajen da sauri, ya bi ta da kallo.... Ranan al-hamis Mayraah na dawowa daga school ta tarar an kai lefen Haseenah, akwatuna set biyu Maheer yayi mata wato 12 boxes, ita dai Mayraah tun kayan na gidan ma bata damu taga abubuwan da aka zuba ba, wasa wasa an fara shirye shiryen biki a gidan babu kama kafar yaro don duk wani abu da za a bukata na taron Abba ya siya ya jibge a store, ita duk ba wannan ba babban damuwarta sunday da Musharraf yace zai kai ta gidansu ta gaida Maminsa, da ta tuna hakan sai taji gabanta ya fadi, gashi gobe za a kawo nata lefen..... Mami ce zaune parlor tare da sisters dinta biyu Aunty Fatima da Aunty Baby dake zaune gefenta, sai su Anty Halima da Ruma'isa kusan dai su biyar ne ke ta fiddo da kayan cikin akwatuna set biyu me guda 7 each dake gabansu, Wasu dattijai mata biyu ma na zaune parlon, wanda daya yayar Dad dinsu Musharraf ce, daya kuma kanwar kakarsu, daya daga friend din Mami Hajiya Hafsah dake tsaye ita ma tana kallonsu Hajiya Halima tana ɗan murmushi tace "Ai ina ga ba sai an fiddo duk kayan nan gaba daya ba Hajjaju, maidasu bazai zama easy ba gaskiya, ga yamma ya gabato ga kuma drebobi na jiranmu a waje" Hajiya Halima ta daga kai tana kallon occupant din parlon gaba daya tace "To wai halan er gwal Musharraf zai auro da za a jibga mata wannan uban kaya haka tsadaddu kamar ɗan fashi? Shi bazai yi tanadi me kyau na rayuwarsa ba sai ya kare a zuba tsadaddun lefe ma yarinya? Ikon Allah! To ko fili ya kara cikin kadarorinsa ai ya karu karuwa ta har abada, amma duk a rasa wanda zai sa shi a hanya ya dinga wannan uban siyayyan? Da kyar idan kayan nan basu yi na Miliyan goma sha ba, da yake dama ita uwarsa duk harkar karya da nuna isa tana kan gaba gaba, banda haka ai ita me
Chapter 20 · 0% Book details