← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 145

Sashe 113

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa irish din a plate, Badiyyah tayi hamma sannan ta nufi kitchen, tana shiga taga wayam duk Haseenah ta wanke kayan da taɓata, ta gama dube dubenta a kitchen din bata ga alamar breakfast ba, can ta fito ta dawo parlon tace "Haseenah ni ina breakfast din nawa?" Ba tare da Haseenah ta kalleta ba tace "Ni zan maki breakfast din da zaki ci? Baki san hanyar kitchen din bane?" Badiyyah ta wani hade rai tace "Ban gane ban san hanyar kitchen din ba, dama a gidan nake da zaki ce min ban san hanyar kitchen ba? ina bakuwa dani baza ki bani breakfast a gidan yayana ba kike nufi?" Banza Haseenah tayi mata ta ajiye ma Maheer plate din irish da kwai ga ketchup a gefe, ta bude wani cooler din ta zuba masa farfesun catfish da tayi, shi dai bai ce mata komai ba, ta langwabar da murya tace "Bari in dauko madara in hada maka shayin baby" Daga haka ta mike ta koma kitchen, Maheer ya kalli Badiyyah da tayi wani mitsi mitsi da ido tana huci tana bin Haseenah da kallo, sai da ya ga Haseenah ta shiga kitchen yace "Zo ki dauka ki je ki ci" Badiyyah ta taho da sauri ta dau plate din irish din da bowl din catfish ta tafi dinning area ta zauna, sai ga Haseenah ta fito, sake baki tayi tana kallon Badiyyah, can ta nufeta a mugun fusace tace "Ke Badiyyah ki shiga hankalin ki kar in maki rashin hankali, breakfast din mijin nawa kika dauka saboda baki da saiti?" Maheer yace "To ke ina ruwanki, ba dai ni na bata ba?" Badiyyah na tafe hannu tace "Kuma baki isa ki hana yayana ya bani abinda ya ga dama ba a gidan nan, ta ya ma zan zo gidanki saboda bakin hali ki hana ni breakfast kamar wata yar iska??" Maheer ya mike tsaye yace "Dauki breakfast din ki wuce daki" A mugun fusace Haseenah ta nufo sa tace "Ban gane ba Maheer?" Calmly yace "Kina nufin da yunwa zaki bar sister na ko kuma ance maki bare ce ita?" Badiyyah ta ja tsaki ta dau breakfast dinta ta wuce ta gaban Haseenah har tana neman bangajeta ta wuce daki ta kulle kofa, Maheer yayi wucewarsa daki shi ma ya bar Haseenah wajen tsaye baki bude kamar an dasa ta.... Wanka yayi ya shirya ya fito parlon, sai ga Badiyyah ta shigo parlon ita ma rike da kwanukan da ta shiga daki da su bayan ta siɗe tass kamar dama a yunwace ta tashi, tana ganin Maheer zaune parlor tace "Yaya aiki zaka tafi?" Yace "Ehh" Tace "Don Allah nima sai ka ajiye ni a school, yanzun nan zan shirya" Yace "Ohk har kin warke kenan" ta sinne kai tana murmushi tace "Ehh hannun kawai ke ciwo amma zan iya zuwa school din" Yace "To kar ki bata min lokaci" Haseenah dake zaune kan kujeran dinning ranta a mugun bace ta dinga bin su da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunani zata yi, Maheer na ta jiran Badiyyah a parlor har ta fito, daga ita har shi babu wanda ya kalli inda Haseenah take suka fita daga parlon. Yana ajiye Badiyyah a bakin gate din school din nasu ta kallesa da sauri tace "Aa yaya bakin gate kuma zaka ajiye ni baza ka shiga ciki ba? Da nisa fa department din namu" a takaice yace "Ana jirana a hospital ne" Tace "Toh shikenan" Sauka tayi daga motar ta rufe tana washe masa baki tana daga masa hannu alamar bye bye, ya gyada kai ya ja motarsa ya bar wajen, A ranta tace kai wai ashe dama haka yaya Maheer ke da kirki bata taɓa sani ba?? Ashe ya Maheer is this nyc? Ko da yake dama ita babu abinda ke hadata da shi kuma ko ta gaishesa da can ma yana amsawa, iyaka idan yaga tayi ba dai dai ba yace zai mata fada ita kuma shine bata so, Usman ne kawai ya tsaneta tun asali, kwafa tayi a ranta tana imagining ta tura ma Usman yan daba su rama mata dukan da yayi mata har sau biyu kenan, da sauri ta shiga cikin makarantar tana addu'ar Allah ya sa Dr Musharraf ya shigo school ta samesa a office, sai murmushi take... Maheer kadai yasan yanda yake tausasa zuciyarsa na ganin ya biye Badiyyah ita kuma har ta wani sake jiki da shi abinda ma ke kara ƙona masa rai kenan, da ta san irin mugun haushinta da yake ji da baza ma ta dinga biyesa ba, but babu komai za su ci gaba a haka he knows his target ae, hostel din da Mayraah take ya nufa don sun yi waya da ita not long ago tace bazata je school ba. Da yamma karfe biyar Maheer ya koma gida, har ya iso gidan ma bai sani ba don tunani iri iri suka cika zuciyarsa, ga damuwar Ammi da taki komawa gida duk da Mayraah bata gidan, Abba dama tun jiya da yamma ya bar kanon ya tafi ya ci gaba da harkokinsa ba tare da ya bi ta kan Ammin ba, ga Mayraah kuma da baya jin dadin yanda yake ganinta yasan she is just pretending to be fine karfin hali kawai take, but she look traumatized, he wish yanzu da ne da zai iya rungumeta ya lallasheta sosai ya kwantar mata da hankali amma that is not possible a yanzu kam, handout da tace masa ta karanta cikin dare ya amsa yayi mata tambayoyi bayan yaje wajenta da safe amma ta zuba masa ido kawai with no answer, if things should continue like this yasan zata samu matsala a makaranta, gaba daya yayi confuse ya rasa way out, parking yayi ya shiga cikin gidan, Haseenah na kwance kan doguwar kujera tana danna wayarta, sai ga Badiyyah ta fito daga daki tana kallonsa don ta ji shigowar motarsa, tana huci tace "Wai yaya fa Haseenah bata ma mutane girkin komai ba a gidan nan yau, tun da na dawo da rana babu abinda na ci, gashi yunwa nake ji yanzu...." Ko rufe baki bata yi ba Haseenah ta mike zaune tace "Ke kuturwa ce da baza ki shiga kitchen din ki dafa abinda za ki ci ba" A mugun fusace Badiyyah tace "Kee kar ki gaya min maganar banza a gidan yayana malama, nan din gidan mijina ne da zan dinga shiga kitchen anyhow?? Ba ke ce matar gidan ba, ai ke ya kamata ki dinga ma mutane girki su ci, ko ke a gidanku haka kika ga ake ma dangin miji??" Haseenah ta mike tsaye da sauri tayi mitsi mitsi da ido tana nunata da yatsa tace "Kar ki sake ki sako yan gidanmu a haukanki, kuma bazan yi girkin ba ai ba zamanki nake ba kuma ke din naga ba gurguwa bace da baza ki iya shiga kitchen kiyi girki ba" Badiyyah ta nufota kamar zata tashi sama tace "Ke ni fa ba Mayraah bace da kika rena wllh kika kawo min nonsense zan nakada maki duka a nan kuma babu abinda zai faru, ko kin ga na maki kama da Mayraah? Tun da yaya ya kawonu gidan nan jiya don ya dinga duba lafiyata naga kina bakin ciki, to naga dae ai ba gidan iyayenki na zo ba ko??" Da sauri Haseenah ta kalli Maheer dake tsaye yana kallonsu without saying anything, lokaci daya ta fashe da kuka ta dafe kirjinta tace "Maheer kana jin rashin kunyar da take min kayi shiru??" Maheer yace "Amma ke me ya hanaki girki kin san gidan da bakuwa? Ko dae baki san wacece ita bace in tuna maki?" Badiyyah ta wani karya kai tana girgiza kafa irin yesss din nan, Haseenah ta bude baki tana kallon Maheer with shock babu ko kiftawa, Maheer yace "To ita din ba bare bace, she have all right to ask for food from you in this house, dama don me aka auro ki? In case u don't know my family over everything Haseenah, dole kiyi girki ki bata" Cikin tsawa Haseenah tace "Toh bazan yi ba sai dai duk abinda zai faru ya faru, wallahi bazan girka ma katuwar banza abinci ba, wannan wani irin Fitina ne daga wannan sai wannan? Wani irin aure ne wannan" Badiyya tace "Sae dae uwarki ce ƙatuwar banza ba ni ba" Haseenah ta zaro ido tana kallonta, cakumota take kokarin yi a fusace, Maheer ya dakatar da ita yace "Keee respect ur self" Sai kuma ya kalli Badiyyah dake girgije girgije yace "Dauko Hijab dinki mu je in siya maki abincin" Da sauri Badiyyah ta koma daki ta dauko Hijab dinta, ko da ta dawo parlor taga Maheer har ya fita ya koma mota yana jiranta, Haseenah kuwa na tsaye ta kasa motsi saboda shock, sae zufa take a goshinta, she just can't believe it, Badiyyah na mata wani kallo tana juya ido tace "Yauwa wannan kudin gold din nawa da kika ce za a biya wannan malamin na biyu da shi na fasa, kawai a bani kudin gold dina ko inyi rashin mutunci, dama can ni ba ruwana da harkan Malamai kika wani tashi kika hada ni da Malami" Sai da gaban Haseenah ya fadi tsabar rikicewa da jin abinda Badiyyah ke cewa don murya a sama tayi maganar yanda in dai mutum na balcony ma zai jiyo ta, Haseenah ta dinga kalle kalle da sauri to be sure Maheer baya wajen zuciyarta na wani bugawa, tuni Badiyya tayi wucewarta ta bar ta nan a tsaye, kawai yau ta dawo gida cike da farin ciki don har numberta sai da Dr Musharraf ya amsa bayan ta samesa a office da wani topic a course dinsa amma rashin ganin abinci a gida ne kawai ya ɓata mata mood dinta gaba daya don ita bata wasa da cikinta, bayan tun da take bata taɓa irin wannan farin cikin da tayi yau ba wai a whole Dr Musharraf yayi requesting phone number dinta zai tura mata wani slide ta WhatsApp kawai Haseenah ta wani ɓata mata mood dinta.... Throughout this week was nothing but hell for Mayraah bata yi tunanin zata yi surviving har zuwa ran friday ba, sosai ta rame duk da kokarin da yayyin
Chapter 113 · 0% Book details