Sashe 114
Mayrah Complete Hausa Novel · about 4 min read
nata maza suke don a rana sai su zo wajenta sau biyu sau uku amma ta kasa samun sukuni gata nan gata nan dai ne kawai, ga karatu yaki tsaya mata a kai, she try all her best tayi composing kanta idan sun zo, amma suna tafiya zata koma gidan jiya, taji duniyar ya isheta komai yayi mata zafi, she just want to see her self far away, may be in a another world, kullum da wannan feeling din take kwana take tashi a ranta, amma da taji zuciyarta na ingizata ta aiwatar da hakan sai ta tuna final exams dinta.. Yau Sunday tana kwance ita kadai a daki Ummi ta shiga School karatu wayarta ya fara vibrate, ta jawo wayar taga Dr Musharraf ne, tun da ya kirata Tuesday, Wednesday, Thursday bata daga ba bai sake kiranta ba sai yau Saturday, tana ta kallon wayar har ya katse, ya sake kira, dagaws tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Ki gaya min me na maki kike avoiding calls dina Mayraah? Yayyinki suka hanaki daga kirana ko?" A takaice tace "Saboda me za su hanani daga kiranka?" Yace "Toh gashi nan baki dagawa all this while, we were good, all of a sudden u stopped responding to my calls Mayraah, kin ga dole zan yi tunanin hanaki ɗaga wayata aka yi" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "It's not so, bani da lafiya ne" Da mamaki yace "Really? but i asked Badiyyah about u yesterday and she said u are fine kince a gida zaki dinga karatun ki" Mayraah dai tayi shiru, yace "Mayraah ki gaya min me yake damunki plss?" Tace "Ai na ji sauki" cike da damuwa yace "Pls ina son ganinki yau, where can i meet you?" Tace "Ai zan shigo school gobe" yace "Da gaske?" Tace "In sha Allah" yace "Amma kina karatun sosai kuwa, next week fa exams din ku" Tace "Ina yi, yanzu ma shi nake yi...." a hankali yace "Ohk in kyaleki ki cigaba kenan?" Tace "Yeah" yace "Toh zan kira ki anjima" katse wayar tayi ta ajiye ta ci gaba da kwanciyarta... Washegari karfe goma da rabi Usman ya ajiyeta a school, a parking space ta ga motar Dr Musharraf, Usman na kallonta bayan ta sauka daga motar yace "In kin gama ki kirani" a hankali tace "Ya Maheer yace zai zo ya daukeni" Shiru Usman yayi, sai kuma yace "Ok" ya ja motarsa ya bar wajen, ta shiga department din nasu, sosai gabanta ya fadi ganin Dr Musharraf na saukowa stairs tare da wani lecturer dinsu, tun da ta kallesa sau daya ta sunkuyar da kanta ta rasa dalilin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, shi ma kallonta kawai yake ta cikin glasses din idonsa, ba tare da ta sake kallonsu ba ta gaishesu ta wuce, inda suke sallah a department din ta nufa tana tafiya a hankali, gabanta ya sake faduwa ganin Badiyyah zaune da kawayenta biyu tana basu labari duk sun cika wajen da muryarsu, Badiyyah ta daga kai tana kallon Mayraah da mamaki, ita wllh har ta manta da ita a duniya, mamaki ta dinga yi tana tunanin daga ina kuma take haka, dama tana nan ashe, can ta wani kyabe baki ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take basu, da har Mayraah zata juya ta bar wajen sai kuma dai kawai ta zauna ɗan nesa da su ta ciro handout dinta tana kallo amma surutunsu duk ya cika mata kunne, Badiyyah tace "In gaya maku har karfe dayan dare we were chatting with him wallahi tallahi" Kawarta Aisha tace "Shi Dr Musharraf din?" Badiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi nake gaya maki, bari ma ku ga" da sauri ta ciro wayarta ta shiga WhatsApp tana nuna masu chat dinta da Dr Musharraf, duk suka zaro ido da mamaki suka ce "Whatttt" Badiyyah dai sai murmushi take ta mayar da wayar jakarta, sai kuma ta fito da wani tsadadden foreign coffee a kwalinsa tace "Toh da yace min yana son coffee shine na dauko masa wannan coffee din a gidan yayana in basa, kun san yanzu gidan Maheer nake for almost a week now, shine ma ke kawo ni school yanzu, dama warce ta shiga tsakaninmu da su yanzu an koreta a gidan, familyn mu ya dawo dai dai yanzu, don haka sai kun ga yanda Maheer ke ji da ni a gidansa wllh tllh, sai ma da na gaya masa zan dauki coffee din kafin in dauka" Aisha ta zaro ido tace "Ke ga Dr Musharraf din na hango ashe ya shigo school din" Badiyya tace "Kai haba" Aisha tace "Wallahi kuwa na ganshi yana tafiya upstairs" Badiyyah ta ciro powder dinta da sauri ta shafa sannan ta fito da wani turare a kwalba ta shafa tace "Bari in kai masa Coffee powder din yanzu kawai" Sai da ta kusa taka Mayraah da gangan sannan ta bar wajen, ita dai Mayraah kanta na kasa tana jin duk hiransu, ta dai kafa ma takardan hannunta ido babu ko kiftawa......