Sashe 24
Mayrah Complete Hausa Novel · about 4 min read
suka yi sallama, Mayraah ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Har tayi bacci ta tashi wajejen karfe uku da rabi Musharraf bai kirata ba, nan taji ta shiga damuwa sosai, bandaki ta shiga tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, sai da tayi la'asar bayan lokaci yayi sannan ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa ya daga, Nan da nan ta hade rai kamar yana ganinta tace "Why are u not picking my calls since morning?" Yace "Ba na ce maki bana jin dadi jiya ba" cike da damuwa tace "Har yanzu? Did you go to the hospital?" Yace "Ban je ba" Tace "Toh wani magani ka sha?" Yace "Ban sha ba" Shiru tayi sai kuma tace "Baka da lafiya kuma baza ka sha magani ba?" A hankali yace "Babu maganin" Tace "Mami fa?" Yace "Tana gida" Da mamaki Mayraah tace "Kai kana ina?" Yace "Bana gidan" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Why are you answering that way?" Yace "How am i answering Mayraah?" Ta dan buda ido tace "Kana ina yanzu?" Yace "I need rest so i am not at home..." Tace "Nasani, cewa nayi kana ina?" Yace "Nan din da nake ma gida ne...." Tace "Ohk, now tell me how you are feeling" Yayi shiru, hakan yasa tace "Hello" Yace "Ina jin ki" Tace "Kayi shiru" Yace "I should tell u how i am feeling?" Tace "Eh" Yace "Ohk i am not feeling fine Mayraah" Da damuwa sosai tace "Don Allah ka gaya min how you are feeling, idan bazaka gaya min ba kuma ka aika wani da prescription ya siya maka magani ka sha" Yace "Wa zan aika?" Tace "Kai kadai ne a gidan wai?" Yace "Yeah" Tace "Amma me yasa zaka zauna gida ba kowa bayan baka da lafiya?" A hankali yace "U said i should get enough rest Dear, shi yasa na zo nan" Mayraah tace "Ni bance kaje inda babu kowa ba" Yace "Ohk ai ban sani ba" Tace "To yanxu ka ci abinci?" Yace "Wa zai bani?" Ta zaro ido tace "Since morning?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Can i go out and get u some food now?" Bayan shirun few seconds yace "Ohk, with the drug" Mayraah tace "In sha Allah" Daga haka ta katse wayar. Mikewa Mayraah tayi ta ciro kayanta a press, within few minutes ta shirya ta saka Hijab dinta har kasa sannan ta saka Nikab, ta dau handbag dinta ta duba ciki to make sure her Atm card is inside, ta zura wayarta a ciki sannan ta fita daga dakin, tsaye tayi bakin kofa tana tunanin inda zata ce ma Ammi zata je, gashi ita in dai zata yi ma Ammi karya sai ta kamata don bata iya karyan ba ma, A hankali take tafiya zuwa Bedroom din Ammi gabanta na faduwa, tayi sallama a bakin kofar sai da aka amsa mata sannan ta shiga, Ammi da Aunty Mariya kadai ne a dakin suka daga kai suna kallonta, da mamaki Ammi tace "Ina za ki?" Mayraah tayi karfin halin karasawa kusa da su gabanta na ci gaba da faduwa sosai, ta durkusa kasa tace "Ammi zan je in siyo abu in dawo yanzu" Ammi tace "Me zaki je ki siyo?" Da kyar tace "Wani material na karatun mu" Ammi tace "Karya kike yi Mayraah, gaya min inda za ki dai" Mayraah ta marairaice tana tunanin inda zata ce mata zata, Aunty Mariya tace "Ko dai wajen kawayenki zaki?" Nan da nan idea ya zo ma Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Ammi kiyi hakuri, wajen Hamida zan je" Ammi tace "Shine sai kin min karya tukun, kuma tun safe baki ce zaki gidansu Hamida ba sai bayan la'asar kina ganin gari na neman lullubewa da hadari, bayan kuma kinsan unguwansu da nisa sosai daga nan, ki bari kawai gobe idan Allah ya kai mu" Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi with pleading eyes tace "Nayi alkawarin bazan dade ba Ammi" Aunty Mariya tace "Kawai ki bar ta Ammi tunda tace bazata dade ba, kilan shirye shiryensu za su yi, kawai dai kar ta wuce karfe biyar a gidan" Ammi tace "Wani karfe biyar, Allah sa zuwa biyar din ta isa gidan, can fa gaban unguwa uku ne, kuma ai ita Hamidan ya kamata ta zo, ba wai ta bi ta gidansu ba" Aunty Mariya tace "Ke dai kiyi hakuri ki barta Ammi, nasan dai Mayraah ba fita take ba idan ba kwanan nan ta canza ba, tunda tace sharp sharp zata je ta dawo kawai ta tafi, Allah ya tsare" Ammi dai tayi shiru, can tace "Amma me yasa baza ki bari gobe ba Mayraah?" Mayraah tace "Ina son inje yau ne don akwai reading material dina da zan amso wajenta ran monday muna da test kuma ban yi karatu ba" Ammi tace "Shikenan, Allah ya tsare, amma kar ki jima Mayraah kinga yamma tayi ga hadari, kina gama abinda zaki yi ki kira Maheer yaje ya dauko ki, kar ki wani ce zaki shigo adaidaita sahu" Mayraah tace "To Ammi nagode" Ammi tace "Kina da cash dai ko?" Mayraah tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kin dawo" Mikewa tayi ta ma Aunty Mariya sallama sannan ta nufi kofa duk suka bi ta da kallo.