Sashe 102
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
[7/1, 5:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya zauna parlon bayan ya shigo yana kallon Ammi ganin bai ga Haseenah ba yace "Ta sauka downstairs ne?" Ammi tace "Aa sallah take a daki" mamaki yayi don yasan sun yi magrib before leaving home, a ransa ya fara tunanin to sallan me kuma take tunda dai ko isha ba a kira ba, bai dai ce komai ba yayi shiru, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Uwar daƙan naki ta shiga tayi sallah duk girman parlon nan?" Ammi tayi kamar bata ji ta ba don tasan Mama Ladi da ɓarin zance, Mama Ladi tace "Ikon Allah, to bari in je mu gaisa a dakin" Dakin ta nufa ta bude kofa a hankali ta shiga, salati Mama Ladi ta saki tana gwale ido, Maheer da Ammi duk suka juya suna kallonta da sauri, Mama Ladi na tafe hannu tace "To dai wani wajen daban ta kalla take sallah ba gabas ba, ita bata tambaya idan abu ya sha mata kai??" Ammi tace "Ai bata sani bane Mama Ladi" Maheer ya mike yana kallon Ammi yace "Idan Mimi ta shigo ki ce ta shirya za mu wuce" Daga haka ya fita daga Parlon, Haseenah na murmushi bayan ta katse sallan ta juya tana kallon Mama Ladi, tsabar yanda gabanta ya fadi sai da hannunta dake cikin hijab ya fara rawa, cike da karfin hali tace "Ban sani ba Mama, ina ne gabas din?" Mama Ladi ta nuna mata sannan ta koma parlor, kusa da Ammi ta zauna murya can kasa tace "Amma a zancen gaskiya bai kamata ki bari ta shigar maki daki ba, da sai a mata shimfida a nan tayi sallahn, duka duka yaushe ma aka yi auren har aka gama sanin halinta zaki tura ta dakin ki wai tayi sallah, kawai ni dai jikina bai yarda da ita ba tun ranan da na fara ganinta lullube a mayafi...." Mikewa Ammi tayi don bata son zancen tace "Ina zuwa Mama Ladi" Daga nan ta fita daga parlon, Mama Ladi ta kyabe baki tace "Ai shikenan, tunda an maida ni gantalalliya" Bayan isha za su tafi Ammi ta bi Maheer har downstairs tana tsaye kusa da shi tace "Maheer pls ka dinga bin Mimi a hankali, ka ga she is just recovering kar ka sake birkitata don Allah, in dai Musharraf ne pls kar kace zaka hanata mu'amala da shi, after all he is still her lecturer and she is still in school, it's none of their fault that this happened, kuma don an rabu ai baza a ki zumunci ba ko" Maheer dai sauraronta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, Ammi tace "Magana nake maka kayi min shiru" A hankali yace "Toh Ammi" Har mota Mama Ladi ta rakasu tana washe baki bayan Maheer yayi mata alkawarin zuwa ya dauketa ranan juma'a, sai tayi sati a gidansa... Haseenah sai hira take jan Maheer da shi happily bayan sun bar gidan bini bini kuma sai ta kyalkyale da dariya, ita dai Mayraah na zaune bayan mota tana danna wayarta, Maheer ya kalli Haseenah don dariyar nata ya fara yawa yace "Farin cikin meye haka kike ne?" Tayi wani dariyar tace "Na zo na gaida Ammi na ji dadi mana, ai tamkar Mumy nake jin Ammi a raina" Bai sake ce mata komai ba har suka isa gida, yana parking ta sauka daga motar, Mayraah ma ta sauko zata dau warmers din abincin da suka taho da shi daga can gidan, Haseenah tace "Kawo daya in taya ki da shi" Ba Mayraah ba har shi Maheer sai da yayi mamaki, Mayraah ta bar mata daya, ita ta dau dayan, a haka suka nufi cikin gidan.... Mayraah na office din Dr Musharraf washegari wajen karfe goma tana masa bayanin wani course dinsu dake bata tough time using her understanding, ko handout babu a gabanta but the way she is explaining in details zaka ce takarda na gabanta, kallonta kawai yake yana mamakin irin brain dinta, she is really intelligent he must admit, kwankwasa office din aka yi duk suka juya, ya tambayi waye suka ji muryar mace, nan da nan Mayraah ta gane muryan, yayi mata izinin shigowa ta shigo, lokaci daya kamshin turarenta ya cika office din, yau ma sanye take da atamfa riga da skirt sai mayafinta dake rataye kanta, ta gaishesa da ladabi tana sinne kai, ya amsa yana kallonta yace "Morning Badiyyah, how are you" Tace "Fine sir... Dama sir wani tambayar zan maka ne if u are less busy" Dr Musharraf ya kalli Mayraah da ta hau danna wayarta without raising her head, sannan ya kalli Badiyyah yace "Ohk, can you come back in the next 30 minutes?" Tana gyada kai tace "Sure sir, thank you" Ya gyada mata kai yana kallonta yace "You are welcome" Juyawa tayi ta fita ta kullo office din tana murmushi, Dr Musharraf ya kalli Mayraah yace "Go on dear, ina jin ki" Ta kashe wayarta without looking at him tace "I think a nan na tsaya, sai na ci gaba da karatun before going further, let me go and continue now" Yace "Haba sauran ma zaki iya mana, kawai ki ci gaba nasan ai kin karanta course din during test" Ta dau handbag dinta tace "I am serious nan na tsaya, yanzu zanje in ci gaba" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk, idan kin ga Badiyyah around the premises ki ce ta shigo" Mikewa Mayraah tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Ohk" Daga haka ta fita daga office din. Tana sauka downstairs taji gaba daya makarantar yayi mata zafi, ta kasa zama cikin department din har sai da ta fita waje, rasa inda ma zata je tayi, ta zauna karkashin wani bishiya, kawai sai taji hawaye ya cika idonta, nan da nan ta goge da sauri, ta ciro wayarta a jaka, tun da suka yi exchanging number da Maleeha basu taɓa waya ba sai chatting, yau kawai tayi dialing numberta yana fara ring ta daga, bayan sun gaisa Mayraah tace "Kin shiga school ne yau?" Maleeha tace "Aa ina gida wllh" A hankali Mayraah tace "Ohk, i tot u are in School" Maleeha tace "Why not come over to our house ba wani nisa fa daga school din" Mayraah tayi murmushi tace "Aa next time" Maleeha tace "No plss, don Allah ki zo tunda kinyi niyyar mu hadu" Shiru Mayraah tayi, Maleeha tace "Pls ki samu mai adaidaita sahu sai in gaya masa address, muna nan tudun yola fa, kinga ai ba nisa sosai" Mayraah tace "Ohk zan zo" Cikin minti sha biyar Mayraah ta isa gidansu Maleeha, Maleeha tayi farin cikin ganinta sosai, suka shiga parlonsu, Maleeha da mai aikinsu kadai ne a gidan duk parent dinta sun fita aiki, gisting with Maleeha made Mayraah felt relieved taji hankalinta ya kwanta sosai, tana gidan har aka yi azahar, bata yi niyyar cin abinci ba amma sai da Maleeha ta tursasa ta ta ci, suna cin abincin Mayraah tace "Plss Maleeha kar ki gaya ma Ya Usman na zo gidanku yau fa" Maleeha tayi shiru tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace "Ai muna dadewa bamu yi magana da shi ba" Mayraah ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "How?" Maleeha tace "Nothing.... he is just a frnd fa, Colleague din yayana ne, so i knew him through my brother, once in a while yana zuwa gidanmu" Mayraah tace "Wai ba soyayya ku ke ba?" Maleeha tace "At all, wai don coincidentally ya kai min abinci school ranan tare da ke? Yayana fa na kira ranan suna office tare sai nayi requesting abincin sai yayana yace he is busy, shi kuma sai ya kawo min amma wllh ba soyayya muke ba, ko chatting muna jimawa bamu yi ba" Mayraah was speechless, A hankali Maleeha tace "But i must confess to u Mayraah, i love ur brother amma shi bai san ina yi ba" Mayraah tayi murmushi tana kallonta tace "Then why not shoot ur shot dear" Maleeha tace "Hmmm, i am afraid" a hankali Mayraah tace "U need not to be Maleeha, zan so ace kun yi aure da yayana" Maleeha ta kauda zancen kawai ta kawo wani hiran. Karfe biyar saura Mayraah ta isa gida bayan ta bar gidansu Maleeha, tun fitowarta daga gidan gaba daya mood dinta ya canza, sai a sannan ma ta kara tuna cewar Dr Musharraf bai kirata ba all through, tayi kokarin yakice damuwar nan a ranta, bata ga motar Maheer a parking space ba bayan ta isa gida, ta zauna compound for some minutes don kawai sai taji bata son shiga gidan, kasa ci gaba da zaman tayi saboda damuwar dake tare da ita, taji kawai kwanciya take so tayi, mikewa tayi duk da yanda gabanta ke faduwa ta karasa balcony tayi using spare key da Maheer ya bata ta bude kofar parlon, zaune ta tadda Haseenah da Badiyyah a parlon duk suka juya suna kallonta, ta sauke idonta kasa ta cire takalminta a bakin kofar parlon zata wuce dakinta Haseenah ta mike ta sha gabanta tana mata wani matsiyacin kallo tace "Ke gidan ubanki ne nan din da zaki shigo mana babu sallama sannan ki saka kai zaki wuce daki kamar kin ga marasu asali zaune a parlon? Are you mad?" Mayraah dai tayi shiru tana kallonta, Badiyyah tayi wani dariya ta mike tace "Kinsan duk inda mara galihu yake to yafi masu galihu iya shege banda haka mu sa'anninta ne da zata wuce bata gaishe mu ba? wallahi na rasa jin kan me yarinyar nan take har yanzu bayan tasan mummunan history dinta, da nine ita da nikab zan dinga yawo a gari on a serious note, duk department yanzu an san bata da asali kuma Shegiya ce" Juyawa Mayraah tayi da zuman fita ta bar masu parlon, Haseenah ta fizgota a fusace ta cakumi hijab dinta tace "Don ubanki mu zaki yi walk out on muna maki magana ko dai codeine kike sha ne??" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can tace "Pls take ur hands off me" Bata rufe baki ba Badiyyah ta wanka mata mari me kyau a fuska, Haseenah ta kara mata a other cheek din tace "Ni kike gaya ma i should