← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 145

Sashe 141

Mayrah Complete Hausa Novel · about 2 min read

yi Hajiya Amina ta shigo da sallama da basket din breakfast, Mama Ladi ta amsa sallaman, Hajiya Amina ta gaisheta da ladabi, Mama Ladi tace "Lafiya lau" Hajiya Amina tace "Ya kwanan takura" Mama Ladi tace "Wani kwana er nan? Ni ina naga ta bacci an bar min amanar yarinya, ke dai kawai ayi sha'ani, ita kam dai ta sha baccinta" Hajiya Amina tace "Allah sarki, dama gida zaki tafi yanzu ki samu kiyi wanka ki karya sai ki kwanta kiyi baccin ki huta" Mama Ladi tace "Aa ni ba sai na wani je gida ba, abinda in da sabo na saba, sae in iya kai wa wani daren a haka ma" Hajiya Amina tace "Toh bari in zuba maki abincin kawai ki karya" Mama Ladi tace "Yauwa to, dama yunwa nake ji" Karfe takwas Musharraf ya shigo ward din har yaje gida yayi wanka ya dawo, Mama Ladi na kallonsa tace "Yau naga bala'i sake dawowa kayi ɗan nan? Ba nace ka tafi mun gode ba" Hajiya Amina tace "Mama naji fa Alhaji yace malamin makarantarsu ne, shi ne ma ya kawota asibitin" Mama Ladi tace "Ayyoo to kai ba sai kayi bayani ba, wallahi na zata irin gayun nan ne masu zaman banza, naga sai sintiri yake kamar yana son a biyasa abinda yayi, ashe malami ne sannu kaji yaro" Musharraf dai murmushi kawai yake ya karaso, tana kallonsa tace "Ai tun da ka tafi ka bar mu wajen karfe sha biyun nan har yanzu a haka nake, hana rantsuwa dai na ɗan gyangyada" Musharraf ya dinga kallonta babu ko kiftawa.
Chapter 141 · 0% Book details