← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 145

Sashe 84

Mayrah Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta bi ta da kallo, Maheer yace "Sai na dawo" Kin ce masa komai tayi tsabar bacin rai, shi dai ya nufi kofa ya fita, fuuuu ta juya ta koma dakinta. A hanya Maheer na driving wayar Mayraah dake kafarta ya fara vibrate, ya juya yana kallon screen din wayar, tayi silencing kiran bata daga ba, bayan tafiyar kusan minti goma Maheer yace "You are going to school because of him right?" Ta ɗan kallesa da mamaki tace "Why because of him?" Maheer yayi shiru yana ci gaba da driving dinsa, can yace "Toh mu tafi asibiti mana, don nasan ko kinje school babu abinda zaki yi sai kwanciya, i know how u behave during this period of the month...." Mayraah tace "Makaranta zan je i can cope" Bai sake ce mata komai ba har suka isa makarantar, yana isa gaban department yayi scanning parking area din da ido har ya hango motar Musharraf, kashe motarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, Mayraah ta juya tana kallonsa ganin bai bude motar ba, can dai da taga ba shi da alamar budewa tace "Yaya i am late fa" Tada motar yayi without looking at her ya fara reverse yace "Baza ki shiga school din nan yau ba Mimi, when I know babu wani lectures da zaki iya zama a class kiyi attending" Ta marairaice tace "No plss yaya, nace maka fa zan iya wllh" Bai saurareta ba ya ja motar suka bar department din, nan da nan hawaye ya cika idonta ta dinga kallonsa, shi dai bai kalleta ba har suka fita daga school din, ya dau hanyar asibitin da yake aiki..... Har suka isa asibitin Mayraah share hawayen da ya ki tsaya mata take, kiris ya rage ta fashe da kuka, bayan yayi parking ba tare da ya kalleta ba yace "Wajen Dr Musharraf za ki je ba lectures ba, if i may ask, do u still have any business with him?" Bai jira me zata ce ba ya sauka daga motar, ta fashe da kuka sosai, ya zagayo ya bude mata motar yace "Sauko" Ta hade rai ta sauko ya kulle motarsa, yace "Mu je" Tafiya ta fara yi yana biye da ita suka shiga cikin asibitin, gaba daya nurses din sun santa don banda yanzu da karatu yayi mata zafi a da asibitin is like her second home barin idan yana da aiki weekends, to a nan take spending weekend dinta ita ma, tayi composing kanta suka gaisa da nurses din gaba daya ta bar sa reception tsaye ta nufi office dinsa... Tana tsaye ya karaso ya bude office din ta shiga ciki ba tare da ta kallesa ba ta tafi inda take kwanciya duk sanda ta zo, hawaye kawai take a inda take kwance ga ciwon ciki da ya takurata sae juye juye take, kiran Musharraf ya shigo wayarta for the second time tun shigowarsu asibitin, ta mike zaune a hankali tana kallon screen din wayar, leka office din Maheer tayi da yake anyi demarcating inda take kwance da main office din, ta gansa zaune office chair dinsa yana attending to a lady with her baby, Daga kiran Dr Musharraf tayi ta kai kunne tayi shiru, Daga daya bangaren yace "Mayraah" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Ya Maheer yace bazan je school din ba kuma" Shiru Musharraf yayi, bayan few seconds a hankali yace "Ohk" Shiru suka yi gaba daya, can Musharraf yace "Hope you are feeling much better now?" Ta gyada masa kai tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara lafiya, sai anjima" Nan da nan jikinta yayi sanyi wasu hawayen suka cika idonta, ta ji ya katse wayar, leka office din Maheer tayi ta gansa shi kadai yana rubuce rubuce, ta zabga masa wani harara kamar yana ganinta, dai dai nan ta ga ya mike ya nufo inda take, da sauri ta goge idonta ta koma ta kwanta ta juya baya ta rufe ido, yana isa wajen ya leka fuskarta yace "Mimi" taki bude idonta, yace "Ina jin ki fa kina waya not long ago" Mayraah tayi still jin abinda yace, sai a sannan ta tuna how sharp his hearing is, ta mike zaune fuskarta babu walwala, yace "Cikin na ciwo har yanzu?" Ta gyada masa kai kawai, yace "In maki allura?" Ta kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa ya juya, sai kuma yace "Bari in kira Amina ta maki" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga office din, sae da ya sa ta ɗan ci abincin da aka siyo mata sannan Nurse Amina ta mata alluran, ko minti ashirin ba ayi da mata alluran ba bacci ya dauketa, don dama ana mata alluran take ji kamar an zare mata ciwon... Tun da Maheer ya fita tare da Mayraah Haseenah ta rasa sukuni, tasan zuwa yanzu dai Badiyyah ta kamo hanya, kuma tana zuwa gidan nan tunda har Mayraah bata nan dole hankalinta zai koma kan zancen gold, gaba daya ta rasa yanda zata yi, daga karshe dai ta saka Hijab dinta ta fita compound da sauri, gun mai gadi ta nufa yana gaisheta ko amsawa bata yi ba tace "Malam ya sunanka?" Da ladabi yace "Musa Hajiya" Haseenah tace "Ohk, akwai wata mata da zata zo gidan nan at anytime, zaka ganta doguwa tana da haske, sannan bata kai ni jiki ba, to tana zuwa kace mata babu kowa a gidan kai kadai ne" Mai gadin yace "An gama Hajiya, in sha Allahu" Haseenah ta juya ta koma ciki, wayarta ta dauka ta rufe layin da Badiyya ta san ta da shi yanda tana kira zata ji switch off, sannan tayi dialing number kawarta kuma aminiyarta Salima, Salima na dagawa Haseenah ta saka wani uban shewa tace "Kawata ayyuka sun yi kyau fa ta ko ina in gaya maki" Salima tace "Kai haba, bani labari in sha" Haseenah ta gyara kwanciyarta tana murmushi tace "Wallahi in gaya maki ya dawo yanda kika san wani bita zai zai, kin ma san nawa ya tura min a account jiya da nace masa bani da kudi? Wallahi tunda nake da shi bai taɓa tura min irin kudin ba" Salima ta saki guda tace "To maza a ciko min kudaden mutane in kai masu" Haseenah tace "Kai wannan ai dole ne, don Allah wacece wannan me siyar da kayan nan??" Salima ta kwashe da dariya tace "Aa wallahi bazan fada ba, kinsan babu boye boye tsakanina da ke to nima wllh sarowa nake wajenta in ɗan yi mix sannan in daura nawa riban in siyar, yanzu in na gaya maki ai gun ta zaki nufa direct gashi nata shine sadidan haka kawai ki saka bawan Allah ya zama makale mata ki ja a koresa aiki, gwara dai ki tsaya iya nawa me mix" Haseenah tace "Kai kawata, wallahi ni ko biyanki kika ce inyi sai in biyaki ki bani numberta, fadi price in tura maki yanzu" Salima ta kwashe da dariya tace "Yanzu duk ba wannan ba, Hajiya cikon kudin Malam fa? Kinsan fa har da nasa aikin, ko kinji ya sake maki wancan maganar me muni?" Haseenah tace "Cewa ma yayi sharrin shaidan ne wllh, kar fa ki ji komai duk zan tura kudin casss, sannan akwai ma wani matsalar yanzu haka Salima, amma kinsan ance the wall have ears, don haka mu yi chatting kawai" Salima tace "Toh shkkn bari in kunna data" Katse wayar Haseenah tayi ta bude WhatsApp dinta. After sleeping all day Mayraah ta bude idonta a hankali ta dalilin hannun da taji a forehead din ta, suna hada ido ta mike zaune da sauri tana murza ido tana kallonsa, yace "How are you feeling?" A hankali tace "Alhamdulillah, ina yini?" Yace "Lafiya lau" Maheer ya karaso wajen nasu yana kallonta yace "Are you okay now?" Ta gyada masa kai, Usman ya juya ya koma kan kujera ya zauna, Maheer yace "Me za ki ci?" Usman yace "I will get her, idan mun fita, it's getting late now" Maheer yace "Ohk, baza ki shiga bandaki ba, za ku fita da Barrister" Mayraah ta kalli Usman, sai kuma ta sauko daga kan gadon ta dau handbag dinta ta nufi bandaki, zata iya daukan pad a gaban Maheer but not Usman tun tasowarta, Maheer dai ya bi ta da kallo ya koma office chair dinsa ya zauna, ko da ta fito daga bandaki Maheer kawai ne a office din, yana kallonta yace "Yana jiranki a mota" Ta marairaice tace "Ina za mu je yaya? Kasan bani da lafiya" Maheer yace "Ai ba dadewa za ku yi ba, zai dawo da ke soon" Ta ɗan yi shiru, sai kuma ta nufi kofa ta fita......
Chapter 84 · 0% Book details