Sashe 63
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
mu daya fa yanzu a nan a zaune, wacece wannan ka aura haka Maheer? Ko har an fesa mata daga karaye nake ne take kokarin kawo min raini?? Shi fa karayen nan ba kauye bace don ma ku ji in fada maku" Usman ya mike ya nufi kofa ya bar parlon, Mama Ladi tace "Tada motar ga mu nan fitowa yanzun nan Usman...." Maheer yyi kasa da murya yace "Mama yanzu fa zata fito, ae nasan wankan take ne" Mama Ladi ta mika masa jakarta tace "Oho ko ma canza fata take, ni dai gashi kwaso min gara in san inda dare yayi min" Maheer ya amshi jakar yace "Mama kin san yanda mata suke dadewa a bandaki fa, yanzun nan zaki ga ta fito" Bai jira me zata ce ba ya tafi kitchen din, Haseenah ta mike zaune daga kwancen da take tana nazari, to ko ba komai ai zata so taga wa enda suka zo gidan, hijab dinta ta dauka ta saka sannan ta fito parlon, da Mayraah ta fara hada ido, wani irin faduwa gabanta yayi da farko ta kasa karasowa, Mayraah ta dauke idonta, Haseenah ta karasa parlon tana tafiya a hankali ta zauna empty chair ta gaishesu kamar me ciwon baki, Mama Ladi na kallonta da kyau tace "Mijin naki bai gaya maki mu su waye bane halan?" Ta dan girgiza kai ba tare da tace komai ba tana ɗan juya ido, Mama Ladi tace "Toh kanwar kakarsa ce ni uwa daya uba daya, ita kuma wancan da kike gani kanwar uwarsa ce uwa daya uba daya, ta gefenta kuma kanwarsa ce, sai dai kawai akwai aure a tsakaninsu ne a yanzu ba kamar yanda kika sani ba a baya, yanzu abubuwa sun canza, duk da dama mu mun san da auren tsakaninsu su ne dai basu sani ba, amma kanwarsa ce halaq malak" Sosai gaban Mayraah ya fadi, sai dai na Haseenah ya fi nata faduwa, Mama Ladi ta ci gaba tace "Shine dama nace a kawo ni in ga gidan ɗa na in sa albarka, ba wai zuwa nayi takanas saboda ke ba, tunda ai na ganki a can gidan" Tana kai wa nan ta mike tace "Mariya zaga da ni in ga gidan mu yi wucewar mu" Ko gama mikewa Aunty Mariya bata yi ba Mayraah ta mike, Mama Ladi tace "Yauwa mu je har ke kika gidan yayan naki..." kitchen suka ga Mayraah ta nufa, Mama Ladi tace "Au to, ganawa zata je tayi da yayan nata, mu je Mariya" Haseenah ta dinga bin Mayraah da kallo zuciyarta na bugawa, Aunty Mariya ta bude wani spare room tace "Wannan dakin baƙi ne ina jin" Mama Ladi tace "Waiii gashi da girma kuwa, kinga ai ko hutu aka yi Mera zata iya zuwa nan tayi hutun ta idan can gidan ya isheta" Mayraah na shiga kitchen din Maheer dake ta deban chin chin da cokali yana saka ma Mama Ladi a jakarta ya juya, he was surprise to see her, ita kanta sai ta daburce ta fara kame kame tace "Dama, dama yaya ina son ka ara min wayarka ne" Maheer yace "Did u misplaced urs?" Ta gyada masa kai, yace "To anjima zan kai maki wani gida, wanne kike so?" Shiru tayi tana wasa da handle din kofar kitchen din, yace "Ohk nama san wanda kike so" Ta ɗan kallesa tace "To wanne?" Yace "Idan na kai zaki gani" Ita dai bata sake cewa komai ba, yace "Zo ki debar mata snacks din ban san yanda ake yi ba" Karasawa ciki tayi, ta amshi jakar sannan ta fara debo kayan garan tana zubawa a ciki, yana tsaye gefe yana jiran ta gama zubawa aka bude kofar kitchen din, Haseenah na huci cikin daga murya tace "I am not going to tolerate this Maheer" Maheer kallonta kawai yake, Mayraah bata ko dago ba ta dinga zuba ma Mama Ladi alkakin da take, Haseenah ta karaso cikin kitchen din jikinta na wani tsuma tsabar bacin rai ta ci gaba da cewa "Bazan dauka ba wallahi, bazan yarda wata banza da baku hada komai da ita ba ta dinga shigo min gida...." Sai a sannan Maheer yace "Kin san wani abu Haseenah? Za ki iya yi min rashin kunyanki, ki gaya min duk abinda ranki yake so in dauka, amma kar ki kuskura ki sa Mimi a rashin hankalin ki don a nan ne ranki zai yi mugun baci wallahi, ki cire Mimi a bakin ki" Cikin daga murya Haseenah tace "Do ur worst Maheer, nace do ur worst, ba Mimi ba Momo, na sa ta a baki din yi abinda zaka yi in ga, kuma karya nayi ne? Ko da abinda ka hada da ita banda kasancewarta er uwarka musulma? To wa ma yasan ko kafura aka haifeta, A yanzu dai Maheer babu wanda bai san wacece ita ba duk da ni ka munafurceni baka gaya min abinda ke faruwa ba da fasa aurenta da aka yi saboda rashin asalinta, to har gida ake samu na a gaya min duk abinda ya faru, kowa yasan bata da asali, er tsintuwa ce kawai warce ma ba a san ta hanyar da aka sameta ba" Kallonta kawai Maheer yake babu ko kiftawa, Haseenah na tafe hannu tace "In sha Allahu kuma sai ta zama abun kyama a al'umma, don dama irinsu ai abun kyama ne tunda a walakance aka yasar da ita, kai kanka sai kaji gwara ka saka makiyin ka a ido da ka saka ta a ido, sannan tun ma kafin haka sai ta fara nuna maku cewar ita tsintattciyar mage ce...." Haseenah na kai wa nan ta fice daga kitchen din tana huci, Sai bayan kusan second ashirin Maheer ya iya juyawa ya kalli Mayraah, kulle jakar hannunta take kokarin yi, duk da idonta a kasa yake but he can see the tears filled in her eyes, lokaci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya ma rasa me zai ce mata, ta ajiye masa jakan hannunta a kan cabinet ta nufi kofa ta fita daga kitchen din, har sannan su Mama Ladi basu fito parlon ba, Haseenah da ta kasa zaune sai safa da marwa take a parlon zuciyarta na wani irin ƙuna ta bi Mayraah da ta nufi kofa da kallo, har ta fice daga parlon, wani murmushi Haseenah tayi ganin har da hawaye a idonta, nan da nan taji ta samu nutsuwa a ranta ta nemi kujera ta zauna ta sauke wani ajiyar zuciya, Mayraah na isa kofar gida ta tadda Usman a tsaye jikin motarsa ya rungume hannayensa yana jiran 12 dot yayi idan yaga basu fito ba yayi wucewarsa, tun da ta fito yake kallonta, ganin yanayinta yace "Me ya faru?" Ta karaso kusa da motar ta kasa ce masa komai, lokaci daya kawai ta fashe da kuka, da mamaki yace "Ke meye haka?" Kuka kawai take kamar ranta zai fita, kalle kallen wajen ya fara yi yaga babu kowa, yace "Talk to me, an maki wani abu ne?" Still taki ce masa komai sai kuka, ya jawota gefensa yana kallonta yace "Baza ki gaya min me ya faru ba? Me suka maki a gidan?" Still taki cewa komai don kukan ma bazai bari tayi magana ba, ya dawo yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Tell me what happened???" Ganin bazata yi magana ba ya bude bayan motar yace "Shiga ciki" juya masa baya tayi ta hade kanta da motar taki shiga tana rusa kuka, Cikin calm voice yace "Mimi...." Sai a sannan ta juyo ta girgiza masa kai cikin rawan murya tace "Ina son zan je wajen Ammi" Shiru yayi yana kallonta, can yace "To shiga in kai ki" shiga cikin motar tayi hawaye na sauka idonta, ya kulle motar sannan ya shiga front seat ya tada motar suka bar layin, sai da suka hau main road ya kalleta ta madubi, zuwa sannan ta daina kukan ta jinginar da kanta da motar kana ganinta kasan tayi nisa cikin tunanin da ta fada, bai ce mata komai ba har suka isa gida don bai son ya mata magana ta fara sabon kuka. Mama Ladi tace "Ahaf... Ai dama tun suna yara suka iya munafurci, Mera da Usman ba? Sam ai zuciyarsu ba kyau, to banda rashin kyan zuciya mu taho tare rimi rimi ana hira a mota daga karshe ku zame ku yi tafiyarku ku bar mu? To da babu Maheer din wa zai maida mu gida yau, wallahi da na sani ma jiya da ban karesa wajen Hajja ba, don irin dukan da yayi ma Badiyya ya ci ace yana self din yan sanda yanzu haka, da ya sumar da er mutane sai yace me?" Haseenah dake tsaye parlon tana ɗan murmushi tace "Kiyi hakuri Umma, kilan wani uzurin ne ya taso masu" Mama Ladi ta ɗan kalleta tace "Ke kuma wannan magana ai ta pamily ce ba sai kin sako mana baki ba, sun ga za mu ɓata masu lokaci ne yasa suka yi tafiyarsu tunda suna da abun yi" Daga haka ta nufi kofa, tuni dama Aunty Mariya ta fita daga parlon, Haseenah bata ko damu da abinda Mama Ladi ta ce mata ba don ita yau ranta fari tass, tana kallon Maheer da ya bi bayan Mama Ladi cike da shagwaba tace "Sai ka dawo baby, amma don Allah kar ka jima" Yace "Ohk in sha Allah" Daga haka ya fita daga parlon, Haseenah ta zauna kan kujera tana wani murmushi, ita ta ma manta rabon ta ji ta cikin nishadi irin yau.... Maheer na ajiye su Aunty Mariya, Mama Ladi tace "Baza ka shigo ka gaida baabarka ba bawan Allah?" Yana ɗan murmushi yace "Zan shigo anjima da daddare in gaisheta ae" Mama Ladi tace "Duk barin jikin ka koma wajen wancan kodaddiyar matar taka ce haka?" Yayi er dariya yace "Aa ni dai ban ce haka ba" Sallama yayi ma Aunty Mariya yayi reverse ya bar layin. Ko da ya koma gida Haseenah har tayi wanka sharp sharp ta bada tsadaddun turarrukanta a jiki sannan ta dauko wasu shegun kananun kaya ta saka, welcoming dinsa tayi tun daga bakin kofa ta rungumesa, yayi pecking dinta a goshi sannan ya karasa cikin parlon ya zauna, ita ma ta zauna kusa da shi