← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 145

Sashe 128

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

driver seat Ummi ta dinga daga masu hannu har suka bar area din. Mayraah suna isa gida bayan Usman yayi parking ta bude motar ta sauka, haka kawai gabanta ke faduwa sosai, bata taɓa tunanin akwai ranan da zata shigo gidan da take ma kallon comfort zone dinta tun tana er yarinya ba ta dinga jin wannan faduwar gaban da feeling din kanta as a stranger, ya fito da akwatinta biyu bayan ya mika mata karamin jakar, shi kuma ya dau 2 boxes din suka nufi entrance din shiga gidan tana tafiya a hankali har sannan gabanta na faduwa, wnn ya sa ta fara addu'a a ranta har suka shiga parlon, gaba daya an canza fasalin parlon ba yanda yake a ɗa ba, parlon ya dawo sabo fil don har da sabon fenti aka yi, ga wani daddadan kamshin turare da ke tashi a each and every angle din babban parlon, turaren kuma babu hayaki ko kadan sai azababben kamshi me sanyaya zuciya, Usman ma dai ya ɗan yi jim a parlon don har a sannan yasan Ammi bata dawo gidan ba gashi rabonsa da garin kusan sati uku, yana ajiye Boxes din Mayraah wayarsa ya fara ring, ita dai Mayraah na rakube bayan kujera kamar bakuwa tana bin ko ina na parlon da kallo, kawai samun kanta tayi da tunanin she is not a member of this big house anymore fa, ita din bare ce kawai a cikin yan gidan, she is a total stranger yanxu ta kuma yi accepting haka, ta goge hawayen da ya taru idonta tana kallon Usman da ya ciro wayarsa dake ring, dagawa yayi ganin Abba ne, Abba yace "Ku kuka shigo yanzu?" Yace "Ehh" Abba yace "Ohk ku taho parlorna a sama" Usman yace "To" Katse wayar yayi ya kalli Mayraah yace "Meye kike yi haka kamar kin shigo gidan da baki taɓa shigowa ba?" Ita dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Mu je Abba na sama" Bin bayan Usman tayi suka haura sama, Mayraah ta dinga bin Corridor din da kallo don har nan ma anyi fenti, turaren wutan har sama, infact everywhere is soo cool sbda kamshin nan, tana biye da Usman har suka isa parlon Abba, Usman yayi sallama Abba ya amsa sannan suka shiga parlon, Abba na zaune Parlon rike da cup din shayi, Mayraah ta karasa ta zauna kasa kusa da shi tana murmushi ta a kallonsa tace "Abba ina yini" Abba yyi patting kanta yace "Welcome back home daughter, fatan kun gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta gyada kai tace "Alhamdulillah Abba" Abba yayi murmushi yace "Maa sha Allah dear, Allah Ubangiji ya fiddo sakamako mai kyau in samar maki aiki a babban asibiti..." Murmushi Mayraah ta dinga yi don har ranta taji dadin wannan abinda Abba yace, Abba ya kalli Usman dake kallonsu yace "Ya gajiyan hanya barrister?" Usman ya dan shafa kansa yace "Alhamdulillah" Abba yace "Amma na hanaka tuƙin dare baka ji" Usman yace "Wajen 5 muka baro Kaduna, akwai matsala a hanya ne" Abba yace "Toh Allah ya tsare, a dinga kula dai da tafiyar dare pls" Usman yace "In sha Allah" Abba ya dau wayarsa yayi dialing number sannan ya kai kunne, ana dagawa yace "They are around" Daga haka ya katse wayar, ba a wani dau lokaci ba aka bude kofar parlon daga Usman har Mayraah suka daga kai don ganin wanda zai shigo, wata mace ce in her mid 40 ta shigo parlon da sallama, Usman dai sai kallonta yake haka ma Mayraah, matar ta zauna kan kujera cike da fara'a tace "Sannunku da zuwa" Usman ya kalli Abba, sai kuma ya kalleta yace "Ina wuni" Tana murmushi tace "Lafiya lau, barrister ko?" Yace "Eh" Ita dai Mayraah kasa ma gaisheta tayi ta kafeta da ido har sai da matar tace "Mayraah fatan a gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta sauke idonta daga kallonta gaba daya she is confuse, can dai tace "Ina yini" Matar da fara'a yaki barin fuskarta tace "Lafiya lau dear, Allah ya baki sa'an jarabawa a fito da sakamako me kyau in sha Allah" Mayraah tace "Ameen" Usman dai yayi shiru, in ya kalli matar sai ya kalli Abba daga karshe dai ya mike da nufin barin parlon Abba yace "Aa zauna ai ban yi introduction ba" Usman ya koma ya zauna yana kallon Abba, Abba na nuna matar dake zaune yace "Sunanta Hajiya Amina, she is ur new aunt...." Usman ya dinga kallon Abba babu ko kiftawa haka Mayraah da ta jingina da kujera kamar idonta za su fito tana kallon matar da har a sannan take murmushi, Abba yace "A jiya friday aka daura mana aure da ita, few hours ago ta tare, she will continue taking care of the house and the people in it kamar yanda ake yi a baya, for more than a month now the house lack this, zata ci gaba da kula da duk wani welfare din gidan nan, kaga kamar kai da ka biyo hanya tun karfe biyar u need something to eat, so akwai abinci a kitchen yanxu haka, Mayraah ma kaga bazata sake zaman hostel ba akwai warce zata sa mata ido a gida ko da bana nan, ku ma bakwa nan, Umar dake hanya gobe bazai dawo gida babu kowa ba, ka gane ko...." a takaice Usman yace "Allah ya sanya alkhairi, let me take a shower" Yana fadin haka ya mike yana kallon Hajiya Amina ya ɗan yi bowing yace "You are welcome Ma" Tana murmushi tace "Thank you so much dear" Juyawa yayi ya fice daga Parlon ya ciro wayarsa yana dialing number Maheer, Abba na kallon Mayraah yace "Mu je ki ga dakin ki daughter" Mayraah da jikinta yayi sanyi kalau, ta mike da kyar bata sake yarda ta kalli Hajiya Amina ba har suka fita daga Parlon Abba ya kai ta har dakin Maheer yana nuna mata yace "This will be ur new room" shiga dakin kawai tayi Abba ya bar wajen ta kulle kofa, Mayraah ta jingina da kofar hawaye cike idonta ta fashe da kuka, she still can't believe this, kishiya Abba yayi ma Ammi? Did this also happen because of her? Dama tun barin ta gidan nan Ammi bata sake dawowa ba kenan, ita all this while tayi zaton Ammi ta dawo gidan, yanzu fa duk ta dalilinta abubuwan nan ke faruwa kenan, tunanin hakan yasa ta kara fashewa da sabon kuka ta sulale kasa tana jin komai na duniyar ya isheta why is all this happening for her sake, why??? me yasa abubuwa ke ta faruwa because of her. Har kusan karfe goma Mayraah na zaune bakin kofar dakin ko motsi ta kasa yi tsabar yanda ta kidime, taji anyi knocking kofa, da sauri ta mike tana kallon kofar ta goge hawayenta kafin ta bude, Hajiya Amina ta gani tsaye sanye da hijab har kasa, Hajiya Amina na kallonta cike da kulawa tace "Kin ci abinci kuwa?" Mayraah ba ta yarda ta kalleta ba a takaice tace "Na ci" Hajiya Amina tace "Ohk to, sai da safe kenan?" Mayraah tace "Eh" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tashe mu lafiya" Tana barin bakin kofar dakin Mayraah ta hade rai ta kulle kofar ta tafi can cikin dakin ta zauna hawaye na sauka idonta. Washegari Aunty Mariya ta nemi izini gun mai gidanta na zuwa kaduna urgently, yana barinta kuwa ta kamo hanya, karfe tara da rabi ta isa kano ta nufi gidan Hajja, tana shigowa parlon Hajja, Hajja tayi sororo tana kallonta daga sama har kasa, can tace "Lafiya?" Er dariyar karfin hali tayi ta karaso ta zauna, ita kanta Ammi kallon Aunty Mariya take don sai da gabanta ya fadi, Hajja tace "Tambayarki nake lafiya??" Aunty Mariya tace "Wallahi ba komai kawai mun zo wani biki ne na family din mai gidan, tun jiya ai nake kano kawai nace bari in maku surprise shi da ban sanar maku ba" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To kin zo a dai dai kuwa, sai ki raka er uwarki zata koma gidanta yanzu haka ma Maheer take jira na kirasa yace yana hanya, ko don saboda yaran nan gwara kawai ta koma dakinta baza a biye Mamuda ba, Umar din ma wai bai iso ba sai yau" Aunty Mariya tace "Kai Alhamdulillah amma naji dadin wannan labari wallahi ashe na zo a dai dai, dama abinda nake ta son ku gane kenan Hajja, ai ba saboda Alhaji Mahmud zata koma gidan nan ba ko don albarkacin 'ya yanta da yanda hankalinsu ke a tashe ya kamata kawai tayi hakuri ta koma" Hajja tace "Yanzun ma saboda su din ne ai ba wani ba, bazan so wannan yaro Umar ya dawo bata gidan ba babu dadi haka" Maheer ne ya shigo parlon da sallama he look so down kawai karfin hali yake kiran da Usman yayi masa jiya ya basa sleepless night bai taɓa zaton haka daga Abba ba, kawai sai ya dinga tausayin Amminsa, da mamaki yake kallon Aunty Mariya bayan ya zauna yace "Aunty daga ina haka?" Tayi murmushi tace "Daga sama" Yace "Kai amma nayi mamaki fa, babu wanda yace min za ki zo" Aunty Mariya dai ta ɗan yi dariyan karfin hali tace "To ai babu wanda na gaya ma" Hajja ta nuna masa jakan Ammi tace "Ga kayan can ka kai mota" Mikewa yayi ya dau box din ya fita daga parlon ya fita kofar gida ya bude booth ya saka, ya rufe booth din kenan, ya ga adaidaita sahu ya tsaya dai dai gidan, ya dinga kallon adaidaitan don ganin wanene a ciki sai ga Mama Ladi ta sakko da kwarababben akwatinta tana ce ma mai daidaita sahun "To kai yaro Allah ya sa ina da dari biyar din da kace, don wllhi daga ni sai dari da hansin na sauka kano, in zaka hakura ka amsa haka gashi...." Mai adaidaita sahun ya kashe machine din nasa yana kallonta yace "Ban gane ba baaba" Haseenah na kallon Badiyyah dake cin dankali da kwai tace "Ke don Allah Badiyyah?" Badiyyah tace "Wallahi nake gaya makiz ai sai da na bi duk yanda na bi na gano daga inda take zuwa exams, har hostel din sai da naje da nose mask in gaya
Chapter 128 · 0% Book details