← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 145

Sashe 97

Mayrah Complete Hausa Novel · about 2 min read

gidan nan Haseenah? Wannan wani irin kazanta ce? Are you not perceiving d odour coming out from ur body?" Haseenah ta hade rai ta dakatar da shi tace "Aa don't go there Maheer, kai yanzu banda tsabar sharri tun daga can ka jiyo odour dina? Kuma nace maka ban yi wanka bane yau?" Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da dannan wayarsa, ta juya ta fice daga dakin.... Ana kiran Magrib Maheer ya fito, ya bude kofar dakin Mayraah, karatu ya sameta tana yi, ya kulle kofar ya karasa parlor, har a sannan Badiyyah da Haseenah na zaune suna kus kus a parlon, kuma har lokacin basu kwashe kwanukan tsakar parlon ba, ya koma corridor ya bude kofar dakin Mayraah yayi instructing dinta ta kulle dakinta sannan yayi tafiyarsa masallaci, ko da ya dawo daga masallaci Badiyyah ce kadai zaune kan 2 sitter a parlor tana kallo, zuwa yanzu dai an kwashe kwanukan goran ruwa da lemo ne dai ba a kwashe ba, ta daga kai ta kallesa ta ci gaba da kallonta, zaunawa yayi kan 2 sitter din shi ma yace "Ya Hajja fa?" Sai da Badiyya ta kara kallonsa to be sure first, kafin ta ci gaba da kallonta tace "Tana lafiya" Yace "Kinyi resuming school din ko har yanzu kina nan kina gantalin ki?" Tace "Gantali kuma, ni ai kullum ina zuwa school" Yace "Ohk, kin dai ga final semester din ku ne you have to be very serious with ur studies, da alama yau ma yini ku ka yi a nan ko handout baki bude ba" Tace "Bayan ma bani da handout din duk ban san inda suke ba" Yace "A haka za ki yi exams din to?" Ta ɗan tabe baki bata ce komai ba, yace "To nawa ne handout din?" Kallonsa ta kara yi to be sure again, is this really Maheer?? can dai tace "Gaba daya fa kusan 15k ne, kasan handout dinmu akwai tsada" Yace "To tura min account dinki in sa maki kudin" Badiyyah ta kara kallonsa this time around with surprise on her face, Haseenah ce ta fito daga daki tayi wanka ta canza kaya sai baza kamshi take ta karaso parlon tana kallonsu ganin su zaune kujera daya suna kallon juna, Badiyyah tace "To ai ni bani da number ka" yace "Nima bani da taki" Yana fadin haka ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Sa min numberki"
Chapter 97 · 0% Book details