← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 145

Sashe 56

Mayrah Complete Hausa Novel · about 2 min read

ba, kaji har na rantse, ni babu wanda nabi na kai ma wani takarda, a ina nasan su? balle in kai takarda?" Kuka take sosai tana rantse rantse bata san zancen ko wani takarda ba ita, Alhaji Garba yace "To a ina kika samu labarin an daga aure har kika gaya mana?" Cikin kuka tace "Matar yaya Maheer kawata ce ita ta kirani take ce min an daga aurensu ni kuma sannan ina Bichi, kilan kawai bata son in zo bikinta ne, zuciya daya na yarda da abinda tace min ni kuma na gaya maku, amma ni ban kai ma kowa takarda ba, to ma a ina nasan gidajensu? in kuma ana ganin karya nake a kai ni gidajen da suka ce an kai masu sai su fadi ko ni ce na kai masu, kawai don an ga ni marainiya ce bani da kowa sae Allah" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka har da kifa kai a carpet tana shessheka kamar ranta zai fita, Aunty Mariya tsabar mamaki ta kasa rufe baki tana kallon Badiyya, Maheer ji yayi kamar ya tashi ya tattakata a wajen ya rufeta da duka, Ammi kuwa dama bata dago kanta ba, Hajja na matsar kwalla tace "Ni dama ina ta tunanin ta inda za ace Badiyya tasan gidajen mutanen nan da suka ce an kai masu takarda, Badiyyar da kowa yasan babu inda take zuwa daga gidana sai Bichi sai gidan kawarta wato matar Maheer da aka daura aure jiya, don ko gidan nan wllh sai nayi da gaske take zuwa, amma to an bi ance ita ce ta dinga kai ma jama'a takarda...." Kowa dai yayi shiru a parlon, Maheer yayi da ya sanin zaman nan da ake yi da shi, he wish bai shigo ba, kuma banda bai son daga hankalin Ammi babu abinda zae sa yayi shiru a wajen, Aunty Mariya tayi saurin mikewa tace "Lahh na fa daura abu a kitchen Ina zuwa..." daga haka ta samu ta fice daga parlon don kar takaici ya kar ta..... Bata san yanda aka karke ba dai daga karshe sai ga Badiyya ta shigo main parlor Hajja na biye da ita a baya tana gaya mata dakin da su Haseenah suke, Badiyyah sai wani hade rai take tana kumbure kumbure, kuma ko gaida Aunty Mariya bata yi ba ta haura sama, sai a sannan ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tana murmushi ta nufi dakin da su Haseenah suke tana bude kofar ta saki guda....
Chapter 56 · 0% Book details