← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 145

Sashe 119

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayraah ta sunkuyar da kanta saboda hawayen da taji ya kawo idonta, bata taɓa shiga exams hall taji kanta so empty like today ba, ɗaga kai tayi after some minutes ta goge tears dinta, suka hada ido da Dr Musharraf dake kallonta, dauke kanta tayi daga direction din, Badiyyah dai sai kallon Mayraah take tana murmushi kasa kasa ganin sunanta da reg number kawai ta rubuta a booklet, yawanci idan suna exams in dai Dr Musharraf na invigilating zama yake yi colleagues dinsa su yi invigilating din, ko nan da can bai son zuwa, yau kam ya amshi attendance sheet going round to give each and every student to sign, har ya iso roll din da Mayraah take zaune, yana isa gabanta taki yarda ta dago kanta, ya ajiye mata sheet din attendance din kan booklet dinta, ya amshi pen dinta dake hannunta ya ajiye mata nasa, kallon pen din nasa ta dinga yi ba tare da ta yarda ta daga kai ta kallesa ba, can dai ta dau pen din nasa tayi signing attendance din, ya dau attendance sheet din ya bar wajen, lkci daya duk kamshin turarensa ya cika mata hanci, ta wani hade rai ta ajiye pen din nasa kawai kan booklet, dai dai nan wani lecturer dinsu ya karaso inda take ya tsaya yace "Are you not comfortable here?" Ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yes sir" Yace "Ok let me change ur sit" Mikewa tayi ta dau booklet dinta da pen din Dr Musharraf ta bi bayan lecturer din ya kai ta har gaban hall ya nuna mata kujera da table dake kusa da podium ta karasa ta zauna, tana zaunawa ta bude booklet din sai ta samu kanta kuma da fara rubutu, 50 minutes da fara rubutunta ta gama abinda zata iya a questions din, zuwa Lokacin students sun gama sun fara fita class din, sai a sannan ta lura Badiyyah ma ta fita, ta hada ido da Musharraf that is sitting opposite to her, yana amsan booklets din wa enda suka gama, ta rufe booklet dinta ta mike ta tafi zata yi submitting, tana ajiyewa gabansa ya dauka ya bude, ita dai kanta na kasa tana jiran ya bata attendance tayi signout don yana hannnunsa attendance sheet din, after few seconds ya ajiye mata yana kallonta, pen dinsa dake hannunta ta ajiye zata dau nata da ta ga ya ajiye kan table yayi saurin daukewa, daukan nasa din tayi, tayi signing ta fice daga hall din, Hamidah na ganin Mayraah ta fito ta nufeta tana kallonta tace "How was the paper Mayraah?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Alhmdlh" Hamidah tace "Toh Allah ya bamu sa'a" Mayraah tace "Ameen" Hostel Mayraah ta wuce bata kara ko minti daya a department din ba. Mayraah na kwance ita kadai a daki da yamma tana ta tunane tunane, zuwa yanzu tunani har ya zame mata jiki, tayi wannan tayi wancan, wani tayi murmushi, wani kuma taji hawaye ya cika idonta, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo wayar a hankali tana kallon screen din ta ga Maheer ke kiranta, da kamar bazata daga ba don dazu ya kirata bayan ta dawo hostel, can dai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yace "How r u Mimi?" Tace "Alhamdulillah, ina yini" Yace "Bacci kike ko karatu?" Tace "Just lying down...." Yace "Ohk, na bada sako a kawo maki ki fita kofar gida ki amsa" Shiru tayi sai taji da ma tace masa tana school, yace "Hello" a hankali tace "Toh" Daga haka ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta fita waje, tsaye tayi bakin gate din hostel din ganin Abba, bata san sanda ta nufesa ba da farin cikin ganinsa ta gaishesa, ganin yanda ta rame Abba yace "Kina cin abinci kuwa Mayraah?" Maheer dai na tsaye jikin mota shi ma yana kallonta, he is not happy with the way take ramewa kullum, tun shekaranjiya rabonsa da ita sai dai ya kirata a waya, yana bata enough space kamar yanda tace don tayi karatu, Mayraah na murmushi a hankali tace "Ina ci fa Abba" Abba bai gamsu da hakan ba ya kalli Maheer yace "I don't think she is comfortable here Maheer, ta dawo gida kawai" da sauri Mayraah tace "Abba exams ne fa, but ina cin abinci wallahi, karatun da nake yi ne shi yasa" Abba yace "Papers nawa ku ka yi yanzu?" Tace "On monday muka yi daya, muna da wani gobe Thursday in sha Allah" Abba yace "Sai kuma yaushe bayan na gobe?" Mayraah tace "Sai kuma Monday" Abba ya kalli Maheer yace "Idan tayi paper din gobe ta dawo gida for the weekend, bring her back home" Lokaci daya Mayraah taji gabanta ya fadi ita gaba daya bata ma son tuna gidan, da sauri tace "Amma Abba za mu yi practical a laboratory for Monday's paper, friday and Saturday duk za mu shiga school, ka tambayi yaya ya sani ai" Abba yace "Duka courses din nawa ne gaba daya?" Tace "Guda 6 with project" Abba yace "Toh za ku gama da wuri kenan" Mayraah dai ta yi murmushi kawai ta gyada masa kai, duk da dai intervals na 2 days ne for every course, Siyayya sosai Abba yayi mata Maheer ya fito mata da su daga mota ta shiga da su cikin hostel, minti sha biyar kawai Abba yayi suka wuce tare da Maheer, ita kuma ta koma cikin hostel, zaunawa tayi tana kallon handout din da ta ajiye gefen gado, tun jiya ta kasa bude handout tun da taga course din Musharraf za su yi, ba shi ba har course din nasa taji ta tsana har cikin ranta, wanda a da it's among her best... Sai can da daddare bayan tayi isha ta jawo handout din ta ɗan yi scrolling daga karshe kawai ta ajiye tayi kwanciyarta don ranta kara baci yake just scrolling through the handout... Washegari tana zaune hall din exam din nasu da booklet dinta da aka masu sharing suna jiran question paper, kamar ran Monday yau ma Badiyyah a gefenta ta zauna, ita dai ko kallon side dinta bata yi ba, wani lecturer dinsu ne yayi sharing masu question paper din don Musharraf din ma bai shigo ba, ta dinga kallon takardan questions din, tuni Badiyyah aka fara rubutu babu ɓata lokaci ana murmushi irin anyi karatun nan, Mayraah na daga kai after some minutes taga Musharraf zaune hall din, tayi saurin dauke kai ko da mistake bata sake kallon side din da yake ba, bata wani stressing kanta ba a exam din, she just wrote what she can cause bata ma yi karatun ba ai, an hour into the exams ta mike ta tafi inda zata yi submitting booklet dinta, kallonta kawai Musharraf yake ta cikin glasses din idonsa, zata yi signing attendance dake gabansa ya janye, ya amshi booklet din nata ya bude, ita dai taki yarda ta kallesa ta wani hade rai tana tsaye, rufewa yayi ya ajiye mata right in front of her yace "Go back" ta dau booklet dinta ta juya ta koma ta zauna fuskarta a daure, yawanci invigilators din close colleagues din Musharraf ne shi yasa nobody was against his action a lkcn, Mayraah ta rufe booklet din ta hade kanta da table ba tare da ta kara ko fullstop a abinda ta rubuta ba, kusan ita ce karshen fita hall din bayan duk Coursemate dinta har Badiyyah sun fita, ta tafi tayi submitting gun wani lecturer tayi signing out ta fice without looking at Musharraf da ya bi ta da kallo ta cikin glass, ba wanda zai ce ita yake kallo. Sauran exams din haka Mayraah tayi su ba yanda ta saba exams dinta ba, hakan ke kara daga mata hankali, ita yanzu she is not even after any first class kawai ta samu ko da pass ne ta tafi don ita kanta tasan bata abun arziki a exams din nan, komin dadewan da zata yi tana karatu sai ta ji bata iya rikesa a kai kamar da, nan da nan karatun yake bin iska, a haka har suka yi 5 exams, ya rage masu just last paper dinsu da za suyi on Friday, saboda wahalan course din sannan tasan bata da wani score me yawa a test yasa ta dage tayi karatu ba na wasa ba, ana gobe za su rubuta last paper din nasu tana kwance tana replying message din da Maheer yayi mata ta WhatsApp, bayan ta gama replying dinsa wani message ya shigo mata, ta bude message din ganin bata da number a contact dinta, Pdf taga an turo mata guda biyu with her name, ta bude taga complete project dinta ne from chapter 1 to end, daya pdf din kuma taga project Defense slide ne, tana fita daga cikin slide din taga message kamar haka "Print out 3 copies, 1 for ur Supervisor, 2 for ur project co-odinator, to be submitted to ur external supervisor.... submit ur Supervisor's copy on Monday 5:30pm prompt" Mayraah ta fita daga cikin message din ba tare da tayi reply ba ta ajiye wayar, time din da aka sa ne ya tsaya mata, ta sake dauko wayar ta bude message din tana sake kallon time din wai 5:30pm, tabe baki tayi ta jawo handout dinta ta ci gaba da karatun ta. Washegari da safe karfe goma Mayraah na zaune hall bayan an raba masu booklet suna jiran question paper dinsu, kowa ka gani a class din kasan a tsorace yake da last paper din nan, ga malamin ba shi da kirki, don Malamin da ya kirata office yana mata masifa ne kwanaki, a haka har aka masu sharing question paper, Badiyyah na zaune seat din da take zama tun fara exams din, yau ma Hijab ne har kasa a jikinta, Mayraah ta lura duk ranan da take so tayi expo ne take sako Hijab, ranan da bazata yi ba to mayafi take sakawa, 40 minutes da fara exams din Mayraah taga Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, ita dai rubutunta kawai take kafin ta mance abinda ke kanta tunda bata iya rike hadda for long yanzu.... Lokaci daya duk yan ajin suka juya jin wata lecturer dinsu da ta nufi
Chapter 119 · 0% Book details