Sashe 81
Mayrah Complete Hausa Novel · about 4 min read
sallahn magrib taji alamar cikinta zai fara mata ciwo, ta karasa ta bude kofar, mika mata ledan hannunsa yayi yana kallonta yace "Do you need any other thing?" Ta ɗan yi shiru tana kallonsa, sai kuma tace "I need sanitary pad" Yace "Oh.. ok" Juyawa yayi ya bar wajen, Mayraah ta mayar da kofar ta kulle da lock, Haseenah dake tsaye parlor har sannan ta bi Maheer da kallo ganin ya nufi kofa, tana jin sa ya sake fita da mota, ta zauna gefen kujera zuciyarta na tafarfasa tana kokarin calming kanta down, sai kusan 8 Maheer ya dawo gidan, Haseenah na jin shigowarsa gidan tun bai karaso cikin parlor ba ta shige dakinta ta rufe kofa, Maheer yayi knocking dakin Mayraah ta bude, ya mika mata ledan hannunsa yace "Akwai magani a ciki, i don't know ko zai maki naga yanzu baki son allura" Tace "Zai yi, nagode" Yace "Let me get u hot water" Ta gyada masa kai, kitchen ya tafi ya dafa mata ruwan zafin ya zuba a flask ya kawo mata har da cup, ta amsa tana kallonsa tace "Nagode yaya" Yace "Take care of ur self" Ta gyada masa kai, yana barin wajen ta kulle dakinta. Har dare ya tsala Mayraah bata yi wani bacci ba saboda ciwon mara, Maheer na kwance amma gaba daya tunaninsa na kanta cause yasan yanda cramps ke mata, ya kuma san wahalan da take sha, in da gida ne har ayi asuba ya dinga shiga dakinta yana dubata shi da Ammi, but now baya son issue da Haseenah dake gefensa, yana fita dakin nan yasan sai ta bi shi ya zamar masu bacin rai, haka nan ya dinga juye juye all his thinking akan Mayraah, kasa daurewa yayi daga karshe ya mike zaune yana kallon Haseenah dake baccinta hankali kwance, taba ta yayi yace "Dear...." Ta bude ido a hankali, ya kunna closet light din dakin, ta mike zaune tana murza ido tana kallon agogo dake nuni da karfe biyu da rabi tace "Baby lafiya, why are you awake?" Yace "Erm pls, i want you to check on Mayraah bata da lafiya, ni ina fita yanzu zaki iya maida shi issue" Tace "Bata da lafiya? Shi yasa ka kasa bacci? To me ya sameta?" Yace "Ban gane na kasa bacci ba, u have started again ko?" Tace "To nace me ya sameta?" Yace "Ki je ki dubata" Sauka tayi daga kan gadon da shegun kayan baccin jikinta zata fita daga dakin yace "Haka za ki fita?" Juyawa tayi ta kallesa tace "Wajen namiji zan je halan?" Yace "Plss cover ur body before going out Haseenah" ta wani kyabe baki ta dau zani ta daura sannan ta fita dakin.... Mayraah na durkushe a dakin ta daura kanta saman gadon wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta jawo wayar da kyar ta daga ta kai kunne amma bata ce komai ba, daga daya bangaren yace "Kin samu kin sha ruwan zafin?" kai kawai ta gyada masa, yace "Har yanzu kuma baccin bai zo maki ba?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "You are not saying anything ko dai baccin kike ji Baby?" Kamar zata yi kuka tace "Aa" a hankali yace "I wish I can take away the pains for you" Ita dai bata ce komai ba don azaba ya isheta, yace "Ko za ki sake shan maganin" da kyar tace "Na sha sau uku ai" shiru yayi yana jin tausayinta har cikin ransa, cike da karfin hali tace "Ina zuwa" Yace "Aman ne dai?" Tace "Eh" Ajiye wayar tayi ta shiga bandaki da sauri, Haseenah ta gama zagayenta a corridor din dakunan bayan yan mintuna ta koma dakinsu tana kallon Maheer dake zaune, ta kashe closet light din dakin tace "Bacci take yi, kai ma sai ka kwanta kayi bacci" Bata jira me xai ce ba ta shige jikinsa.... Har karfe hudu Dr Musharraf bai yi bacci ba kamar yanda Mayraah bata yi ba, every few minutes xai kirata to check on her, har dai ya kirata around 4:45 yaga bata daga ba, nan ya gane bacci ya dauketa....