Sashe 13
Mayrah Complete Hausa Novel · about 1 min read
ya shige ki" Ammi ta gyada masa kai tace "In sha Allah Maheer" Yace "Ki tashi kije ki kwanta" Tace "Kai me ka sakko yi" Yace "Abinci zan ci" Ammi tace "In ko baka daina cin abincin tsakar dare ba zaka ajiye tumbi ne" Yayi murmushi yana shafa cikinsa yace "Yau ne fa kawai Ammi, kuma kaɗan zan ci, bari ma in zubo ki ga" Daga haka ya mike ya tafi kitchen, ba a dau lokaci ba ya fito rike da plate din abinci, yana ci suna hira da Ammi a parlon, har ya gama, tare suka koma sama ganin ya nufi dakin Usman tace "Can zaka kwanta?" Yace "To tayi hijacking min dakin" yana fadin haka ya shige dakin Usman ya kulle, Ammi ta bude kofar dakin nasa a hankali ta kunna wuta tana kallonta, tana kwance tana bacci, Ammi ta karasa cikin dakin ta lulluba mata bargo a hankali sannan ta juya ta kashe wutan dakin ta fita ta tafi nata dakin.