← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 145

Sashe 61

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 aji tsoron Allah a sauke hakkin marainiya😥 amma fa ba irin maraicin Badiyya ba🙄 [6/19, 12:43 AM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ce ke rusa kukan azaba ga bakinta yayi suntum tana biye da Hajja dake rike da hannunta suka nufi kofa, Mama Ladi ta ajiye kwanon abincin hannunta tace "O'o Hajja ba haka zaki ce ba, yaran nan fa duk daya suke a wajenki, ni wllh abinda yasa hankalina bai tashi ba saboda nasan ba wani can bare bane yayi mata wannan mugun bugu haka, ɗan uwanta ne na jini fa, zuciya ce kawai ta debesa yayi mata wannan aika aikan, kai har ma da sharrin shaidan don ni nasan ba haka yayi niyya ba" A mugun fusace Hajja dake huci tace "Babu abinda ta hada da shi banda uwarsa da take kanwar uwarta, don haka kar ki sake ce masa ɗan uwanta Ladi" Aunty Mariya dai na makale dakin baƙi tana jiyo duk abinda ake a parlon amma taki fitowa, Mama Ladi ta kyabe baki ta jawo kwanonta ta ci gaba da tsotsan ƙashin hannunta tace "To ke yanzu da kika figeta haka a ina za ku samu abun hawa da talatainin daren nan, wannan ai sai mai adaidaita sahun ya tsorata ya zata barauniya ce ta tsere daga hannun jami'an tsaro.... Wai anya ma Badiyya ce wannan ko dai kawai haukanmu muke, ya za ayi daga ɗan duka baki yayi suntum haka kamar leben rakumi?" Mama Ladi na kai wa nan ta tuntsire da dariya har da kwanciya tana kyakyatawa tace "Hajja duka ne fa an riga an nakada mata shi babu yanda muka iya sai dai muce Alhamdulillah, komai Allah yayi dai dai ne, kawai hakuri zaki yi idan Allah ya kai mu gobe da asuban fari sai ki ja ta ku tafi duk inda za ku amma yanzu dai ku rufa mana asiri don kuna fita idan Allah ya sa ku ka hadu da yan sanda cikin daren nan duk bayanin da zaki masu baza su gamsu ba, cewa za su yi sata taje tayi aka mata haka...." Cikin kuka Hajja ta katse ta tace "In kwana su karasa kasheta Ladi? In kwana saboda gidan ubana ne nan din ko kuma gidan ubanta? Ae wllh da dai ni da Badiyya mu kwana gidan nan gwara ko titi ne mun je mun yi shimfida mu kwanta, kuma ba laifin kowa bane laifina ne don dazu da safe da ta bukaci in bata makulli da na bata da duk haka bazai faru da Marainiyar nan ba, sannan da ace nayi tafiyata tun safe naje nayi abinda zai fi min alkhairi a gidana da hakan bai faru da Marainiyar ba, ko dabba baza ayi ma wannan dukan da aka mata ba, ki dubi jikinta fa duk a farfashe, dubi bakinta fa, kafarta kuwa da kyar idan bata yi targade ba, yanzu idan dangin ubanta suka ce sai sun dau mataki akan wannan abinda aka mata ni na isa in hanasu? Ko barawo dai baza ayi ma wannan tsinannen dukan na rashin imani ba balle ita da ba sata tayi ba ba kuma ɗan mutum ta kashe ba kawai tsabar zalunci da zuciyar kafirci yasa aka mata haka, kuma in dai burin mutane ne cin mutuncin maraya su walakantasa to wllh wllh baza su wanye lafiya da duniya ba, sannan ko ma wanene ya mata wnn aika aikan Allah ya isar mata cikin gaggawa, babu yafiya tsakanin ta da koma waye, ni ma kuma ba yafe masa zan yi ba tunda amanata ce ita" Ammi dake tsaye parlon ta kasa cewa komai sai hawaye, gaba daya jikinta yayi sanyi, she is soo speechless, Mama Ladi dai sai fama take da ƙashin hannunta tana lullumshe ido tana kallon Hajja, Hajja ta figi hannun Badiyya dake dingishi tana rusa kuka har sannan, za su fita daga parlon, Ammi tayi karfin halin bin su tace "Don girman Allah Hajja kiyi hakuri ki bari...." A fusace Hajja ta dakatar da ita tace "Ba abinda zaki ce min, inyi hakuri in bari a kasheta ki huta 'ya yanki su huta? kuma kije ki rungumi warce zaki runguma da ta fiye maki Badiyya tun asali dake da yaranki, ai tun ba yanxu ba dama kike nuna baki hada komai da Badiyya ba, ni kadai ce dolen Badiyya a duniyar nan tunda ni na haifi uwarta...." Mama Ladi ta buda baki tace "Kaji wata magana kuma, to wai ita Badiyyar er gwal ce da baza a doketa ba, ni wani irin duka ne ban sha a wajenki ba ina karama duk da bani da uwa bani da uba a lokacin, kin dubi maraicina da kike nakada min duka? yarinya munafuka kawai mara tsoron Allah kiyi ta daure mata kugu, wato dai duk wannan tsiyar da ta tafka so kika yi a zuba mata ido saboda ga ta munafukar Marainiya ko? To wai ma uban waye ba maraya ba a zamanin nan na yanzu, ni iyayen gareni? Bakina fa da nata na bata labarin yanda aka samo Mera da zuciya daya wllh, sae ga labari a duniya an kasa a faranti ana ta yawo da shi, to wani marayan arziki ne zai yi wannan mugun abu? A marayun ma Badiyya er iska ce kawai...." Hajja tace "Ke ma Allah ya isa wannan kazafin da kika mata Ladi, in sha Allahu sai Allah ya saka mata, za kuma ki gani a kwaryar ki" Mama Ladi ta kyabe baki ta koma ta ci gaba da taune ƙashinta tana hararan Badiyya, Hajja tace "Kuma ina ce dai saboda ni kika zo garin nan ko? To ki koma inda kika fito ba a bukatarki, bana son ma kice zaki kara zumunci da 'ya ya na, ni da na zame maki dole kiyi da ni amma ba 'ya yana ba...." Hajja na kai wa nan ta fice daga parlon tana rike da hannun Badiyya, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "To ko dai wiwi Badiyyar ta banka mata ne" Ammi dai ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kan kujera tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Ko ma dai waye yayi mata wannan jibgar Allah yayi masa albarka, kyau ace ma ya cire mata haƙora biyu na sama da na kasa ta dawo kamar mujiya...." Mayraah dai ta gaji da zaman parlon baƙi ga baccin da ta fara ji, she is been sitting for almost an hour now a parlon, ta kalli agogo dake nuna karfe goma da minti arba'in, sannan ta ɗan kalli inda yake kwance, waya yake amma duk da babu wani tazara tsakaninsu bata jin abinda yake cewa, she just notice he is on phone call, a hankali tace "Ina jin bacci Yaya" Ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune ya katse wayar, after few seconds ya tashi, tana ganin haka ta tashi ita ma, ya nufi kofa ta bi bayansa, sai da ta fito parlon ya kashe Ac da wutan parlon sannan ya kulle kofar ya fara sauka porch din building din tana biye da shi, suna shiga main parlor din gidan suka tadda Ammi da Mama Ladi har sannan a parlor, ita dai Aunty Mariya daga karshe dama kwanciyar ta tayi a dakin baƙin ta fara bacci don bata da strength din fara lallashin Ammi, kallo daya yayi masu zai wuce sama fuskarsa a murtuke, Mama Ladi tayi saurin cewa "Yauwa Usuman don Allah nace gobe zaka kai ni gidan Mashir kasan ba dani aka je kai amaryarsa ba, daga shiga makota in fito na tarar wai an tafi kai amarya, kaga Mashir ae bazai ji dadi ba ace ban je ba ko? To ina gudun kar ya kullace ni shi sa gobe da sassafe zaka kai ni gidan" Usman yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya wuce sama, Ammi ta bi sa da wani kallo shi kam yaki kallon ma inda take dama, Mama Ladi tace "Kya wani bi sa da harara, me yayi maki? Ance maki kowa ne baya son gaskiya kamar ke da uwarki?" Mayraah ta juya a hankali ta tafi kitchen don sake dafa ma Ammi shayin da take dafa mata dazu. Ammi na zaune Bedroom dinta da safe, waya ne kare a kunnenta cikin sanyin murya tace "Wallahi ban yi wani baccin kirki ba jiya" Daga daya bangaren Maheer yace "Pls ki kwantar da hankalin ki Ammi, in sha Allah zuwa anjima zan je can gidan nata, ke ba sai kinje ba tunda ranta ya baci haka" Da damuwa Ammi tace "Amma shi Usman bai duba halin da nake ciki ba ya kara dauko min wannan maganar bayan yasan halin Hajja? Me yasa bazai yi considering din condition dina ba?" Maheer yace "To kika san abinda tayi masa, ke dai kawai ki bar zancen, shi da ba shiga harkanta yake ba kika ga yayi mata haka ai kinsan dole da abinda tayi masa" Ammi tace "Ya wuce wannan abinda tayi a kan auren Mayraah? Bayan shi ai ba wani abu da ya hadata da shi na ga, burinsa kawai ya ga ya janyo min magana, shekarun baya haka yarinyar nan ta nuna tana sonsa ita in ba shi ba bazata yi aure ba, amma duk irin lallaba Usman da nayi daga karshe ai kaga abinda yayi mana gaba daya, shi yasa har yanzu Hajja ke kullace da shi ba kuma fita ranta abun yayi ba don har gobe cewa take saboda Usman taki tsayar da miji, sannan kwanaki kiri kiri ya daukota a motarsa ya ki, babu abinda Hajja ta manta bata gaya min a waya ba akan wnn abun da yayi, to yanzu kuma kaga irin dukan da yayi mata, haka kawai ya ja min magana wajen Hajja" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ni dai yanzu duk ki bar zancen nan ki kwantar da hankalinki Ammi, ki samu kiyi breakfast ki sha drugs dinki ki kwanta, in sha Allah anjima za mu yi magana idan na je gidan" A hankali Ammi tace "Naji Mama Ladi na cewa zata je wajen naku yau, to bana son inyi magana ita ma ta juya min zance ne yasa ban ce mata komai ba, amma ai bai kamata daga tarewar yarinya a fara mata sintiri ba" Maheer yace "Ai ba komai don ta zo Ammi, ita da
Chapter 61 · 0% Book details