← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 145

Sashe 140

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

he notice she is shivering, ya dau remote ya kashe AC din office din yana kallonta yace "Mayraah" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, and he saw how pale she look, mikewa yayi da sauri ya dafa goshinta ya hau jero mata tambayoyi without waiting for answer yace "Baki da lafiya ne? Your temperature is so high, have u been sick?" Duk da halin da take ciki ta wani hade rai ta cire hannunsa da sauri a goshinta, ta mike da nufin barin wajen ta ji wani dizziness tuni ya kamata ya zaunar da ita kan kujeran nan da nan hankalinsa ya tashi, still holding on to her yace "Tun yaushe ne baki da lafiya Pls??" Mayraah ta hade kanta da table bata ce komai ba, da sauri ya koma ya bude drawer dinsa ya ciro Blood pressure gauge ya dawo, ya duƙa gabanta ya kamo hannunta, janye hannun tayi nan da nan hawaye ya cika idonta amma ta kasa cewa komai, cike da damuwa yace "Pls ki bari in duba B pressure dinki..." Haka nan ta bari ya dubata, yayi unwrapping din inflating rubber cuff din da sauri ya zauna kujeran da ke kallon wanda take, a bit shocked yace "Subhanallah, ur blood pressure is beyond low, Baby what's wrong with you? Me yake faruwa?" Mayraah dai bata dago kanta ba hawaye ne kawai ke zuba idonta, Mikewa yayi ya dauko mug dinsa ya dauraye ya zuba ruwan zafi ya hada mata coffee drink ya ɗan yi diluting dinsa da bottle water ya dawo gabanta ya dagota yace "Drink this plss dear, it's a first aid, sae mu tafi hospital right away" Hannunta na rawa ta amshi mug din, ganin haka yaki sake mata ya fara bata coffee din da kansa, sae da ta kusa shanyewa ya kyaleta ya ajiye cup din, ya kashe fridge din office din ya sake curtain din windows ya dawo ya dau makullin motarsa amma sae ya tuna ba lallai ta iya tashi da kanta ba, assuming ba department suke ba he will definitely assist her, kawai ya fita office din hoping zai ga wani student mace or even a female Lecturer da zata rike Mayraah zuwa Motarsa, Dr Asma'u ya samu office dinta, ta biyosa har nasa office din bayan ya gaya mata abinda ke faruwa, ta dago Mayraah tana mata sannu suka fito daga office din har zuwa parking space tana rike da ita, back seat ta bude mata tana kallon Musharraf tace "Dr ko zaka jira in rufe office dina mu tafi asibitin tare?" Yace "Toh ba damuwa" Ta koma cikin department din, sannu kawai yake ma Mayraah da ta hade kanta da seat din motar, a haka Dr Asma'u ta dawo ta samesu da jakarta ta shiga back seat din ta dago Mayraah tana mata sannu, Musharraf ya shiga motar suka kama hanyar asibiti. Tun da aka yi ma Mayraah allurai aka sa mata drip take bacci, Dr Asma'u suna isowa asibitin bayan anyi admitting Mayraah dama ta wuce gida, Musharraf na ganin karfe takwas yayi kawai yayi deciding ya kira Maheer cause definitely yasan za a kikkira Mayraah a waya kuma jakar na office dinsa, he was even surprise da ya ga har a sannan Maheer bai kirasa ba tun da zuwa yanzu dai yasan dole za a san bata koma gida ba, Maheer na daga kiran bayan sun gaisa, Musharraf yace "Mayraah ce bata da lafiya anyi admitting dinta hospital since around 6:30...." Maheer yayi shiru, sai kuma a hankali yace "Subhanallah, bana gari but zan tura maka number Abbanmu right away, nima ban jima da kunna wayar ba kilan Abban ya neme ni bai sameni ba, let me send u his contact now" Musharraf yace "To ina jira" Babu bata lokaci Maheer ya tura masa number Abba, Musharraf yayi dialing bayan Abba yayi picking, ya gaishesa sannan yayi introducing din kansa tare da sanar masa dalilin kiran duk a lokaci daya, Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tun 6 ake kiran layinta no response...." Musharraf yace "Eh i think jakar nata na makaranta" Abba yace "Wani Asibitin ne?" Musharraf ya sanar masa, Abba yace "Gani nan zuwa yanzu, thank you" Daga haka ya katse wayar. Hajiya Amina ta fito daga dakinta sanye da hijab bayan Abba ya sanar mata Mayraah na hospital, sai ga Mama Ladi ta taho daga bangaren Ammi rike da kwanon abincin da ta ci zata kai kitchen, Hajiya Amina tace "Mama wai malamin makarantar su ya kira tana asibiti an kwantar da ita, yanzu Abban nasu ya kirani yake gaya min" Mama Ladi ta saki salati tace "Mun shiga uku, asibiti kuma, me ya sameta? to ke yanzu ina za ki da hijabi?" Hajiya Amina tace "Asibitin za mu tafi, yana waje yana jirana" da sauri Mama Ladi tace "Jirani in dauko gyale mu tafi tare kawai, ai hankalina bazai kwanta ba idan ban bi ku ba" Hajiya Amina tace "Toh zan jira ki a kasa Mama" Da sauri Mama Ladi ta koma bangaren Ammi, Ammi na zaune kan darduma a parlon, Mama Ladi ta ajiye mata kwanon hannunta ta figi mayafinta tace "To ga Mayraah can bata san inda kanta yake ba a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, yanzun nan aka kira daga asibitin aka sanar za mu tafi da su Mamuda" Ammi ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi da har ta fice daga Parlon da gudu da mayafinta. Ko da suka isa asibitin har a sannan Mayraah bacci take, Musharraf ya mike daga kan plastic chair da yake zaune yana ma Abba sannu da zuwa da ladabi, kallo daya Abba yayi masa ya amsa ya karasa gadon ward din yana kallon Mayraah, Musharraf ya gaida Mama Ladi da Hajiya Amina da ladabi, Hajiya Amina ce kawai ta amsa, Mama Ladi ta dafe kirji cikin rawan murya tace "To me ya sameta ni Ladiyo? Ko dai hatsari tayi? Don lafiya ta fita gida" Abba ya kalli Musharraf yace "I want to see the Dr" Musharraf yace "Toh yana office Abba" Abba ya bi bayansa suka fita zuwa office din likitan. Har karfe sha dayan dare Mayraah bata farka ba, Hajiya Amina ta koma gida ta kawo mata blanket da kayan shayi da flask ta dawo, babu yanda Abba bai yi da Mama Ladi kan a maida ta gida sai Hajiya Amina ta kwana da Mayraah ba amma taki, Hajiya Amina na kallon Abba tace "To kawai ka tafi bar Alhaji" Da sauri Mama Ladi tace "Aa, bi shi ku tafi, ni kadai raina na isa in dubata, abinda duk 'ya yan mijina da jikoki haka na dinga wahala da su in aka kwantar da su a asibiti gashi gantalallun ko bin ta kaina basa yi yanzu, ai in da sabo ni dai na saba da jinyan jama'a a asibiti, kawai ku tafi kuyi baccinku ni ina nan" Babu yanda suka iya haka nan suka tafi gida leaving Musharraf behind duk da Abba yace masa ya tafi gida shi ma it's already late, Mama Ladi na kallon Musharraf bayan tafiyarsu Abba tace "To kai kuma bawan Allah ai mun gode kuma haka, ka kama hanya kayi tafiyarka Allah ya saka da Alkhairi, ko da wani abun da kake so a baka ne da ka kasa ka tsare ka ki tafiya?" Musharraf dake kallonta yayi mata sallama ya juya ya fita daga ward din, tace "Haba, kai ba saninka aka yi ba ba komai ba, daga kawo yarinya asibiti kawai sai ka makale cikin mu kaki tafiya, in ma wani abu kake so a baka ai da tun wuri kayi ma Mamudan magana ko er dubu biyar ce ya sallameka da shi" reception Musharraf ya koma ya zauna don bai jin zai iya tafiya gida, tun da Musharraf ya fita daga dakin Mama Ladi ta dau bargon da Hajiya Amina ta kawo ma Mayraah sabo fil da shi a leda ta fiddo shi ta warware ta shimfida kasa ta kwanta, ko minti biyu bata yi da kwanciya ba ta cika dakin da minsharinta. Wajen karfe sha biyu da rabi Mayraah ta farka, sosai kanta yayi mata nauyi ta kasa bude idonta gaba daya, ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, amma ta kasa sunkuyawa ta ga wanda ke minshari a kasa tsabar ciwon kai, a hankali aka bude kofar dakin Musharraf ya tsaya bakin kofar yana kallon Mama Ladi dake ta baccinta kamar a dakinta take, ya karaso cikin ward din bayan ya kulle kofar a hankali, ya nufi gadon yana kallon Mayraah da damuwa yace "Baby kin tashi? How are you feeling now?" Ta kasa cewa komai, bude flask yayi ya fara hada mata shayi me kauri sannan ya mika mata yace "Zaki iya rikewa?" Ta amshi shayin ya zauna plastic chair dake kusa da wajen yana kallonta, a hankali ta dinga shan shayin, ta sha me ɗan yawa ta mayar masa da sauran ya ajiye, ya dau magungunan da Dr din ya bari a dakin da za a bata idan ta farka, ya budesu ya bata ta amsa ta sha da bottle water, ganin tana disconnecting drip din daga hannunta yace "Me yasa kike cirewa?" Cike da karfin hali tace "Zan yi sallah" Yace "Ohk" Tashi yayi ya cire mata da kansa, sannan ya kamo hannunta ta sauka daga kan gadon a hankali, duk wannan abun Mama Ladi na ta buga minsharinta kamar kato na bacci, Mayraah na idar da sallah Musharraf ya maida mata ruwan, yana kallonta yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah, i am sorry for everything" Ita dai bata ce masa komai ba, a hankali yace "You know i love u so much" Komawa tayi ta kwanta ta kulle idonta, bai kuma ce mata komai ba sai kallonta yake, har yaga alamar ta koma bacci. Musharraf bai bar dakin ba sai da aka kira sallan Asuba, kuma har sannan Mama Ladi bata farka ba, ya kamo hannun Mayraah dake bacci yayi pecking dinsa sannan ya fita daga ward din ya kulle kofar. Washegari da safe karfe bakwai Mama Ladi na zaune kan Bargon da ta kwana ta hada shayinta cikin Cup, Mayraah dai na kwance idonta rufe duk da ba bacci take ba, Bude kofar ward din aka
Chapter 140 · 0% Book details