Sashe 8
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi ta bude kofar dakin Maheer ta shiga da sallama, ya amsa yace "Baki kwanta ba Ammi?" Ammi tace "Ban kwanta ba" Karasowa tayi ta zauna kan kujera dake dakin tana kallonsa tace "Ka sake komawa gidan Hajja kuwa? Ina son sanin yanda ake ciki ne" Yace "Ko dazu naje har yanzu dai bata dawo daga Bichi da ta tafi ba" Ammi tayi shiru, can tace "Ya kake ganin za a bullo ma lamarin nan Maheer, ni duk kaina ya daure wllh" Da mamaki Maheer ya kalleta yace "Kamar ya kenan Ammi? Wai me yasa ake biye Badiyya ne..." Ammi ta katse sa tace "Marainiya ce Maheer, er kanwata ce duk yanda ku ke tunanin zan maku ita ma haka zan mata, wallahi abun ya tsaya min a rai, sannan bazan fifita Mayraah a kanta ba" Maheer yace "Don Allah Ammi ki bar wannan zancen, it's not even making sense sai kace wani wasan kwaikwayo, this is reality, abinda zai yiwu shi ake yi, ba ita wannan mutumin yace yana so ba, to don me za mu mayar da kanmu kananun mutane, don Allah ki bar issue din nan yayi sliding haka, ni wllh idan ta kuskura mu ka yi ido hudu da ita Allah sai na mata dukan tsiya tunda bata da kai" Ammi tace "Aa kar ka taɓa ta, tunda ku baku san meye maraici ba...." Maheer yayi saurin kauda zancen don ɓata masa rai ma yake, yace "Ammi gobe Haseenah zata zo gaisheki in sha Allah" Ammi tace "Toh, Allah ya kai mu lafiya" Yace "Ameen, and Mayraah ta sameni jiya da wata magana wai ita bazata iya gaya maki ba" Ammi ta maida attention dinta gaba daya kansa tace "Wace magana kenan?" Maheer yace "Gobe Saturday za su fita siyayyan lefe shine bazata iya gaya maki ba" Ammi tayi shiru tana kallon Maheer, bai bata daman cewa komai ba ya ci gaba "Kinsan ai yanzu haka ake yi, nima ba gashi tare mu ke hada kayan da Haseenah ba, so ba wani abu bane wannan" a hankali Ammi tace "To ai ban san ko Abbanku zai yarda ba" Maheer yace "Ni zan gaya masa da kaina, yanzu modern era mu ke, komai kuma tafiya yake da zamani" Ammi dai sai kallonsa take, yace "Kuma bikin na gabatowa zai kai ta ta gaida mahaifiyarsa, ni ba gashi zan kawo Haseenah gobe ta gaisheki ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "To dai duk ku gaya ma Abbanku ni ba ruwana" Murmushi yayi yace "Zan kirasa gobe da safe in sha Allah, naji yace next week zai dawo ko" Ammi tace "Haka yace" Mikewa tayi tace "Zan je in kwanta" Maheer yace "Allah ya tashe mu lafiya Ammi" Ta juya ta fita daga dakin ta kulle masa kofa. Washegari da ya kasance friday Mayraah bata je makaranta ba duk don tayi assisting Sabeera su yi girke girken da za a tarbi Haseenah, Fried rice ta yi da pepper chicken sai zobo drink da small chops, ganin da sauran time tayi cupcakes, babu abinda ke kara sa yayyinta maza ji da ita sai saboda iya girkinta, Mayraah is so perfect in making any sort of food, iya girki na daya daga cikin baiwarta, banda yanzu da ta shiga final year bata da time din kanta da kusan kullum ita ke ma Maheer girki, haka ma Umar dake bribing dinta tayi masa in dai yana gari, Usman ne kadai ko a jikinsa in an basa ya ci idan ba a basa ba ko kallo abincin bai ishesa ba, dama kuma ba wai suna wani shiri bane can da shi, Maheer ne favourite dinta sae Umar idan ya dawo, Wajen karfe sha biyu Ammi ta shigo kitchen din tace "Su Mayraah abun nema ya samu, wannan duk na Antyn taki ce haka" Mayraah tayi dariya tace "Abinci kala daya fa kawai muka yi Ammi" Ammi tace "To sannunku da aiki" Daga haka ta bar kitchen din. Bayan sallan juma'a Maheer ya iso gidan tare da Haseenah, tun suna hanya yayi ma Mayraah text yace sun taho, tana jin shigowar motarsa compound ta dau gyalenta ta fito ta tsaya balcony, shi ya fara sauka a motar sannan Haseenah ta sauko, sanye take da tsadadden atamfa an mata riga da skirt, sai mayafi medium size da ta yafa hannunta rike da jakarta, tayi ma fuskarta very light make up, tun daga nisa Mayraah ke hango gold din fingers dinta wa enda ke ta daukan ido, tayi kyau sosai ba karya, Mayraah ta sauka balcony din ta karasa har gun motar da fara'a tace "Sannu da zuwa Aunty" Maheer dai yayi gaba zuwa cikin gidan, ba tare da Haseenah ta kalleta ba tana taunar gum tace "Yauwa" Daga haka ta bar ta wajen tsaye ta bi bayan Maheer, Mayraah ta bi ta da kallo irin na mamaki, can dai ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Mayraah na shiga parlor ta tarar har Haseenah ta zauna shi kuma Maheer ya haura sama, hada ido suka yi Mayraah ta dauke kai ta wuce sama ta tafi dakinta tayi kwanciyarta, bayan kusan minti ashirin aka bude kofar dakinta, ta yi saurin kulle ido don har taji kamshin turarensa, ya kulle kofar yana kallonta yace "Mimi" Ta bude ido da kyar kamar irin baccin nan take, yace "Why did u come upstairs?" Ta mike zaune tana murza ido cike da shagwaba tace "Yaya kaina ciwo yake tun safe kasan nake ta aiki fa, kuma da na shigo ban san sanda ma bacci ya daukeni ba" Yace "Ohk ki fito ku yi sallama i am taking her back home now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya my head is so heavy, i am not feeling fine" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta, ba a dau lokaci ba ta sake jin an bude kofa ta juya, ya shigo cikin dakin ya ajiye mata paracetamol a bedside drawer da bottle water yace "Ki tashi ki sha, sai na dawo" Daga haka ya fita daga dakin. Maheer na ajiye Haseenah a gidansu tana shiga compound tayi dialing number Badiyya, Badiyya na dagawa Haseenah na buga kirji tace "Badiyya, ni wannan cousin din taki zata walakanta yau?? Ni zata ma kallon banza tayi wucewarta kamar ta ga kashi saboda naje gidansu?" Badiyya tace "Oh kin je gidan kenan yau?" Rai bace Haseenah tace "Wallahi wallahi da nasan abinda Maheer zai kai ni gidansu kanwarsa ta min kenan da ban je ba, babu abinda zai fara kai ni gidan komin tashin hankalin da za mu yi da shi, ita kanta uwar tasa kamar bata yi wani farin ciki da zuwana ba don ko minti biyar bata yi ba a parlon bayan mun gaisa tayi wucewarta sama aka bar ni daga ni sai TV da abinci a gabana kamar abinda ya kawo ni kenan" Badiyya tace "Atoh, shi yasa nace kice masa ba yanzu za ki je ba, kyau ace ina gidan kika zo" A fusace Haseenah tace "I feel so humiliated Badiyya, yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta zata min wannan walakancin? Me aka yi aka yi ta?" Badiyya tace "Yanzu dai ki bari za mu yi waya jirana ake, nima ai yau zan koma gidan Hajja, Mayraah kuwa ko da ni Badiyyah ban auri Dr Musharraf ba ba fata nake ma kaina ba, to wllh sai dai taga wata can daban ta auresa amma ba ita ba, balle in sha Allahu ni ce matarsa, in Allah ya yarda.. " Haseenah tace "Ai wllh in har kika bari ta auri lecturer din nan ni na ma raina ajinki da capacity dinki, baki cika Badiyyan da duk muka sani ba in har hakan ta faru" Badiyya tayi murmushi tace "Ke dai za mu yi waya" Daga haka ta katse wayar. Ranan asabar kamar yanda Mayraah tayi ma Hajja alkawari karfe goma ta gama shirinta ta sauko downstairs don Ammi na parlor tare da Usman, Mayraah ta rakube jikin kujera tana kallon Ammi tace "Ammi na shirya" duk tunanin Ammi siyayyan za su je yi, ta kalli agogo tace "Ya zo ne?" Mayraah tayi jim tana tunanin yaushe tace ma Ammi Musharraf zai zo, can tace "Ammi ni fa gidan Hajja zan je" shiru Ammi tayi tana kallonta kafin tace "Ba naji ance za ku je siyayya ba, kuma me za ki je yi gidan Hajja" Mayraah ta ɗan ɓata rai kamar zata yi kuka tace "Ammi na mata alkawari zan je yau fa, kuma ma ai ba yanzu za mu yi siyayyan ba sai da yamma" Ammi tace "Aa ki hakura da zuwa gidan Hajja, ki bari ranan da baki da lectures sai mu je tare" Usman dake kallon Tv ya kalli Ammi yace "Saboda me?" Ammi tace "In zan je sai mu je tare kawai" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba amma abinda Ammi tace bai mata dadi ba, Usman yace "Ni ma ai can zan je yanzu, ki bari in ajiyeta sai mu dawo tare idan zan dawo tunda ni ba dadewa zan yi ba, i will be going to Zaria later" Ammi ta kalli Mayraah don har cikin ranta taji wani iri ɓata ran da tayi, Ammi tayi kasa da murya tace "To ku je tare, amma ki tabbatar kin biyosa idan zai dawo" a hankali Mayraah tace "To Ammi, Nagode" Kallon Usman Mayraah tayi tace "Yaya yanzu zaka tafi?" Usman ya kalleta yace "What is ur business?" Nan da nan Ammi ta hade rai tana kallonsa tace "Kai komai masifa bawan Allah" Mikewa Mayraah tayi ta tafi kan kujera ta zauna bata sake cewa komai ba, Ammi tace "To meye laifi ma don ta tambayeka banda fitinarka tayi yawa" Ya mike yace "To idan bata da lectures din sai ku je tare, sai na dawo" Mayraah ta zaro ido da sauri ta mike tace "Yaya don Allah kayi hakuri" tuni ya fice daga parlon, Ammi ta tabe baki tace "Bi sa ku tafi" Mayraah ta bi bayansa da sauri.... Tafiyar minti talatin suka yi suka iso gidan Hajja, tsabar ba dadewa zai yi ba a waje yayi parking motarsa suka gaisa da mai gadin gidan ya shiga ciki Mayraah na biye da shi, parlon Hajja cike yake