← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 145

Sashe 17

Mayrah Complete Hausa Novel · about 6 min read

iyayen ya gada, kinga kuwa ae ba banza bishiyar take ba, tun fa asuba nake aikin share wajen nan sae yanzu na gama, ai kinga an cuceni an ci amanata, sai cikin dare ko wani mahaluki ya tafi ya kwanta ya bai ma hakarkarinsa hakkinsu sai shaidanun yaran su hada daba karkashin bishiyata suna shan rake suna cin gyada, kuma in sha Allahu ƙara zan sa a zagaye min bishiyar da shi, sai in ga ta inda 'ya yan banza za su zauna karkashin bishiyar" Matar dake tsaye tana sosa kanta tana sauraron Mama Ladi tace "Ai ko kawai yanda kika ce ya kamata ayi, abi duk a zagaye wajen kawai da kara, sai dai fa wannan zai ci damin ƙara ba kadan ba tunda bishiyar tsamiyar kin ga ai tana da girma, kina yin haka kuwa kin yi maganinsu, kin ma huta da masu bi maki kofar gida kullum" Machine ne ya tsaya kofar gidan aka sauko rike da akwati, Mama Ladi tayi shiru tayi mitsi mitsi da ido tana kallon warce ta sauko daga saman machine din, can dai tace "Wacece wannan?" Warce ta sakko bata ko kalleta ba ta ja akwatin zuwa cikin er tsakar gidan, Matar dake tsaye tare da Mama Ladi ta washe rubabbun hakoranta tace "Baƙi aka yi daga birni kenan Baaba Ladi" Mama Ladi ta kalleta tace "Ke dai tseguminki yawa ne da shi Delu, nan kika gama bani shawaran banza wai in zagaye bishiya da ƙara kamar don ni kadai aka halitto bishiyar, to ai mugun halina bai kai haka ba da zan ki bari a zauna a sha iska in samu lada a karkashin bishiyata, kawai mata kiyi ta yawo kina doyi kina shiga hakkin jama'a, ke baki jin warin jikinki ne baiwar Allah, ke wari mijinki wari, aa to Allah ya mana tsari... Tafi ki ban waje munafuka" da sauri Delu ta yi gaba, Mama Ladi ta shige gidanta, haɓa ta rike tace "Wa ya maki kwatancen nan Badiyya?" Badiyya da har ta tube kaya ta watsar kasa tace "Nan din ne bazan gane ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Ai ko gaki nan kin kawo kanki tubarkallah, naga baki taɓa zuwa ke kadai bane sai da Hajja kuma kuna zuwa baki wuce awa daya kike wucewa ki bar Hajja tunda ita har sati tana iya yi a kauyen nan, ke sae kice baxa ki iya ba" Badiyya tace "Yanzu dai wanka nake so inyi, wannan garin naku zafi kamar oven...." Mama Ladi tace "To Hegen almajirin me debo min ruwan a rafi bai zo ba, amma akwai ruwan da na adana bari in kai maki kiyi wankan" Daga haka ta fita daga bukkar, Badiyya ta bi ta da kallo, katon drum da ta sa ma kwado ta bude ta dau bokiti ta cika da ruwa tace "Banda ke ma wa ya isa yasa in bude wannan ajiyar tawa, ruwan nan yafi wata shidda komin rashin ruwan da nake bana taɓa sa, sai dae rashin ruwan ya kasheni babu ruwana, nasan wataran zai min amfani, to yau ga amfaninsa" Badiyya ta fito da sosonta da Sabulu ta wuce ɗan karamin bandakin dake tsakar gidan bayan Mama Ladi ta kai mata ruwan, Mama Ladi tace "Allahu Akbar, wllh sak marigayiya, bana mantawa haka take zuwa ta min sati a garin nan tun ma bata yi aure ba, ita kadai ce bata kyamatar inda nake sae er uwata Hajja kaka, Allah dai ya ji ƙan Rukayyah, shi yasa komi na samu er ta Badiyya nake ajiye ma idan na samu me shiga kano in basa amana ya kai mata" Badiyya na fitowa daga wanka ta tarar Mama Ladi ta ajiye mata kunu da kosai, ta ɗan yi shafe shafenta sannan ta fara cin abinci don karfe biyu na rana ake nema, Mama Ladi har da shimfida mata sabon zanin gado a kan gadon karfenta, Mama Ladi ta dawo ta zauna gefenta tace "Ban ji kince er uwata Hajja tace ki gaisheni ba" Badiyya ta fashe da kuka kamar jira take, a gigice Mama Ladi ta saki kara tace "Wayyo Allahna, mutuwa Hajjan tayi? Na shiga uku na lalace, ta mutu ne?" Cikin kuka Badiyyah tace "Tana nan Mama Ladi ba abinda ya sameta, kawai dama na zo in gaya maki abinda ake min ne saboda an ga bani da kowa, anga Abbana da Ummata basu da rai" ta kare maganar tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Subhanallahi me ake maki Badiyya, su fa mutane har yanzu basu gane rikon maraya akwai tsarkakkiya ba shi yasa da yawan jama'a wuta za su, wa yace masu ana ma marainiya haka? Yanzu basu san ta dalilinki duk sai su shiga wuta ba" Nan Badiyya ta gyara zama ta labarta ma Mama Ladi duk abinda ke faruwa, na karya da na gaskiya, wanda na karyar ma yafi yawa, Mama Ladi tayi shiru tana kallonta baki bude, can ta gyada kai a hankali tace "Tabbas Hajja ta kirani ta sanar min da wannan biki har nace idan Allah ya nufa in zo to zan zo, don gaskiya naci alwashin sai bikinki zan je garin kano don kece tawa, Ita kanta Ammin ta kirani ta sanar min da batun bikin na mata Allah ya sanya alkhairi kawai, ko ba komai hakan ma zan samu lada, to da naji har da na Mashir ne ma yasa na canza shawaran zanje bikin don Mashir nawa ne, ashe kwace suka maki suka makala ma ita meran, ikon Allah, mutane sun zama abinda suka zama a harkan rashin tsoron Allah... Amma Ammi ta bani mamaki ainun, wllh ta ban mamaki, ita Hajja dama bazan kullaceta ba tunda nasan Ammin ce ke juyata yanda ta so, Hajja bata jin maganar kowa sai ita ko don tana kulla mata shinkafa a leda ta kai mata ne oho, amma banda haka ko ita da bazata amince da wannan abu da aka maki ba, me aka yi akayi Mera kuma Allah na tuba? Ana nufin Mera ta fi ki matsayi wajen Ammi ko Hajja kenan? To ko dai cutar mantuwa ce ta kama su, kina er kanwarta uwa daya uba daya a maki haka akan Mera?" Badiyya dake ta kallon Mama Ladi tace "Ko dai baki gane wacce Mayraahn nake nufi ba?" Mama Ladi tace "Ni ko na gane warce kike nufi, ko ba er wajen Ammi ba? Ko ba wannan tsigalalliyar fara doguwa da hanci zarere kamar biro" Badiyya ta hade rai tace "Ita mana... Ita ce ta kwace saurayina za a masu aure yanzu haka saura wata daya" Murmushi Mama Ladi tayi ta rike haɓa tace "Ikon Allah, dama ance in da ranka zaka ga abubuwa iri iri, to gashi ko na ga wannan"
Chapter 17 · 0% Book details