Sashe 73
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ki sauke hakki kiyi karatu hankalinki kwance..... [6/22, 11:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mikewa Usman yayi da sauri yana kallon Abba cike da mamaki, tsabar yanda maganar Abba ya zo masa a ba zata kasa cewa komai yayi, can dai yayi gathering courage yace "In auri Mayraah fa kace Abba? Did you mean it? How? Mayraah da muka taso nake ma kallon kanwata Muharramata how zan aureta as wife? This sounds more like an abomination to my ears, it's weird, ta yaya zan auri kanwata da nake ma kallon uwarmu daya ubanmu daya kawai don abun nan ya faru? No pls tell me ta yaya Abba?" Komawa yayi ya zauna ya ciro handkerchief yana share zufan da ya keto masa a forehead, he looks so confuse, yana girgiza kai yace "No Abba, this isn't going to work, Mayraah kanwata ce har yau, har gobe, har abada, bayan wannan babu wani kallo da zan sake mata, kanwata ce ita ta jini...." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "It's okay Usman, i understand you, but we all neva bargained for this, kawai abinda yasa na kawo shawaran nan naga abinda muke boyewa for many years an tonosa ta hanyar da bamu taba zato ba bamu yi tsammani ba, sannan duk wanda zai zo neman auren Mayraah ina da tabbacin tun daga waje za a tsegunta masa asalin wacece ita, my wish yanzu a rayuwa bai wuce ace Mayraah ta wuce gori ba, i want her to live like every other person, kuma nasan ku da na haifa kadai ne baza ku goranta mata asali ba, baza kuma ku kyamace ta ba, za ku riketa ne da amana ko da raina ko babu raina" Abba ya girgiza kai yace "I don't think there is any means da za ace za'a fara neman iyayenta or anything of such a yanzu because it's of no use, ko daga yanda aka yi dumping dinta a wajen nan a ranan ya nuna ba a bukatarta ne kawai, ba a kuma ajiyeta a wajen da niyyar ta rayu har wani ya dauketa ba, a'a an ajiyeta ne kawai ta mutu, ba kuma a jikin masallaci kamar yanda ku ka ji ana cewa aka ajiyeta ba, i don't know who created that rumors, kawai nasan that faithful day na fito kamar yanda na saba zan zuba ruwa a randunan masallaci kafin jama'a su fara fitowa sallahn asubahi, daga inda ake debo ruwan a wani rijiya ne, sai dai babu wani tazara tsakanin inda rijiyar yake da masallacin, a nan gaba da rijiyan aka nannadeta cikin zani har fuskantar sannan aka saka ta cikin kwali kuma aka rufe kwalin da plank ta yanda iskan kirki ma bazai shiga ba, kaga wanda ake son ya rayu ai baza ayi masa haka ba, kuma me imani bazai taɓa yi ma ɗan da ya haifa haka ba, kai koma ba ɗan da ya haifa ba bazai bari ayi ma wani haka ba, tabbacin koma wacece ta ajiyeta bata da imani, bata tsoron Allah sannan azzaluma ce don da niyyar kasheta tayi hakan, ina jan ruwa a rijiyar nan ina jin kamar kukan jariri amma na rasa a ina gashi kukan babu sauti sosai can kasa kasa ake jin kukan, kawai na bayar ko mage ce ke wannan kukan, har sai da nayi sahu uku da ruwan na kasa hakuri na fara duba wajen da torchlight ina neman inda wannan sautin kukan ke fitowa, in takaice maka nafi minti 10 ina dube duben area din daga karshe na lura da kwalin da aka ajiye nesa da rijiyar kusa da wani kwata na karasa na daga plank din, sai ga sautin kukanta sosai, i was shocked don dai anyi wrapping har fuskarta da zani, na kasa taɓa ta gashi babu kowa, duk ana ciki yawanci ba a tashi bacci ba don karfe hudu da rabi ma bai karasa ba a lokacin, tsabar yanda na zama confuse kawai na koma gida gun Amminku, ita ma tana bacci na tasheta nan na sanar mata abinda na gani bakin rijiya, babu bata lokaci ta sako hijab ta biyoni muka dawo wajen, har sannan kuma jaririyar bata daina kuka ba, Ammi bata yi wani tunani ba kawai ta cirota daga kwalin cikin tashin hankali ta warware zanin da aka yi wrapping dinta da shi, a lokacin sai Amminku ta fashe da kuka tana salati, don yanayin da jaririyar ya nuna ba a ma jima da haihuwarta ba tunda ko goge jikinta ba ayi ba, Ammi bata bi ta kaina ba tayi cikin gida da jaririyar nan a hannunta, Ni dai tsabar yanda mamaki da takaici ya isheni jikina yayi sanyi na koma bakin masallaci na zauna ina tunanin wacce azzalumar ce zata aikata wannan abun comfortably babu tsoron Allah a ranta, sannan duniya na kwance lkcn duk bamu san a haifi jariri a yasar shi ba, wannan yasa abun ya tsaya min, ya kuma tsaya ma mutane da yawa a rai, don kafin gari ya waye labari ya karade unguwa har ma da makota an tsinci jaririya a bakin masallaci kamar yanda ake cewa, da Ammi ta gyara yarinyar ta mata wanka sai da nayi kwalla, ita dama tun da ta dauko yarinyar take kuka, fara ce kal jaririyar, she was a cute baby kamar balarabiya, nan dai aka kai ta gun manyan anguwa aka fara shawaran yanda za ayi da ita, kowa dae na tsoron yace zai riketa don ba a san dalilin yasar da ita a walakance ba a bakin kwata, wasu suka bada shawaran a kai ta gidan marayu, a sannan ma gidan Marayun bai yi yawa ba kamar yanzu ina jin ma babu a garin sai anje wani gari, aka dai yarda akaita can gidan Marayun a harhada kudin mota, duk fa ba wai mun san yanda process din yake bane a lokacin sannan bamu sako yan sanda a ciki ba, nan na shigo gida na sanar ma Amminku shawaran da aka yanke akan jaririyar nan, Ammi ta sakar min kuka ta fara hadani da Allah ita dai a bar mata yarinyar zata rike, tunda a sannan Umar was almost 5 years kuma shi kadai ne a gabanmu, after much pleading and begging, har ta hadani da Hajja, Hajja ma ta saka baki a maganar babu yanda na iya ba don raina ya so ba manyan anguwa suka damka ma Ammi jaririyar nan, a ranan kuma tace min ita dai ta saka mata suna MAYRAAH, as at then we were leaving from hand to mouth, nayi ta kokarin nuna ma Ammi baza mu iya da dawainiyar jaririyan ba muma muna fama da kanmu a garin, gashi Ammi ta jima da yaye Umar babu ruwan Maman da zata ba yarinyar which means dole madara za a dinga siya mata kenan, a hakan ma yan anguwa sun harhada tsofaffin kayan yaransu an kawo ma jaririyan, har kudi aka hada da bai taka kara ya karya ba aka bamu, da shi muka fara siya mata madara, ni dai duk hankalina bai nutsu da rikon yarinyar ba kawai ina jin kunya Hajja ne, a ranan na fita naje kasuwa inda nake dako a biyani kafin in harhada yan kudadena in siya kaya marasu tsada in shiga Cameroon in siyar sai inyi wata daya ban gama hada kudin siyan kayan ba wani lkcn duk abinda na samu ma dole da shi za a ci abinci, that same day da muka tsinci Mayraah ina kasuwa from no where sai ga wani bawan Allah ya bani dubu goma daga kai masa kaya mota, imagine 10 thousand 22 years ago, ai kaga ba karamin kudi bane, nayi ta farin ciki na koma gida duk da ko minti talatin banyi da fitowa ba, a washegari sai ga wata dubu uku daga wata Hajiya ita ma na dau mata kaya zuwa mota, let me make this brief, tun daga sannan ba ayi ranan da zan fita ba a min kyauta ba, me yawa, ɗan kadan a haka dai kullum, nan na dinga saran kaya ina shiga Cameroon a kwana biyu uku kaya suke karewa tas ga riba wanda a baya sai inyi sati uku a Cameroon kaya basu kare ba, tun daga samun Mayraah hanyoyin arziki suka dinga bude mana ta ko ina, ta yanda bamu taɓa tunani ba a rayuwarmu, in less than few months ni kaina na tsorata da abinda na tara, nayi ta jin tsoro, haka ma Amminku wanda nasan da bata san halina ba tunani zata yi sata na fara, amma abu sai kara ci gaba yake, harkoki na ta bunkasa kan kace me kafin wata 12 muka tattaro muka dawo kano, kaga kuwa samun Mayraah alkhairi ne a garemu, kuma ko da muka dawo Kano barka kawai ake shigowa yi ma Ammi tunda shekaranmu daya a can muka samu Mayraah, tana wata sha biyu kuma muka dawo Kano, don haka babu wanda ya kawo cewar ba er mu bace Mayraah, ku kanku where very happy bayan dawowarmu don an sanar maku Amminku ta haihu tun bamu dawo ba.... Usman ya ɗaga kai yana kallon Abba jin yayi shiru, Abba ya nisa yace "Ko da wasa mu ma bamu taba zaton akwai randa za mu yi ma 'ya yan da muka haifa tayin auren Mayraah ba don duk daya muka dauke ku gaba daya babu banbanci, amma muna namu Allah kuma na nasa...." A hankali Usman yace "Yanzun ma hakan baxai faru ba Abba, we will continue being the brothers we are to her, for better for worst we will protect her and will always be there for her, babu wanda zai taɓa ta ya kwana lafiya, ko da yau ta samu wani da zai aureta kallon banza idan ya hadasa da ita balle har ya kai ga goranta mata asali zai gane she has a Barrister as a brother and 2 other elder Brothers, not even outsider ko na cikin gida ne yace zai takura Mayraah i in particular can go to any extent na kwatar mata 'yancin ta, i will take that personally i am assuring you Abba, don haka har abada babu aure tsakaninmu da Mayraah, she remains our blood sis" Yana kai wa nan ya mike yace "I want to excuse my self sir" Abba ya gyada masa