Sashe 104
Mayrah Complete Hausa Novel · about 1 min read
ya bude kofar parlon ta daga kai da sauri, ganinsa ta mike ta nufesa da damuwa tace "Baby ya jikin nata, har na gaji da kiranka a waya baka dagawa, kaga tun dazu sai yanzu na iya dafa Indomie zan ci...." Takardan dake hannunsa ya jefa mata ya juya ya fice daga parlon, ta dinga kallon takardan gabanta na wani irin faduwa, da kyar ta durkusa ta dauka ta warware tana duba content din, wani ihu ta fasa ta bi sa a guje tana cewa "Maheer ka sakeni saki daya kamar yaya??? ban gane ba Maheer, ni din ka saka?" Amma tuni ya shige motarsa ya bar layin, shi dai mai gadi sai zare ido yake.