Sashe 124
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
abinda ke faruwa" Badiyyah na shessheka tace "Gidan ya Maheer kawai na tafi shi kuma bai dawo ba sai da daddare sannan nayi bacci, shine yanzu da safe na zo nan" Ammi ta zauna tace "In sha Allahu za a san yanda za ayi, za a samu malaman" Duk da Ammi har cikin ranta take jin she have nothing to do with Mayraah anymore, ta dalilin Mayraah ta ga abubuwa marasu dadi da bata taɓa expecting a rayuwarta ba, ta dalilin Mayraah yau rabonta da gidan mijinta wata daya currr kuma har a lokacin ko bin ta kanta Abba bai yi ba, yanzun ma ba don Hajja da ta tilasta ta koma gida saboda Umar dake hanya ba ko shekara nawa za suyi ita da Abba a haka sai dai su yi, wai duk ta dalilin er da ba karamin jahadi tayi ba na rainonta tun tana tsumma, er da da farko kin amincewa yayi ta rike ta, shine yau saboda ita yayi mata wannan rashin mutuncin da girmanta da shekarunta, bata taɓa da ta sanin abinda ta aikata na alkhairi irin wannan ba, tayi da ta sanin don ko jin sunan Mayraah ma bata son yi, duk da wannan abubuwan amma deep down tasan Mayraah bazata yi abinda Badiyyah tace ba, dama can Badiyyah na da history din satan amsa a koreta a school, idan kuma ba satan amsa ba to point din ta will be very low har sai an koreta a makarantar, Hajja tace "Mu muka ga karshen taimako, dama ance ba kowa taimako ya ke amsa ba, mu kam bai amshe mu ba wallahi" [7/8, 5:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer na zaune parlon Hajja wajen karfe biyu da rabi na rana bayan kiran da Ammi tayi masa, duk tunaninsa gida zai maida ta kamar yanda dai suka tsara a jiya da ya zo gidan, don ba karamin kai ruwa rana akayi ba kafin Ammi ta yarda zata koma gida, at first she was reluctant don tace ita da komawa gidan Abba sai dai wani ikon Allah kuma, kusan kullum idan Maheer yaje gidan hakuri kawai yake bata ta janye vow din nan da tayi ta koma gida, yawanci ma abinda ke kai sa gidan Hajja kenan kawai ya ba Ammi hakuri har cikin ransa he is not happy da zaman gidan Hajja da take, gashi ba isassun dakuna, don ma Badiyyah na gidansa banda haka dole sai dai tayi sharing daki da bandaki da ita don yasan Ammi bazata dinga kwana dakin Hajja ba, to a jiya sai da Hajja ta saka baki har da nuna bacin ranta, wanda a baya idan yana ma Ammi magiyan ta koma gida sai dai Hajja ta kyabe baki ta kauda kai, wani lokacin kuma tace shi Mamudan ai bai biyota ba har yau balle ta kwashi kafa ta koma masa gida kamar bata da gata, to jiya dai kam Hajja ta saka baki kan Ammi tayi hakuri kawai ta koma don 'ya yanta amma ba don Mamuda ba, wanda hakan na nuni da ita ma abun ya fara isarta tunda Abba yaki waiwayansu balle ya biyo su har sannan, da yake Ammi na jin maganar Hajja kuma bata son duk abinda zai sosa ranta wannan yasa kawai ta yadda zata koma amma ba don ranta ya so ba sai don babu yanda ta iya, Shiru Maheer yayi yana kallon Hajja har ta kai aya rai a bace, Maheer ya ma rasa abinda zai ce tsabar mamaki, kullum sake mamakin mugayen halin Badiyyah yake, dama tun da ta kyallara ido ta ga ya shigo gidan ta saka kai ta fice daga gidan tunda tasan abinda ta hada, after few seconds Maheer ya girgiza kai very careful with his words kar ya tunzura Hajja ko ya bata ma Ammi rai yace "Hajja karya Badiyyah take gaskiya, jiya da na koma gida idonta biyu bata yi bacci ba don a parlor na sameta zaune har na tambayeta ya jarabawa tace min Alhamdulillah, amma ku nan tace maku ai tayi bacci kafin in koma gida, yanzu kawai abinda zai faru kamar yanda Ammi tace aje a samu Malaman sai mu je tare da ke ko Ammin ai suna wajen sanda abun ya faru sai su mana bayanin duk yanda aka yi a ajin, ae su baza su yi karya ba" Hajja ta katse sa tace "Ka ji ka da wata magana, zuwa za ayi a titsiye su kake nufi kenan, mutanan da za aje a lallaba su yi hakuri su bar ta ta koma ta ci gaba da jarabawanta kake so a je a kure, ai zuwa kawai za ayi a lallaba su ba wai a titsiye su ba, cuta ne an riga an cuceta kawai sae kuma neman mafita" Maheer ya gyada kai don bai son jan zancen yace "Toh shikenan, zan je makarantar ranan litinin in sha Allah" Hajja ta hade rai tace "Me ya hana baza ka je yau ba sae Litinin?" Yace "Yau asabar babu makaranta ai, sai Litinin din" Hajja tace "To Allah ya kai mu, amma ina lafiya za a kori yarinya da tayi shekara biyar tana wahala a makaranta ga uban kashe kudi" Maheer ya kalli Ammi yace "Za mu tafi ne yanzu Ammi?" A takaice Ammi tace "Ban shirya ba" Shiru yayi, sai kuma ya mike yace "Toh zuwa Anjima zan dawo" Ammi tace "Kar ka ba kanka wahala ban yi niyyar zuwa ko ina yau ba" Hajja tace "Aa ke kuma, anjima da la'asar kawai ya dawo ya kai ki gida tunda haka aka tsara idan ya so ranan litinin din sai yaje can gidan ya dauke ki ku je makarantar tare a ba Malaman hakuri, idan ma wani abu za a basu ko kaɗara na ne sai in siyar a basu" Maheer dai yayi masu sallama ya juya ya fita daga Parlon, shi dai ba kawai ya ji su ba ya kuma lallaba ya bar parlon ba tare da yayi masu musu ba, sun zata primary school ne da za aje a ba Malaman hakuri, motarsa ya shige ya bar anguwan, ban da yana da plan dinsa na barin Badiyyah a gidansa da yau ya koreta wallahi but there is still time. Da sallama Maheer ya shiga parlon Abba ta dalilin kiransa da yayi shi ma, don ko gida bai karasa ba daga gidan Hajja sae ga kiran Abba, hakan kawai yasa ya nufi gida maimakon gidansa da yayi niyyar komawa, tun shigowarsa gidan mood dinsa ya canza gaba daya don har bai son zuwa gidan saboda rashin Ammi da Mayraah, the house is soo empty without them, ya zauna ƙasan carpet ya gaida Abba dake duba wasu takardu, Abba ya amsa sannan yace "Yauwa kace Mayraah sun gama jarabawan ae ko?" Yace "Eh sun gama" Abba yace "Good, kaje ka dawo da ita da kayanta gaba daya yau" Maheer yayi shiru yana kallonsa shi ya so ace sai Ammi ta dawo kafin Mayraah ta dawo gidan, Abba yace "Ko kuna da wani plan da ku ka kulla kai da uwarka ne kake kallona haka?" Maheer ya sunkuyar da kansa bai ce masa komai ba, Calmly Abba yace "Wai ma tsaya tukunna in tambayeka, ana nufin ni a gidana bani da wani say sai abinda uwarka da danginta suka shirya? Yau ko ba Mayraah ba idan nayi niyyar kawo yara goma gidan nan akwai wanda ya isa yayi questioning dina akan haka? To a yau ba sai gobe ba nace ka dauko Mayraah ka dawo da ita gida tun da sun gama jarabawan" Maheer ya gyada kai cikin sanyin murya yace "Dama zan dawo da ita kamar yanda kace Abba, kawai nayi tunanin sai zuwa next week tun da basu gama project ba har yanzu" Abba yace "To yau nace ka dawo da ita ba next week ba, zata karasa project din a nan, wai ku kuna ma da imani kai da mahaifiyarka da danginta kuwa? That gal is an orphan, ta taso bata san kowa ba sai mu, all of a sudden this unforeseen circumstance came from no where, idan bamu ja ta jiki mun yi consoling dinta ba a wannan stage din depression ake son ta shiga at her young Age?? she neva bargained for this, ita haka Allah ya kaddara mata kuma babu bawan da ke wuce kaddararsa, wallahi Baabarka ta ban mamaki ainun, ba a taɓa disappointing dina irin yarda mahaifiyarka tayi disappointing dina ba, da wannan abun da tayi ma ni da Mayraah akan selfish interest dinta da relatives dinta wllh gwara ace asara nayi na miliyoyin kudi, ban taɓa expecting haka daga gareta ba ko a mafarki, kuma in har tana ganin ita bazata iya dawowa gidan nan don ta ci gaba da rike Mayraah ba to ta sha zamanta duk inda take, don ni a jiya na riga na auro warce zata zauna tare da Mayraah a gidan nan, na kara aure saboda Mayraah, da ban yi niyyar gaya maku ba sae dai ku gani da idonku amma ynzu na gaya maka zuwa anjima ita warce na auran zata tare in sha Allah, wannan ne dalilin da yasa nace ka dawo da Mayraah gida, ita kuma mahaifiyarka taje can ta karata for all i care, all this while da kaga na amince da zaman Mayraah a hostel saboda nasan bazai yiwu ta zauna ita kadae a gida ba ni na tafi sabgogina, kai kana gidanka Usman kuma bai gari, shi yasa kawai na hakura da zamanta a hostel...." Maheer ya dinga kallon Abbansa babu ko kiftawa, and u can see the shock written all over his face, kasa cewa komai yayi tsabar yanda ya girgiza, Abba yace "In kuma baza ka je ka daukota ba ni zan je in daukota da kaina a hostel din yanzu" Maheer ya mike still bai daina kallon Abba ba, he was speechless to ya ma rasa abinda zai ce, can ya juya ya fita daga parlon ya kulle masa kofa, sai a sannan yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Har ya fara sauka downstairs kawai ya juya da sauri ya sake komawa Parlon Abba, sosai hankalinsa ya tashi yana shiga parlon, Abba ya daga kai yana kallonsa, Maheer ya karasa ya zauna pleadingly yace "Abba don girman Allah kayi hakuri