← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 145

Sashe 106

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/2, 6:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe sha dayan dare sannan ya kalli Usman dake danna wayarsa yace "It's getting late, baza ka tafi gida ba?" Usman ya daga kai ya kallesa yace "I should be asking you that kai da kake da iyali a gida" Maheer yayi shiru bai sake ce masa komai ba, lkci lkci yake kallon Mayraah da ta koma bacci tun dazu, ganin har sha biyu Maheer ya mike ya dau makullin motarsa without looking at Usman yace "Sai da safe" Usman yace "Allah ya tashe mu lafiya" Bai ce masa komai ba ya fice daga ward din ya kulle kofar... Through out night din Usman bai yi wani bacci ba, he kept a close eyes on Mayraah dake ta bacci just to make sure is okay, karfe biyar saura na asuba aka bude kofar ward din ya daga kai ya ga Maheer ya shigo, Ajiye ledan hannunsa me dauke da hijab din Mayraah da toothpaste and brush yayi, sannan ya ajiye takalmanta a kasa kusa da gadon ya juya ya fita daga ward din, sai da aka kira sallah Usman ya fita shi ma. Da safe karfe bakwai da rabi aka yi discharging din Mayraah daga asibitin, suna isa parking space da brothers din nata taga ko wannensu da motarsa a nan, tsaye tayi gefe daya not knowing motar wanda zata shiga cikin su, Usman dai ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar su tsaye wajen yayi wucewar sa from the hospital, Mayraah ta bi motarsa da kallo sannan ta bude motar Maheer a hankali ta shiga ta zauna. Kusan a tare suka isa gida sai dai Usman ya riga su shiga cikin gidan, Maheer na gaba tana biye da shi suka shiga gidan, zaune suka tadda Usman a parlorn downstairs tare da Mama Ladi dake cusa lafcecen kwai cikin biredi tana dannewa, ga cup din shayinta a gefe tana cewa "Wallahi yanzu haka wai suna asibiti, ko wani asibiti ne oho, wa ya sani ko gantalinta zata je mota ya kade ta, tun karfe hudun asuba Ammi ta bar gidan nan har yanzu babu ita babu alamarta inji Saliba me aikinku, ni dai nace sai na ci na koshi kafin inje ko ina babu ruwana da lalacewa inje yunwa yayi min lahani ayi min hisabi da yan hanjin cikina ranan gobe kiyama" Shigowan Maheer da Mayraah yasa ta daga kai tace "Yauwa Mashir wai me ke faruwa haka ne? Saliba tace min Ammi tun asuba ta bar gidan nan" Maheer ya karasa ya zauna kan kujera yace "Sabira dai ko, ina kwana..." Mayraah dai tafiya take a hankali ita ma tana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta yagi kwai da bread ta kai baki tana cewa "Ni jiya da wuri nayi bacci bayan na ci abinci ban san kan komai ba wllhi, ita Salibar ke gaya min an kai Badiyyah asibiti" Bata rufe baki ba Ammi ta shigo parlon rike da basket din flask da kayan shayi, Maheer da Usman suka juya suna kallonta haka ma Mayraah da ta nufeta zata amshi basket din hannunta tace "Sannu da zuwa Ammi" Ammi bata ce mata komai ba kuma bata bata basket din hannunta ba ta wuceta ta karasa cikin parlon tana kallon Maheer da Usman tace "Ina jiranku a sama...." Daga haka ta ajiye kayan hannunta ta wuce sama, duk suka bi ta da kallo, har Mayraah da ke tsaye inda Ammi ta bar ta, Mama Ladi na kora bread dinta da shayi tace "Ko kudi za a harhada na trintment din Badiyyar tunda dai duk mun san dangin ubanta matsiyata ne, tun tana karamarta Ammi ke mata komai sai Mamuda da Hajja da ni, sai kuma ku da ku ka kawo karfi yanzu, ku dai je ku ji, iyaka ku bada dubu daddaya ta rabaku da kowa lafiya tunda ba wani ya aiketa ba...." Usman ya fara mikewa ya wuce sama, Maheer ya tashi ya bi bayansa shi ma, Mayraah dai ta kasa karasawa cikin parlon ta zauna, Mama Ladi ta mike ta dau shayinta da bread tace "To ya ma za a bar ni a nan sai kace wata bare..." Sai kuma ta kalli Mayraah tace "Zo ki dau min shayin nan mu tafi sama kar garin hawa benen nan in barar in shiga uku ance milo ya kare, duk an wani watse a bar mu kamar mun ci mutum" Mayraah da gaba daya jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin hakan, ta karasa gun Mama Ladi ta dau mata shayin suka wuce sama a tare. Usman na shiga parlon Ammi ya ga Haseenah zaune kan kujera da hijab dinta har kasa sae counter din carbi a hannunta, duk da yayi mamakin ganinta ya gaisheta a takaice ya shiga dakin Ammi, Maheer ya shigo Parlon few seconds later, he was very very surprise to see Haseenah sitted in Ammi's parlor, ya dinga kallonta, suna hada ido ta kauda kanta ta wani daure fuska tana daddanna counter din hannunta, lkci daya yaji wani mugun ɓaci rai ya zo masa, but ya dai yi calming kansa down bai ce mata komai ba ya wuce dakin Ammi, tsaye ya ga Ammi bakin window duk tana jiran su, kallo daya Usman yayi mata bai ma karasa can cikin dakin ba ya tsaya daga gefen kofa cause her facial expression isn't giving, Maheer ne yayi karfin halin karasawa ciki yana kallonta shi ma, daga shi har Usman babu wanda ya iya bude baki ya gaisheta don basu ma ga fuskar yin haka ba, Mama Ladi ta shigo parlon Ammi Mayraah na biye da ita, buda baki tayi ta koma baya da sauri ganin Haseenah, cike da mamaki tace "Ke kuma daga ina matar nan? Ko dai ba da ke aka tafi jiya ba?? Ni fa na raka ku har mota, garin yaya haka na ganki a nan?" Haseenah dai ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi ta nufi dakin Ammi tace "Yau ni naga ikon Allah" Mayraah bata bari sun hada ido da Haseenah ba ta ajiye Shayin hannunta a kasa sannan ta zauna kan carpet din parlon, tun da Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo ta kyabe baki ta kauda kai tana girgiza kafa.... Maheer yayi gathering courage yana kallon Ammi yace "Ina kwana Ammi" A fusace Ammi tace "Ban kwana ba, nace ban kwana ba..." Kallonta kawai Maheer yake yayi shiru, Ammi na nunasa cikin bacin rai tace "Before going into my main point ina son ka maida matar ka immediately first..." Maheer ya sunkuyar da kansa, Ammi ta masa tsawa tace "Are you deaf, ko baka ji na ne?" Ya dago kai a hankali yace "I have done that" Mama Ladi da ta shigo dakin ta buda baki tace "Wai me yake faruwa ne kike daga murya haka? Me ke faruwa ni Ladiyo? Wace matar za a mayar?" Ammi bata ko kalleta ba tana kallon Maheer tana gyada kai tace "Sai yanzu na fahimci inda Hajja ta dosa all this while, sai yanzu na gane abinda take son ta fahimtar da ni na kasa ganewa, i now fully understand Mimi is nothing but a nuisance in our midst now, she is beginning to cause nothing but chaos in this family, kai ka saki matarka da ko sati uku ba kuyi da aure ba duk a saboda ita, shi kuma ɗan uwanka ya sake komawa for the second time yayi ma Badiyyah dukan tsiya duk a kanta ba tare da yayi binciken abinda ya faru ba, a saboda yarinyar nan har yau mahaifiyata bata ɗaga wayata, ko naje inda take babu maganar arziki tsakanina da ita all because of Mimi, is that how she wants to pay us by destroying us? Toh all this is going to end now" Cikin daga murya Ammi tace "Maheer from today henceforth she is not staying in ur house any more, bazata sake zama a gidanka ba nace...." Maheer couldn't believe this is really coming out from Ammi's mouth, ji yayi kansa ya wani sara masa yana kallonta cike da karfin hali yace "Where will she stay then?" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't care Maheer, idan ma kai da Usman za ku dawo hankalinku ku dawo, baku hada komai da ita ba, i repeat babu abinda ku ka hada da ita in any way, she is not ur blood, and because of her bazan zuba ido zumunci ya lalace ba, Ita Badiyyar da ku ka mayar makiyiyarku ita ce dolen ku duk inda za a je kuwa, ita ce er uwarku ta jini, sannan baza ka taɓa hada matar da kake aure da ita ba, matar ita ce dolen ka ba ita ba" Usman ya dinga kallon Ammi da mamaki babu ko kiftawa, jin maganganun nata yake kamar a mafarki, Mama Ladi dai sai zazzare ido take duk da turanci yafi yawa a maganganun amma sarai ta fahimci komai, salati ta saki tayi zaman dirshan a kasa tana girgiza kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Hajaru yau kece kike wannan munanan kalaman akan Mera? Me suka baki kika sha a asibitin Hajaru, yau mun shiga uku mun lalace, ina ake son Marainiyar ta sa kanta taji dadi kenan?" Kawai sai ta fashe da kuka wiwi, Maheer dake ta kallon Ammi ganin zata fita ta bar masu dakin, a hankali yace "Ohk then, tunda kince babu abinda muka hada da ita, sannan ita din ba jininmu bace yanzu na yarda kuma na amince da hakan, as at before i was still doubting that, don bamu ji kin gaya mana hakan da bakin ki ba duk abubuwan da suka faru, it was hard for us to assimilate Mimi isn't our blood all this while, but after saying this today naji na yarda da hakan har cikin raina, saboda haka ni
Chapter 106 · 0% Book details