← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 145

Sashe 2

Mayrah Complete Hausa Novel · about 11 min read

Ranan litinin da safe Mayraah na zaune cikin department dinsu tare da kawarta Hamida da wata Coursemate dinsu Amira, tun dazu suke tsokanarta wai amaryar next month, ita dai handout din hannunta kawai take dubawa pretending bata san da ita suke ba, a ranta kuma she is regretting telling Hamida, don tun ranan da aka kai kudin ta kirata ta gaya mata don bata da kamar ta a kawaye... Daga wani bangare na Department din clique din wasu yan mata ne in their early thirties su uku a zaune, Farar cikinsu ta gyara zama tana kallon kawayenta biyu Aisha da Amina with shock written all over her face tana sauraron abinda suke gaya mata, Aisha tace "Wllh Surayya ce taji Hamidah na ta tsokanarta da suka shigo department shine ta zo ta gaya mana, amma kar ki ce mana baki da labari, mu nan muna ta jiranki mu sha labari" Amina ta rike haɓa tace "Ikon Allah, wato baki ji ana zancen a gida ba kenan? To ko dae karya ne" Badiyyah da ta ji wani zufa na keto mata ga wani sanyin dake shigarta duk lokaci daya, ta girgiza kai cike da karfin hali tace "Kinsan naje weekend gidan yayan Babana a Bichi, yanzun ma daga can na taho makaranta...." Sai kuma ta mike ta dau jakarta tace "Bari kawai in tafi gida" Tashin hankalinta kwata kwata bai boyu ba, Amina da Aisha suka hada baki wajen cewa "Toh Lectures din fa?" Aisha ta kara da cewa "kinsan fa yanda attendance dinsa yake, kuma saura minti kadan karfe goman yayi..." Ko sauraronsu Badiyya bata yi ba ta nufi hanyar fita department din da sauri, Mayraah ta bi ta da kallo don sai a sannan tayi noticing dinta, Hamidah tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace "Hope tasan an kai kudin aurenki?" Mayraah tace "I don't know" tana fadin haka ta mike ta ajiye ma Hamidah jakarta tace "Zan yi alwala in dawo" Hamida tace "Saura fa minti bakwai, yanzun nan zaki ga ya shiga class fa" Mayraah tace "Bazan jima ba" Daga haka ta bar wajen da sauri zuwa inda zata yi alwala, ko minti biyar Mayraah bata yi da barin wajen ba sai ga lecturer din, Hamidah ta mike da sauri ta tafi inda suke sallah a department din ta tadda Mayraah ta tada sallah, tuni student suka shige lecture hall sanin wanene lecturer din not because he is strict or he have problem, but because of him being a principal person, Hamidah da Amira ma tuni suka shiga Hall din suka nemi wajen zama. Yana ta tsaye gaban rostrum dake hall din, ya jira har student din suka yi settling, idonsa na kan roll din da su Hamida ke zaune amma saboda glasses da yake sanye da baza kace ga direction da yake kallo ba, the class became absolutely silent in just few seconds, kowa kuma idonsa na kan lecturer din, after about a minute ya gaishesu gaba daya sannan ya fara abinda ya kawosa ajin, wasu student biyar maza da mata ne suka karaso bakin kofar hall din da sauri, sai dai basu yi gigin shigowa ajin ba sanin rules dinsa, kallonsa kawai suke with pleading eyes, bai ce masu komai ba ya ci gaba da bayanin da yake ma class din, ganin they are distracting ya kalli wani student dake front roll zai ce masa ya kulle kofar kawai ya hango ta, da sauri ta kauda kanta ganin direction dinta yake kallo, Ya dae ci gaba da lecturing dinsa, bayan some minutes ya kalli wa enda ke gaban kofa yace "Fine! You can come in, but no attendance for u all" godiya suka dinga masa suka shigo class din, ita ce karshen shiga, taki yarda ta kallesa ya bi ta da kallo ta cikin glasses dinsa, ta nufi wajensu Hamida don sun ajiye mata seat ta zauna, ya ci gaba da bayanin da yake, Hamida tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace "Dama nasan dole a shigo tunda da ke a ciki" Ita dai Mayraah bata ce komai ba ta ciro littafinta da biro ta fara rubutu, duk wani student da suka zo daga baya ya bar su sun shiga ajin sai dai fa basu da attendance kamar yanda ya ce. Karfe sha daya da minti arba'in ya gama lectures dinsa ya fita daga hall din. Wani Coursemate dinsu me suna Bashir ya nufo Mayraah yace "Hajiya Mayraah mu bi bayanki mu tafi mu basa hakuri mana, wllh bani da attendance dinsa wannan semester din, kuma duk wanda bashi da attendance dinsa baya test kun sani" Mayraah ta daga kai ta kallesa ta ɗan buda ido tace "Ni kuma?" Sai ga sauran student din duk sun karaso wajen ta suna mata magiyan tayi masu jagora zuwa office dinsa, Mayraah ta ajiye biro din hannunta tace "Ni ma fa bani da attendance din nan, kuma me yasa sai ni zan bi ku" Duk suka hada baki wajen cewa "Saboda kece assistant class rep mana" Ta ɗan yi murmushi tace "Tun yaushe na ajiye maku wannan post din" Hamida tace "Ba wani ke dae kawai ki tashi ku je" Ganin yanda suka takurata, sauran yan ajin na taya su yasa Mayraah ta mike tace "Toh mu je, idan ya koro mu ai shikenan ko" Haka nan suka tisa ta a gaba su kusan goma sha biyu zuwa office dinsa dake sama, Dr M-Abdallah shine sunan dake rubuce saman kofar office din, duk yanda suka yi da ita ta yi Knocking ta fara shiga ki tayi, ta koma gefe tace "Haka kawai ya koreni, wani dai yayi sallama idan yace a shigo sai duk mu shiga" Bashir yayi Knocking hade da sallama, sai da yayi masa izini sannan ya bude kofar ya shiga, Dr Musharraf na kallonsu a bit surprise yace "What happened?" Mayraah dai na makale jikin kofa wanting to hear him say get out, gaba daya student din kuma ita suke jira tayi magana, can dai ta ɗan kallesa a hankali tace "Sir hakuri muka zo baka don Allah a bamu attendance mu rubuta, we are sorry for coming late" Sai da ya fara sauke idonsa, sai kuma ya matsar da laptop din gabansa ya ɗan kalleta yace "I see... Ke ce mouthpiece dinsu kenan." Sunkuyar da kanta tayi, Bashir da sauran student din suka ce "Sir don Allah ayi mana hakuri, baza mu maimaita ba in Allah ya yarda" Dr Musharraf ya dau attendance sheet din gabansa ya mika ma Bashir, Bashir ya karasa da sauri ya amsa yana masa godiya tare da sauran daliban, Dr Musharraf yace "You can sign the attendance outside" Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta juya ta fita daga office din da sauri don dama a makale take jikin kofa, Bashir na signing ya mika mata ta amsa ita ma tayi, ta ba warce ke kusa da ita, har ta fara sauka stairs zata koma gun su Hamida wayarta dake hannunta yayi vibrate alamar shigowar message, duba wayar tayi... "Stay behind" shine content din message din, jingina tayi da stairs din kamar zata yi kuka don bata so haka ba, can dai ta koma daya bangaren corridor din stairs din ta tsaya, tana ganin Coursemate dinta duk suka sauka kasa bayan sun rubuta attendance din, babu kuma wanda yayi noticing dinta a cikinsu a hankali ta fara tafiya zuwa office dinsa, tana isa kofar ta kwankwasa a hankali, jin bai amsa ba ta yi sallama, sai da taji ya amsa sannan ta shiga ba tare da ta kallesa ba ta kulle masa kofar, kallonta kawai yake, tana tafiya slowly ta isa gaban table dinsa without looking at him ta ɗan risina tace "Good morning sir" Calmly yace "Mayraah" ta ɗan kallesa, sosai gabanta ya fadi taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, bata san sanda ta zauna kan daya daga kujerun dake facing dinsa ba amma bata bari sun kara hada ido ba, yace "Why were you late to my class?" Ta girgiza kai tace "Sallah naje yi" Bai ce mata komai ba, bayan few seconds yace "Look at me" Da kyar ta dago ta kallesa suka hada ido, da sauri ta daura goshinta kan table dinsa tana jin wani sabon kunyansa da bata san dalili ba ita ma, ɗan murmushi yayi bai dai ce mata komai ba, ganin taki dagowa bayan kusan 40 seconds yace "Shikenan... Idan baza ki dago ba tashi ki tafi" Kamar jira take ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa ya bi ta da kallo, kafin ta fita yace "Sai ki nemi wanda zai duba maki Defense slide dinki" Da sauri ta juyo ta kallesa ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" Yace "Toh dawo" Ba musu ta dawo tana sinne kai ta zauna, yace "When next ku ke da lecture yau" Tace "Sai 2" Yace "Ohk, kin zo da laptop din ki?" Ta girgiza masa kai, yace "Turo min slide din naki ta Email yanzu" Tace "Toh" Slide din ta shiga nema a wayarta zata tura masa, shi ko sai kallonta yake, can a hankali yace "Kwana nawa su Ammi suka gaya maki anyi fixing?" Sosai gabanta ya fadi, taki dago kanta balle ta basa amsa, maganar da take ta fatan kar yayi mata kenan, yayi murmushi yace "Look Mayraah...." Still taki dago kanta sai ma hade rai da tayi, yace "Toh tashi ki tafi" Da sauri ta kallesa tana buda manyan idanuwanta ta marairaice tace "Duba maka slide din nake fa Sir" Murya can kasa yace "I love you" sunkuyar da kai tayi har da rintse ido, kawai jin kamshin turarensa tayi sharply hakan yasa ta bude ido da sauri ta gansa a gabanta, ta fara kiciniyar mikewa tsabar rudewa ta harde kafa sai ga ta a kasa, ya koma baya da mamaki yace "Meye haka kike yi, do u want to injure ur sef?" Tuni ta mike tsaye kamar zata yi kuka tace "Na tura maka sir" ya duka yana kallon kafafuwanta to be sure bata ji ciwo ba, sai kuma ya mike yace "Ta fi kiyi wucewarki, gobe ki kawo min hardcopy uku na slide din" Da sauri tace "Ok Sir" Sai kuma ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, zaunawa yayi saman kujeran da ta tashi yayi letting out sigh, wondering if she will ever change, ya ga kamar kullum abun ta kara gaba yake. Karfe daya da 'yan mintuna Mayraah na zaune tare da su Hamida a class suna jiran lokacin next lecture dinsu yayi taji wayarta yayi vibrate, dauka tayi ta duba taga sako ne ya shigo, bude message din tayi tana kallo, "Ina jiranki a parking space" shine abinda ta gani a rubuce, ta kalli su Amira da Hamida ta mike tace "Ina zuwa yanzu" Bata jira cewarsu ba ta nufi kofar fita, Mayraah na isa parking space ta karasa har inda ya ajiye lafiyayyen motarsa wanda babu tantama yana ciki a zaune, zagawa tayi ta daya side din amma bata bude motar ba har sai da ya bude daga ciki sannan ta shiga ta kulle motar, maimakon ta kallesa sai ta fara wasa da Hijab dinta, ledan eatry dake back seat ya dauko ya mika mata ta ɗan kallesa sannan ta amsa tace "Nagode" Yace "Duk sanda kika gama lectures ki kirani, am going home now" Ta gyada masa kai, yace "Sai anjima" Bude motar tayi ta sauka tace "Allah ya saka da Alkhairi" Ta kulle masa motar ta nufi cikin department ya bi ta da ido.
Badiyya na isa gida ko sallama babu ta shiga parlon kakarta, hankali tashe ta jefar da jakan hannunta tare da siririn mayafinta, Hajja kaka dake zaune parlon ta bi Badiyya da ido tace "Ke kuma lafiyar ki?" Badiyya ta zube gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta yi saurin dauke kopin kunun dake gabanta tace "Subhanallahi, lafiya Badiyya? Wani abun suka maki a can Bichin?" Cikin kuka sosai Badiyya tace "Wai Hajja da gaske an kai kudin auren Mayraah?" Hajja na kallonta da mamaki tace "Kudin Mayraah? Ina ruwanki kuma da wata Mayraah, yarinyar da ko ga maciji bakya yi da ita, kudi kuma ai yau kwana uku kenan da kawowa, shawara kika so ayi dake kafin a amsa kudin ne ko ko?" Badiyya ta daura hannu a ka ta kara rushewa da kuka tace "Amma Hajja na taɓa ce maki ina son mutumin fa amma kika bari aka amshi kudin nan, wayyo na shiga uku na lalace" Hajja ta koma baya a firgice tace "Anya kanki daya kuwa Badiyya? Me ya sameki haka? Ina ruwanki da mutumin da bai ce yana son ki ba? Ba ga ki da samarin barkatai na banza da na kirki ba, meye sai na Mayraah zaki sa ma ido fisabilillahi? Me yarinyar nan ta tsare maki a duniya ne?" Badiyya tace "Wallahi sai dai ita ma kar ya aureta duk mu hakura..." Hajja ta matsa daga kusa da ita a tsorace tace "Lallai ban san baki da hankali ba sai yau, ita er uwar taki kike ma baƙin ciki kiri kiri babu sakayawa Badiyya?" Mikewa Badiyya tayi tana kuka tace "Ni ba er uwata bace, babu abinda na hada da ita" Daga haka ta shige dakinta da sauri, Hajja ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "To Allah ya sa ki gane, idan ba haka ba ai sai ki zama masifa da annoba a al'umma, ni dai ban taɓa ganin haka ba tun zuwana duniya...."
Chapter 2 · 0% Book details