← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 145

Sashe 144

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka tarar bama nan, don za a sallame mu inji likita" Musharraf yayi murmushi ya gaisheta yace "Ai ina asibitin dama ban tafi ba" Mama Ladi tace "Allah sarki" karasawa yayi ya ajiye ma Mayraah jakarta na makaranta yace "Kin ji sauki sosai ko?" Ta gyada masa kai, yayi kasa da murya yanda Mama Ladi baza taji maganar ba yace "Can i come home in dubaki?" Sai a sannan Mayraah ta daga kai suka hada ido, tayi saurin sauke idonta tace "Gobe in sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Ameen" Musharraf yace "Dr din yace min Abba is on his way zai kai ku gida yanzu, so ni zan wuce, and i need one favor from u pls Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa, a hankali yace "Unblock me plss" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Pls" Ta bude jakar ta ciro wayarta, yana kallonta tayi unblocking digit dinsa, a hankali yace "Saura Whatsapp" nan ma ta shiga tayi unblocking dinsa, ya sakar mata murmushi yace "Thanks" Daga haka ya juya yayi ma Mama Ladi sallama tace "Au har zaka tafi kai ma, toh mun gode Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen ya Allah Mama, Allah ya kara mata lafiya" Mama Ladi tace "Ameen, idan ya so ko gida ne zaka iya zuwa ka dubata kanka tsaye kaji?" Yace "In sha Allahu zan zo gobe" Mama Ladi na washe baki tace "To muna nan muna jiranka" Daga haka ya fita daga ward din, Mama Ladi ta dawo kusa da Mayraah tace "Ke ko dai sonki yake ne, wannan kulan da yake baki kamar ba banza ba wllhi" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa ba haka bane" Mama Ladi ta koma ta zauna tace "To ke me kika sani, mu da muka ga jiya muka ga yau, Allah dai ya kawo sa goben ni zan bincikesa don bana son nuku nuku" Mayraah dai bata ce mata komai ba, ana idar da magrib Abba ya iso ya daukesu duk suka wuce gida. Suna isa gida bayan Abba yayi parking Mayraah ta sauka daga cikin motar, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Jira za mu yi magana Mamuda" Abba yace "To Mama" Mama Ladi ta sauko daga motar tana kallon Mayraah dake kokarin dauko abubuwan da suka dawo da shi daga asibiti tace "Yi wucewarki ki kwanta duk zan kwaso su, ina kika ga karfin jidan kaya" Juyawa Mayraah tayi ta nufi cikin gidan, Mama Ladi ta koma kusa da Abba tayi kasa da murya tace "Mamuda kasan bayan ƙin zuwa da wannan matar tayi har 'ya yanta ma ta hana su zo duba baiwar Allahn nan a asibiti? Wannan wace irin rayuwa ce fisabilillahi?" Abba ya dan yi murmushi yace "Ina sane Mama, tasa ai Usman da Umar sun bar gidan nan yanzu haka basa nan" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu, Abba yace "Amma zan dau mataki nan ba da dadewa ba in sha Allah, duk zan yi maganinsu har Maheer din" da sauri Mama Ladi tace "Aa don Allah kayi hakuri, nasan kayi hakurin nan kuma kana kan yi, amma don Allah ka ci gaba da yi sai kaga duk kamar ba ayi ba wllh, kaga ai ni bana goyon bayan mugun abun nan da suke, don haka sai kaji sanyi ta bangarena, ita kuma Ammi ka rabu da ita kar ka biyeta akwai ranan kin dillanci, su kansu mazan ka bar su su ci gaba da taya uwarsu goyon bayan rashin gaskiya su ma akwai ranan kin dillanci da ina masu kallon masu hankali ashe duk yan iska ne munafukai ace har Mashir yaki takowa ya duba marainiyar nan a gadon asibiti, amma ba komai, ita kuma Mera ni da wannan matar taka me hankali mun isheta a yanzu dai, kayi hakuri komai zai wuce in sha Allah" Abba da yayi shiru kansa a kasa yana sauraronta, ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan Mama nagode sosai" Mama Ladi tace "Yauwa Allah maka albarka, ka ci gaba da hakuri dan nan, duk me hakuri na tare da Allah" Ko da Mama Ladi ta shiga gidan dakin da Mayraah take ta tafi, nan taga Hajiya Amina har ta kai ma Mayraah abinci sama, Mama Ladi ta zauna kan darduma tace "Ni ma kawo min nawa nan kawai er nan" Hajiya Amina ta gaisheta tana mata sannu da zuwa sannan ta fita taje dauko mata nata abincin bayan ta ajiye ta fita. Hajiya Amina na kallon Abba bayan ta ajiye masa abincinsa tace "Alhaji ina da suggestion plss idan baza ka damu ba" Abba ya kalleta yace "To ina jin ki Amina" Ta ɗan yi murmushi tace "Alhaji ina ga fa kamar zamana a gidan nan ba mai yiwu bane with the way things are going, why not kawai ka bar ni in koma gidana kai ka dinga zuwa can din, idan kuma baka son zuwa gidana ne ko haya ne sai ka kama min ko da daki biyu ne Alhaji, ita kuma Mayraah zata iya dinga switching daga gidana zuwa nan gidan ta yanda uwar goyonta bazata kullaceni ba bazata kullaceta ba don yanzu koma waye gani zai yi kamar na zo ina shisshigin rabata da yarinyar ne which is not so, ina ga kamar wannan shine masalha kawai Alhaji, don a gaskiya abubuwa baza su daidaita ba haka sai dai su kara rikicewa, kaga ina dawowa gidan nan duk sons dinka sun bar gidan u just confirm that this morning, to saboda ni kuma kaga ai bai cancanci su bar comfort zone dinsu ba" Abba ya girgiza kai yace "Babu inda za ki Amina, u remain in this house, duk wanda bazai zauna saboda kina gidan ba ya tattara ya tafi duk inda za shi, as far as Mayraah is going to be comfortable bani da damuwa da haka, kowa yayi abinda ya ga dama gatan da suke da shi a yanzu dai ita bata da shi so my major concern now is Mayraah, kamar yanda nace su suna da gata ita kam bata da shi, zan bar su su yi duk yanda suke so....." Hajiya Amina tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon Abba, har yau fa common gaisuwan nan Ammi taki bari ya hada su, iyaka ta shigo kitchen tayi abinda zata yi ta wuce sama babu annuri a fuska. A daren Mayraah na kwanciya ta kashe wayarta ta rufe har kanta da bargo amma har karfe dayan dare idonta biyu ta kasa bacci, tana jin Mama Ladi na ta minshari a shimfidar da Hajiya Amina tayi mata a kasa, Mayraah bata ji dadin kwanciyar da Mama Ladi tace zata yi a dakinta ba cause she needs privacy a wannan moment din. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba taji Mama Ladi na wanka a bandaki bayan ita ma tayi sallan, Mama Ladi na fitowa ta bude akwatinta wanda suna dawowa daga asibiti jiya da daddare taje bangaren Ammi ta daukosa ta ajiye a dakin Mayraah, Ammi bata tambayeta ya mai jiki ba ita ma bata ce mata ci kanki ba, iyaka ta amsa gaisuwar da Ammin ta mata ta fita daga bangaren, Mayraah na ta kallon Mama Ladi har ta gama saka kayanta, ta yafa gyalenta tana kallon Mayraah tace "Ko zaki leka kasa kiyi ma wancan matar magana ta kawo min kumallo don ina da inda zanje yanzu haka" Mayraah tace "Toh" tana fita dakin bayan some minutes suka dawo tare da Hajiya Amina ta ajiye breakfast din hannunta ta durkusa tana gaida Mama Ladi, Mama Ladi ta amsa tace "Lafiya lau wllhi ke dai, dama zan je gidan yayata ne in gaisheta shi yasa zan karya kafin in fita kada in fita ba komai a cikina" Hajiya Amina tace "Hakan ma yayi Mama, bari a hada maki shayin" Bayan Hajiya Amina ta hada mata shayin ta zuba mata abubuwan da tayi for breakfast a gidan ta mike ta fita, sai da Mama Ladi ta tilasta Mayraah suka yi breakfast din a tare, Mayraah dai shayin kawai take sha da kyar, har Mama Ladi ta gama ta mike tayi gyatsa ta dau katon handbag dinta tana kallon Mayraah tace "Zuwa karfe goma zaki ga na dawo idan na gama abinda ya kai ni, kina shan maganinki ki fitar ma Amina da kwanukan ki ajiye mata can kitchen ki dawo ki kwanta kiyi bacci abun ki kinji" Mayraah felt so much relieve tana kallon Mama Ladi a hankali tace "Toh Allah ya tsare" Mama Ladi tace "Ameen daga haka ta fita daga dakin" Mayraah na ganin fitan Mama Ladi ta sauko daga kan gadon a hankali ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje, tana fitowa bayan ta shirya shima sharp sharp, ta nufi jakarta maidaidaici ta dauka, ta dau kwalayen phones din da Usman da Maheer suka siya mata kwanaki ta saka su a cikin jakar, sannan ta dau Atm card da Usman ya taɓa bata da nata Atm card din su ma ta saka a jakan, bin dakin ta dinga yi da kallo, ta shiga bandaki ta dau tooth paste da tooth brush dinta da sabulu da sponge ta saka su a Wani leda ta sa cikin karamin jakar, ta bude press dinta ta ciro iron hijabs dinta uku da dogayen riguna uku duk ta saka a jakan with few of her undies, ta dau perfumes kanana su ma ta saka a jakan sannan ta rufe jakar ta ajiye gefe daya, a hankali ta bude kofar dakin ta fita ta sauka downstairs tana kalle kalle, bata ji motsin kowa a kitchen ba, ta dawo sama da sauri ta dau handbag dinta ta rataye bayan ta sa charger dinta da power bank with lip gloss a ciki, sannan ta dau karamin jakar ta fita daga dakin gabanta na faduwa ta sauka downstairs ta nufi kofar fita, da sauri ta fice daga compound din gidan ta nufi bakin titi tana waige waige kamar munafuka ta samu adaidaita sahu yana tambayarta inda zata je tace "Tasha" sannan ta shiga da sauri. Hajja na kallon Mama Ladi da ta ki zama tace "Ke wa ya gaya maki wannan maganar Ladi?" Mama Ladi tace "Ka ji ki da wani zance kuma Hajja, nace maki Mashir din
Chapter 144 · 0% Book details