← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 145

Sashe 133

Mayrah Complete Hausa Novel · about 3 min read

kamar an bude pampo tace "Na gama zama da Mamuda, na gama zaman gidan nan, ya aiko min da takarda ta bayan na tafi kawai" Aunty Mariya tayi karfin halin zama kan kujera don tasan babu tantama Ammi taga Hajiya Amina kenan, cikin sanyin murya tace "Babu inda zaki je Ammi, nan din gidanki ne, babu wata warce zata hanaki zaman gidan nan, babu warce za ki tafi ki bar ma gidan nan ko ki bar gidan saboda ita..." Aunty Mariya ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka idonta tana taya Ammi jin zafi a ranta, Cikin kuka Ammi tace "Ni Mahmud zai yi ma haka akan yarinyar da na ci wahala kanta tun tana cikin dattin haihuwa, ni zai ma wannan walakancin akan Mayraah? Maheer ya cuce ni wllhi da ya bari na tako kafata na dawo gidan nan naga wannan abun bakin ciki da takaici, da nasan abinda zan dawo in tarar kenan bazan dawo ba Mariya har abada kuwa, nayi da na sanin abubuwa da yawa a rayuwata, nayi da na sani wallahi, alkhairi na aikata ya zamar min sharri daga karshe" Kuka Ammi take sosai tana girgiza kai, Tace "Maheer ya san ubansa ya kara aure shine zai je ya takurani in dawo gidan nan? In dawo in yi me kuma? Me zan dawo in masu? Wallahi ya cuceni" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu jin abinda Ammi ke cewa tace "Mamudan ya kara aure?? A ina kika ji wannan magana haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, aure fa??" Ita dai Aunty Mariya hawaye kawai take ta rasa abinda ma zata ce, Ammi ta ci gaba da fiddo sauran kayanta tana kuka, Mama Ladi ta rike kai tace "Huhuhu, ashe Mamudan ɗan iska ne dama bamu sani ba?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Hajja ce ta ja maki wannan jaraba, kina zaman zamanki lafiya gidan mijinki ta zuga ki kika koma ɗan kuturun gidanta ku ka takure waje daya numfashi da kyar, babu wani alawance din da mutum zai sake ya bararraje komai a takure kamar gidan mayu shi sa nake gudun gidan idan na zo kano na gwammace in sauka nan, yanzu ga irinta nan ta cuceki ta sa an dankara maki kishiya kina can kin saki baki, dama an gaya min wallahi, kuma da kika wani kwaso akwati er iskar da ya auro zaki bar ma gidan kike nufi?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty Mariya ta juya tana kallon kofar, can tayi karfin halin mikewa ta karasa tace "Waye?" Hajiya Amina tace "Ni ce" Aunty Mariya ta ɗan hade rai tace "Ana zuwa" Maida kayan Ammi ta dinga yi daki da sauri, tuni dama Ammi ta shige daki, Mama Ladi ma ta mike tana taya Aunty Mariya tura akwatunan da sauri duk da bata san ko wacece ba, Aunty Mariya ta fito bayan sun kai duk kayan daki ta bude kofar, Hajiya Amina ta shigo da sallama.
Chapter 133 · 0% Book details