← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 145

Sashe 76

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 [6/23, 8:19 PM] Khaleesat Haiydar💖: Har kiran Maheer ya katse Musharraf bai daga ba, can ya jefar da wayar kan gado ya hade rai yace "I see no reason why he should call me because u are missing, what does that mean?" ita dai bata ce komai ba, ta koma tayi lamo kan gadon tana kallonsa, Sake ringing wayar ya fara yi, Musharraf ya kalli screen din yaga Mami ce ke kiransa this time around, ya sauke ajiyar zuciya, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya dau wayan yayi picking ya sa handsfree ya ajiye gefen gadon yayi shiru, Daga daya bangaren Mami tace "Musharraf" A hankali yace "Good evening Mami" cike da damuwa Mami tace "Me yasa ka kashe wayar ka yau kwana uku kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, Mami tace "I am talking to you Musharraf" Musharraf yace "Ina hutawa ne" Mami tace "Kai kenan baza ka amshi kaddaran da Allah ya dora maka hannu bibbiyu ba kana matsayin ka na musulmi? baka tunanin nima kana saka ni cikin damuwa da sleepless night? Why will u just switch off u phones, Kasan adadin kiran da nake ma wayarka a rana kuwa?" Yayi kasa da murya yace "Am good Mami u need not to worry about me, i will take care of my self, nace maki kawai hutawa nake" Mami tace "Yanzu kana ina?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Abuja" Tace "To ka dawo gida Musharraf, hankalina baxai taɓa kwanciya ba idan ba gida ka dawo ba na ganka, it's not the end of life don an rabaka da warce kake so, dama can Allah ya riga da ya tsara baza ku yi aure a yanzu dai da ita ba, and there is always a reason for everything da kaga ya faru a rayuwar nan kuma Allah kadae yasan dai dai, so who are we to question him? sai kaga kilan Allah ya sake hadaku da ita nan gaba a inda bakwa zato, kuma in har matarka ce ko nan da shekara nawa ne babu abinda zae hana ka aurenta, be patient for now pls Musharraf, do not rush things, gaggawa na shaidan ne, ita ma if u have access na contacting dinta ka kwantar mata da hankali kada all the 5 years she spent in school ya tafi a banza tayi asaransa, nursing science is not a joke, she needs to graduate and get her cert, don a yanzu karatu na daya daga cikin gatanta a rayuwar nan, duk da foster parent dinta really tried for her ita ma ya kamata ace tana da abinda zata taimaki kanta da shi nan gaba without being too dependant on any one, idan tana da rabon ganawa da danginta a duk inda suke zata gana da su komin daren dadewa, everything is just a matter of time, don haka kuyi hakuri gaba daya, tun da har ka iya hakuri da rashin mahaifinka da kanwarka in a motor accident wannan ma Allah zai sa maka hakuri har yayi maku abinda yafi alkhairi daga kai har ita yarinyar, find a way to access her ku yi magana ta fahimta da ita, ka kara kwantar mata da hankali, do not be a coward son...." A hankali Musharraf yace "Thank you Mami" Mami tace "Plss gobe ka dawo gida ina son ganinka ka ji" Yace "In sha Allah" Tace "To maa sha Allah, ka ci abinci?" Yace "Na ci" Tace "Toh sai da safe, plss kar ka sake kashe wayarka son" Yace "I won't" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Musharraf ya juya yana kallon Mayraah da ta rufe fuskarta da pillow, gaba daya jikinsa yayi sanyi da maganganun Mami, ya koma inda take ya zauna kusa da ita cikin sanyin murya yace "Baby" Mikewa zaune tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, nan da nan ta karyar masa da zuciya, he hate seeing her cry, cikin rawan murya tace "What Mami is saying is the truth, may be ba yanzu bane lokacin auren mu, kilan ba yanzu Allah ya rubuta za mu yi aure ba, dama tun kafin faruwan abubuwan nan ina ji a jikina kamar baza mu yi aure ba yanzu" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Kauda kai Musharraf yayi, bayan few seconds ya juyo ya kalleta.... Ta mike zaune tana share idonta tace "But i don't have anywhere to go to" Musharraf yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "I will keep on telling you not to be an ingrate, Ammi da Abba where the best of parent to you, basu taɓa failing dinki as parent ba, they raised u well, gave u quality education, protect you in whatever way they can, sun baki tarbiyyar da wasu dake tare da iyayen nasu ma basu samu ba, they gave u both Motherly and fatherly love, babu abinda kika rasa a rayuwar nan, ko da kika ji ina cewa mu je mu yi aure a wani wajen i don't have intentions of separating u from dem forever, komin daren dadewa za mu dawo, a yanzu nasan baza su taɓa bani aurenki ba bayan abubuwan nan da suka faru ni kuma zuciyata bazata iya jure hakan ba, you overheard our conversation with Mami, it won't be fair in bari 5 years dinki a university ya tafi a haka nan ba, kiyi hakuri baby, after ur final exams za mu je mu yi aurenmu, baza kuma mu dawo ba sai after u give me 2 beautiful kids like you" Kallonsa kawai Mayraah take, ya kamo hannunta a hankali yace "Yes dear, idan na tafi dake yanzu baki karasa karatun nan ba ban maki adalci ba cause zaki bukacesa a gaba it will be ur weapon against all odd in future" Hawaye na sauka idonta tace "A ina zan zauna in gama exams din?" Yayi kasa da murya yace "Gidanku, wajen Amminki da Abba" Ta kauda kai tana girgiza kai tace "Saboda ni ai bazai yiwu Ammi ta bijire ma mahaifiyarta ba, ta ce mata ta zabi ko ni ko ita, kaga bazan so abinda zai sa Ammi taki yi ma Hajja biyayya ba" Musharraf yace "Haka za kiyi hakuri ki zauna har ki gama exams din Mayraah, that doesn't mean ance ki bar gidan, Abba ma bazai yarda da haka ba, nasan Ammi ma komin me mahaifiyarta zata ce bazata so ki bar gidan ba bayan sun san baki da inda za ki, trust me Hajja doesn't mean all what she said duk da bansan me ya faru ba" Mayraah ta fashe da kuka ta kasa ce masa komai, cikin sanyin murya yace "Ki min alkawarin kuna gama final exams za mu tafi a daura mana aure Mayraah, ki min alkawarin baza ki canza ra'ayinki ba idan lokacin ya zo" Tana share idonta tace "Bazan canza ra'ayina ba sai in kai zaka canza naka, sai in kai ne zaka fasa aurena Sir" Yayi wani murmushi yace "The last thing i will do on earth is to deny u Mayraah, in kika ga ban aureki ba to bana numfashi ne, i am making you this promise" Wayarsa ne ya fara ring, duk suka juya suna kallon wayar, Maheer ne ke kira still, Musharraf ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallonta, ita dai sunkuyar da kanta tayi, Musharraf ya dauko wayar, da sauri ta rike hannunsa cikin rawan murya tace "Me zaka ce masa?" Calmly yace "I know what to tell him" Daga haka ya mike ya nufi kofa ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, bayan some minutes Musharraf ya dawo dakin yana kallonta, Sunkuyar da kanta tayi, a hankali yace "Tashi mu je Baby" Ƙin tashi tayi kuma bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita ya mika mata hannu, kauda kai tayi hawaye cike idonta ta sauko daga kan gadon tana kallonsa tace "What did u tell him?" Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "You know I won't tell him u are in my house, so no need to worry" A takaice tace "I won't be worried even if u should tell him that" Daga haka ta dau yoghurt din da ya ajiye mata ta sha kadan sannan ta nufi kofa da sauran, ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya sauke ajiyar zuciya, wayarta da ya ajiye a dakin ya daukar mata da magungunanta sannan ya dau makullin Motarsa ya fita, parlor ya sameta a tsaye, ya karaso inda take tsaye, ta kallesa tace "How comfortable are you in a dusty house?" Ya langwabar da kai yace "I was sick" Bata sake cewa komai ba, ya mika mata wayarta ta amsa sannan suka fita parlon, tana tsaye jikin motarsa bayan ya kunna to warm it up, ya zagayo inda take yana facing dinta yayi kasa da murya yace "I still want to remind u of how insecure i am with ur brothers Mayraah" Tana kallonsa a hankali tace "Insecure in what aspect?" Yace "Yanzu akwai aure tsakaninku" Da mamaki Mayraah tace "So u think ni zan iya auren daya daga cikin wa enda na taso nake ma kallon yayyina na jini? Mu yi aure da su as husband and wife or what? I don't understand" Tunanin hakan sai da yasa Mayraah ta fara jin wani sanyi na shigarta ta yaya ma hakan zai yiwu? How? tana girgiza kai tace "That's an abomination to me and them also" Matsawa tayi da sauri tana zaro ido ganin he is trying to lean on her, yayi hanzarin rikota onto him, tace "Meye haka?" Yayi kasa da murya yace "Not even a goodbye kiss Baby?" Kasa ce masa komai tayi, kawai wanda yayi mata ranan a gidansa ya fado mata, she wanted resisting this but he left her with no space for that..... Har suka bar unguwan Mayraah bata ce komai ba a motar, banda kamshin turarensa babu abinda ya cika mata hanci, kuma daga jikinta kamshin ke tashi, Bayan tafiyar kusan minti ashirin Mayraah ta gansu a area din makarantar su ya nemi waje yayi parking, still ita dai bata ce komai ba, ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido, bayan few minutes wayarsa ya fara ring, dauka yayi,
Chapter 76 · 0% Book details