Sashe 46
Mayrah Complete Hausa Novel · about 5 min read
Babu wanda ya rintsa a gidan Abba daren ranan nan, ga Ammi jini ya hau sosai, don she is under medication a gida har da karin ruwa, zuwa sannan duk kowa yasan an fasa auren Mayraah sannan Mayraah ba er gidan Abba da Ammi bace, wajen karfe takwas da rabi jama'a duk sunyi cirko cirko a parlor har da baƙin da suka zo daga nesa da wasu makotansu Ammi, kowa dai duk jiki a sanyaye, duk da ba bacci Ammi take ba amma idonta a rufe suke ita kadai tasan abinda take ji a wannan lokacin, gani take kamar shikenan bazata sake ganin Mayraah ba har abada, Mama Ladi ta fyace majina cikin rawan murya tace "Ni wllh nasan annamimiyar da ta hada wannan bam din aka shiga wannan rudanin a gidan nan...." Hajja dake zaune tayi tagumi a parlon ta juya tana kallon Mama ladi, rai bace Hajja tace "Amma dai nace maki ki iya bakin ki Ladi, wannan wace irin rayuwa ce baki da aiki sai hada hutsuma cikin jama'a? Tun cikin dare kin ishemu kinsan wanene kinsan wanene, to ke a garin kano kike da zaki hakikance kinsan wanene, haba don Allah ki bari mu ji da daya mana, wannan fa ba karamin magana bane kuma kina ji Mamuda yace sai yayi Shari'a da koma wanene yayi mana haka" Mama Ladi ta mike tace "Tun jiya zan yi magana kike hanani magana Hajja, to wallahi ni dai da iyayenmu suka haifeni kema kinsan ba munafuka bace ni, kuma babu ruwana da harkan munafurci, a cikin ku akwai warce nace ma Badiyya taje wajena har tayi kwanaki biyar?" Duk kowa yayi shiru yana kallon Mama Ladi har Hajja don kam bata gaya ma kowa ba, cike da mamaki Aunty Mariya tace "Taje yin me a wajenki Mama Ladi?" Mama Ladi tace "Wallahi ina zaman zamana sai ga shegiyar yarinyar nan Badiyya kamar an jefota karaye, yarinya ta zo ta giggilla min karya wai ana nuna banbanci tsakaninta da Mera don an ga bata da uwa bata da uba, duk kowa ya tsaneta har saurayin da ke nemanta da aure ance ya hakura ya nemi Mera kuma har ya hakura gashi an saka ranansa da Mera, sannan sau dari idan Mariya zata kira sai dai tace a ba Mera baza tace a ba Badiyya waya ba, ni ko da zuciya ta debeni nace wacece Mera? meran da bamu hada komai da ita ba babu dangin iya ba na baba ko dai ita Ammin da Hajjan sun mance ne, nan ko na kwashe duk yanda aka samo Mera na gaya ma Badiyya da zuciya daya ba da zuciya biyu ba, ban san da er iska munafuka nayi tadi ba" Mama Ladi na kai wa nan ta fashe da kuka tace "To yanzu zan fasa kwan nan a gaban kowa, wllh wllh Badiyya ce ta lalata maganar auren nan daga dai na bata labarin wacece Mera da zuciya daya" Ammi ta bude ido ta mike zaune tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, ita kanta Hajja kasa kwakkwaran motsi tayi tana kallon Mama Ladi, Aunty Mariya ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa kika mana haka Mama Ladi?" Bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana bin kowa da kallo kamar yanda duk aka yi still a parlon ana kallonta da shock, Mayraah ta nufi Ammi da gudu hankalinta tashe ganin drip a hannunta tace "Ammi... saboda ni ne?" Mama Ladi ta rushe da kuka tace "To da saboda waye? Banda mun sa ma kanmu salama ai har mu da sai kin ganmu da karin ruwan a hannu, Dama nace masu babu inda zaki je dole ki dawo garemu ko da bamu hada komai da ke ba, ko don halaccin da muka maki ai kya dawo, To idan ba jiya ba ke kin taɓa sanin cewar ba Ammi da Mamuda bane suka haifeki? Ko a bakin wanin mu kin taɓa ji? Kinga ai basu taɓa nuna maki banbanci tsakaninki da ainahin yaran da suka haifa a cikinsu ba, kuma soyayyar da suke maki yasa suka boye ma duniya ba su ne asalin iyayenki na gaskiya ba mu ma kuma muka ja bakinmu muka yi shiru muka taya su rufa wannan asirin banda yanzu da asirin ya tonu, amma gata kam ai babu irin wanda baki samu ba a wajensu Mera, da yawa wa enda ke gun iyayensu na asali ma basu samu gatanki ba wllh, ko su Maheer da suka haifa basu samu haka ba magana ta gaskiya, to don me baza kiyi la'akari da wannan ba zaki gudu ki bar mu cikin tashin hankali ki tauye mana baccinmu jiya, yanda muka ga rana haka fa muka ga dare, kuma da kika kama hanya kika gudu ina zaki je? Ke da baki da dangin uwa balle na uba" Mayraah da ko karasawa gun Ammin bata yi ba ta tsaya tana sauraron abinda Mama Ladi ke gaya mata babu ko kiftawa, lokaci daya ta dinga ganin parlon na juya mata ta dinga kallon Mama Ladi da ta dawo mata double double a ido, Ammi ta kasa daurewa ta hade kanta da kujera tana kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi, Aunty Mariya ma kukan take don su duk tunaninsu Mayraah tasan asalin me ke faruwa daga bakin Musharraf, dalilin da yasa ta bar gida kenan jiya, Mama Ladi ta sharce majina tace "A nan bakin wani masallaci a cikin garin Yola aka yasar da ke ko cibiyarki bai fadi ba, a lokacin Mamuda na fama da baƙin talauci ya fito zai share masallaci ya jido ruwa kafin a fara fitowa sallan asuba ya ganki cikin yakunannen tsumma uwarki ta wurgar da ke ta kara gaba" Tsawa Hajja ta daka ma Mama Ladi ta mike tana huci tace "Ke mahaukaciyar wace gari ce Ladi?? maza dauko rubabben akwatinki ki kama hanya ki koma karaye tun raina bai gama baci ba...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba suka ga Mayraah ta sulale nan kasa, dai dai shigowar Usman parlon yayi saurin karasawa inda ta fadi, tsabar rikicewa Ammi mance drip din hannunta tayi ta mike tayi kan Mayraah a guje, sauran mutanen parlon ma duk suka nufi Mayraah suna salati, Mama Ladi dai sai gwaggwale ido take a inda take tsaye.....
Still on todays discount for the book Mayraah, pay 300 Naira into
👇🏻
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Still on todays discount for the book Mayraah, pay 300 Naira into
👇🏻
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788