← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 145

Sashe 79

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayraah na zaune kan darduma tun bayan da ta idar da sallahn isha bata tashi wajen ba tayi nisa tunanin da take ta ji an bude kofar dakin, da sauri ta juya tana kallon kofar, Maheer ya shigo da sallama rike da plate da ledan takeaway din abinci a hannunsa, karasawa yayi kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan ya ciro takeaway din ciki sannan ya juye a plate, ya daga kai suka hada ido ya sakar mata murmushi yace "Ur favorite" Ta sauke idonta tace "Thank you" Yace "Kinyi wankan?" Ta gyada masa kai, ya mike yace "Ohk bari in saka maki kayanki a press kafin ki gama cin abincin" Yana fadin haka ya mike ya nufi akwatunanta guda uku dake dakin ya bude guda daya, ta maida dubanta kan abincin gabanta ta fara ci a hankali, Absentmindedly take cin abincin da ko taste dinsa bata ji a bakinta, bayan wani lokaci ta juya taga ya bude wani akwatin with her inners inside, da sauri ta ajiye spoon din hannunta tace "Aa, ka bar min wannan zan yi da kaina" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" maida akwatin yayi ya bude wani, ta ci gaba da cin abincinta, har ya gama jera mata duk kayan a press ko quarter din shinkafar bata iya ta ci ba, ya dawo kusa da ita yace "You are not eating Mimi, ko baki son shinkafan ne yau?" A hankali ta matsar da plate din tace "Na koshi" Yace "Ko in kawo maki Milo?" Ta girgiza masa kai tace "I am full" ya dau ledan maganin da Dr Musharraf ya siya mata ya fiddo su yana duba su, ita dai kallonsa kawai take, after examining the drugs ya ballar mata su ya mika mata yace "Take" ta mika hannu ta amsa sannan ta sha da ruwan goran dake gefenta, yace "Tunda baza ki ci abincin ba ni bani in ci" Daukan plate din tayi ta mika masa ya amsa, ta mike ta shiga bandaki zata wanke bakinta, Maheer ya juya yana kallon gefensa, Hijab dinta ya tsura ma ido for few seconds, can ya dauka ya kai hanci yana perceiving din scent din Hijab din, dai dai nan ta fito tana cewa "Yaya babu toothpaste a ciki" Shiru tayi tana kallonsa, ya ajiye hijab din da sauru yace "Oh ok bari in dauko maki yanzu" Yana fadin haka ya ajiye plate din hannunsa ya mike ya fita daga dakin, Mayraah ta karasa bakin gadon ta dau Hijab din nata ta kai hanci ita ma, ajiyewa tayi ta sauke idonta kasa ta juya a hankali ta koma inda take tsaye, can kuma ta sake komawa gun Hijab din ta dauka ta shiga bandaki ta saka a bucket ta zazzaga detergent dake cikin bandakin ta bude pampo, yana dawowa dakin ya kwankwasa mata bathroom din, ta bude kofar ta amshi toothpaste din sannan ta kulle, juyawa yayi ya dau abincin da ta bari ya fita daga dakin, Mayraah ta gama wanke bakinta ta dauro alwala ta fito, kwanciya tayi gefen gadon ta lumshe ido after so many thought that ran through her mind bacci ya dauketa, Wajen karfe goma Maheer ya shigo dakin, ya karaso kan gadon yana kallonta yace "Kinyi alwala kafin ki kwanta Mimi?" Kai kawai ta gyada masa idonta a lumshe, yace "To gyara kwanciyarki" Ta koma middle of d bed ta kwanta, ya rufa mata duvet yace "Don't forget to pray" Ta gyada masa kai, ya rage AC, ya kashe wutan dakin gaba daya sannan ya fita ya kullo mata kofar. Washegari da asuba Maheer zai tafi masallaci ya shigo dakin don tada ta, bai yi mamakin ganin ta tashi ba don a gida karfe biyar take tashi dama, ya fita zuwa masallaci, Mayraah na idar da sallah ta koma ta kwanta, for the past 4 days sai jiya tayi bacci sosai da daddare yanzun ma kuma wani baccin take ji kilan har da maganin bacci a magungunan da Musharraf ya bata, karfe takwas da kusan rabi ta farka, da sauri ta mike bayan ta tuna ai zata school yau, ta shiga bandaki don yin wanka, kafin tara da rabi har ta gama shiryawa, ta zauna gefen gado tayi jim tana bin dakin da kallo, babu abinda babu ciki, and it look beautiful, can dai ganin lokaci na wucewa kuma karfe goma take da lectures ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali, main parlor ta shigo, ta dinga bin parlon da kallo, sosai parlon ma ya hadu yayi kyau, cream with touch of gold ne yawancin abubuwan parlon, ta kalli hanyar kitchen sannan ta nufi can, tana bude kofar ta gansa tsaye yana peeling Irish, ya juya yana kallonta yace "Good morning Mimi" A hankali tace "Good morning Yaya" Yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin yi bacci sosai?" Ta gyada masa kai, yace "That's great" Karasawa tayi cikin kitchen din tace "Kawo in fere" Yace "Aa ke da baki da lafiya, kawai kije kiyi kwanciyarki i will serve u breakfast in bed...." Ɗan murmushi tayi wanda iyakarsa lips dinta tace "Ni dai ka kawo inyi zaka bata min lokaci" Juyawa yayi yana kallonta yace "Yunwa kike ji ne?" Ta girgiza kai tace "Aa, zan je school" Shiru yayi sai kuma yace "No Mimi, ki bari zuwa Wednesday, kin ga u are just recovering, kar ki yi stressing kanki" Tace "Pls ina son inje, I've missed a lot, and our exams is in 4 weeks time" bata jira me zai ce ba ta amshi peeler din a hannunsa ya sake mata ya koma gefe yana kallonta, ta fara fere irish din, juyawa yayi ya fita daga kitchen din, before 10:15 har ta gama ta soya kwai ta dafa ruwan shayi ta fito parlor da fried Irish and egg din, ganin baya parlon ta kai masa dinning ta ajiye sannan ta ja kujera ta zauna tana jiran shayinta ya huce, sai gashi ya shigo parlon, dinning area din ya karasa yana kallon plate din irish dinta wanda bai wuce kwaya biyar ba da karamin kwai a gefe yace "Meye wannan din Mimi?" Ta daga kai tana kallonsa, daukan plate din yayi ya juye abincin nata a nasa sannan ya kai middle of the parlor ya ajiye, ya koma ya dauko shayinta da nasa ya ajiye a parlon ya zauna yana kallonta yace "Dawo nan mu ci" Ta marairaice tana kallonsa, can ta kalli agogo ganin she is wasting her time ta mike ta tafi parlon ta xauna gefensa ta fara cin irish din, haka nan yayi forcing dinta sai da ta ci da ɗan yawa ta sha shayinta, 10:40 ya tafi da ita school din a motarsa.... Gaban department dinsu yayi parking yana kallonta yace "Yaushe za ku gama lectures?" Tace "4pm" yace "Ohk i will be here by 4" Tana kallonsa tace "Aa kawai zan samu me adaidaita sahu Yaya" Yace "Aa for today zan dawo in dauke ki" kudi ya ciro a aljihunsa yace "In case zaki ci abinci a cafeteria" Ta girgiza kai tace "Bazan ci komai ba" Yace "To amshi dai" karban kudin tayi tace "Nagode" Yayi mata sallama ya bar wajen, shiga department din tayi, tasan yanxu duk an shiga lectures, kawai ta tafi inda suke sallah ta zauna, shiru shiru ita dai bata ga shigowar Dr Musharraf ba har kusan 12, lokaci daya mood dinta ya canza gashi bata fito da waya ba balle ta kirasa, sai ga Coursemates dinta sun fara fitowa daga lecture hall, Hamidah na ganinta ta nufota da sauri tace "Lahh Mayraah, ashe kin shigo" Mayraah ta mata murmushi tace "Eh na shigo, Ya lectures din?" Hamida ta zauna gefenta tace "Alhamdulillah, na ma rubuta maki attendance, to me yasa baki shigo hall ba" Mayraah tace "Na ga time ya wuce ne shi yasa" Hamidah ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in nuna maki note din da muka yi, ya su Ammi?" Mayraah ta sauke idonta kasa tace "Suna nan lafiya" Da alama Hamidah bata son kawo ma Mayraah maganan aurenta da aka fasa shi yasa take ta kame kamen nuna mata note, ta ciro notes dinta ta mika ma Mayraah tace "Iyakar abinda muka yi kenan, nasan a yau duk za ki karance" Mayraah tayi murmushi ta amsa tana dubawa, nan sauran Coursemates dinsu suka nufo su ganin Mayraah, duk aka gaggaisa, babu dai wanda ya kawo mata zancen fasa aurenta, har suka shiga second lectures din ranan Mayraah bata da wani walwala balle sukuni, bata taɓa tunanin bazata ga Dr Musharraf a school ba yau, but he told her he will be coming, he didn't keep to his words, a haka dai suka gama lectures din wajen karfe hudu suka fito, sai da suka yi la'asar sannan Mayraah suka fito department din tare da Hamidah, Motar Maheer ta gani a inda ya tsaya da safe, Tana kallon Hamidah tace "Ya Maheer ya zo zai daukeni, mu je sai mu rage maki hanya" Hamida tace "Ai ko nagode" Tare suka tafi gun motar, Mayraah ta bude front seat, Hamidah ta shiga baya, bayan ta zauna ta gaida Maheer, ya amsa da fara'a yace "Ya lectures Hamidah?" Tace "Alhamdulillah" yace "How is preparation for exams?" Tace "Muna ta yi" Yace "To Allah ya baku nasara" Hamidah tace "Ameen mun gode" Mayraah ta kallesa ta gaishesa, ya amsa sannan suka bar gun, dai dai inda Hamidah zata samu adaidaita sahun anguwansu Maheer ya ajiyeta, ya bata 2k kudin ɗan sahu sannan ya kama hanyar gida tare da Mayraah, sai da ya fara tsayawa a hanya yayi masu takeaway din abinci sannan suka karasa gida.... Yana parking a parking space Mayraah ta dau ledan takeaway din ta bude motar ta sauka, shi ma ya sauka, yana kallonta yace "Haseenah is back" Sosai gabanta ya fadi sai dai bata ce komai ba, yace "Mu je mana" Ta fara tafiya ya bi bayanta har suka iso kofar parlon, ta bude kofar ta shiga da sallaman da tayi a ranta, Haseenah na zaune parlorn ta cakare dankwaki a kan doguwar rigar jikinta tana taunar cingam, tun da ta ji shigowar motar Maheer ta fito parlon ta zauna dama, Suna hada ido Mayraah tace "Ina wuni" Haseenah ta kalli Maheer dake bayan Mayraah a
Chapter 79 · 0% Book details