Sashe 92
Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Ammi ta bada a kawo mata, pepper soup din kaza ne da yaji kayan hadi, nan da nan aroma din ya cika dakin, tashi tayi ta saka hijab dinta ta nufi kofa, ta bude a hankali ta fita, zaune ta ga Maheer a parlor shi kadai, ta karasa kitchen ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo, plate da spoon ta dauka zata koma daki nan ma ya bi ta da ido, Mayraah ta debar masa rabin pepper soup din ta kai masa parlon, yana kallon plate din yace "Shi ya siya maki?" Tace "Aa Ammi ce ta bashi ya kawo min" Amsa yayi yace "Ni da Haseenah?" Mayraah bata san sanda ta amshe plate din daga hannunsa ba tayi juyawarta ta koma daki ta rufe kofa, ya bi ta da kallon mamaki, bayan few seconds ya mike ya bi bayanta, Mayraah na kokarin juye naman cikin food warmer din ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take, ya ɗan sosa kai yace "Ok i am sorry, i was only asking Mimi ai ban sani ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ni kadai aka kawo ma dama ae" Yace "Ohk then" juyawa yayi zai fita, ta daga kai tana kallonsa, a hankali tace "To zan tsam maka amma a nan" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" Ta sa masa naman guda hudu a plate ta mike ta kai masa, amsa yayi yana kallonta yace "In je parlor da shi?" Ta ɗan yi shiru sai kuma ta juya tace "Ohk" Yace "Thanks Mimi, good night" Fita yayi daga dakin, ta koma ta debi wanda zata ci, bata wani ci naman da yawa ba, ta ci shawarman da Usman ya siya mata sannan ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta fito, ta kwanta kenan kiran Musharraf ya shigo wayarta dake gefenta, ta dinga kallon call din kafin ta daga ta kai kunne tayi shiru, Musharraf yace "Na maki laifi ne Dear?" Tace "Laifi kuma na me?" Shiru yayi, ita ma haka, can yace "Kiyi hakuri, in ma na bata maki rai unknowingly, may be i should have gotten the food for u my self, i am sorry Mayraah" lokaci daya ta ji jikinta yayi sanyi, yace "Dama kira kawai nayi in baki hakuri, sae da safe" kasa ce masa komai tayi har ta ji ya katse wayar, a hankali ta rufe idonta tana karanto addu'ar bacci, sannan ta ajiye wayar a bedside drawer ta rufa da duvet, amma for almost an hour ta kasa bacci sae juye juye take, daga karshe ta jawo wayar tayi dialing numbersa, yana dagawa a hankali tayi karfin halin cewa "I am.... I'm sorry too" Har kusan karfe biyun dare Mayraah bata kwanta ba kuma babu alamar bacci ko kiris a idonta, yau kam sun yi hira sosai da Musharraf a waya, they talk about so many things, basu taɓa dadewa a waya irin yau ba tun fara dating dinsu, she is just realizing Musharraf is different in many ways, kawai suna tare ne amma bata san abubuwa da yawa game da shi ba sai yau da yake gaya mata, he told her how he lost his father and his sister that was 13 years old in a car accident, how he cherish his Mami soo much, he gist her about his group of frnds da irin rayuwar da suka yi a kasan waje sanda suke karatu... har labarin Farrah da aka so hada shi da a family sai da ya bata, Mayraah enjoyed every bit of their conversation that night, wani taji tausayinsa, wani taji haushinsa, wani kuma ya bata dariya, wani ya bata mamaki, at the end yace "But trust me Mayraah, no matter who my frnds are back then, Billah ban taɓa zina ba, even this common kiss ni ban taɓa yi ma ko wace mace ba sai ke, i will gain nothing if i lie to you, ni ina da kyankyami sosai shi yasa sai in ji mace bata burgeni ko inji feelings na mace, but surprisingly that stop immediately after i met u, bayan ke kuma ni bana yi ma ko wacce mace kallon sha'awa, Alcohol kuma the weather in Canada lured me and some of our friends into taking it, muna fatan Allah ya yafe mana, mind you... har ma da peer pressure, though ni dai na sha wahala sosai kafin in saba da weather din Canada, amma billah tun bayan dawowata Naija na daina shan alcohol Mayraah, back in Canada ma sai inyi many weeks ban sha ba sai in na gani gun abokan mu, many of my friends basu daina ba har yau, i don't know what came over me da har na sha ranan da daddare a zaria, may be it's because i was loosing my self, Mami bata taɓa sanina da alcohol ba har yau...." Mayraah dai tayi shiru tana sauraronsa, Bayan few seconds yace "Now tell me how u felt the first day we met" Murmushi Mayraah tayi ta kasa ce masa komai, can dai tace "Some other time" Yace "Ohk, ina son kuma zan tambayeki...." Tace "Ina ji" Yace "I tot u once told me Badiyyah er gidanku ce or so" Tace "Sure...." Yace "But da safe da ta shigo office naga kun yi kamar baku san juna ba, why?" Mayraah tace "Ai mun riga mun gaisa da ita a downstairs... And wajenka ta zo a office ba wajena ba" Dr Musharraf yace "Ohkk then, it's already late, ki kwanta.... ni zan yi sallah" a hankali Mayraah tace "Ohk" yayi kasa da murya yace "Sleep tight my love..." tace "Thank you..." Daga haka ya katse wayar Mayraah ta lumshe ido. Washegari har karfe takwas Mayraah bata tashi ba don bazata school yau ba tunda Dr Musharraf yace mata bazai je ba, dama kuma friday ne, tana tashi wajen takwas da rabi ta ga miss calls din Ammi tun 5am, kiranta tayi yana fara ring Ammi ta daga, sun kusa 15 minutes suna magana da Ammi daga karshe suka yi sallama, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki, wanke baki tayi, tayi wanka sannan ta fito... Bayan ta gama shiryawa wajen goma saura taji anyi knocking din kofar dakinta, ta mike ta isa bakin kofar ta bude a hankali, Maheer ta gani tsaye, yana kallonta with smile on his face yace "Good morning Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" Yace "Yau baza ki school ba?" Tace "Eh" Yace "Ohk, fito ki debi breakfast" juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor ta bi bayansa tana tafiya a hankali, zaune ta tadda Haseenah a parlor ga breakfast din da tayi ma Maheer a tsakar parlon tana kokarin hada masa shayi tana cewa "Baby special tea fa na dafa maka yau, bana jin ka taɓa shan irinsa wllh" ya zauna kan kujera yace "Really" Tayi er dariya tace "Sai ka dandana zaka gane..." Kamar ance ta daga kai taga Mayraah a parlon, nan da nan ta hade rai sosai, Maheer yace "A ina kika koyi dafa shayin?" Banza tayi masa tana saka cube din sugar a shayin, ya kalli Mayraah yace "Zauna mana Mimi" ta zauna edge din kujera tana kallon Haseenah tace "Ina kwana" Ciki ciki Haseenah ta amsa fuskarta a murtuke kamar hadari, Maheer ya sauka daga kan kujeran ya zauna kan carpet ya dau plate ya debar ma Mayraah irish din da kwai, sannan ya hada mata shayi me ƙauri, yace "Amma lectures ne baku da shi yau ko dai kawai zuwa school din ne baza ki yi ba Mimi" Mayraah tace "Kawai bazan je ba" Yace "Ohk sai kiyi karatu a gida, sauko kiyi breakfast" Mikewa Haseenah tayi fuuu ta wuce daki kamar zata tashi sama, Mayraah dai ta sauko kasa Maheer ya ajiye mata breakfast din a gabanta sannan ya fara hada nasa shayin da Haseenah ta bari, bayan ya gama hada shayin yace "Let me get my phone" Daga haka ya mike ya bi bayan Haseenah zuwa daki, Mayraah ta kyabe baki ta mike ta dau breakfast din ta kai daki ta ajiye sannan ta dau warmer din farfesunta na jiya ta tafi kitchen tayi warming, Maheer na shiga dakin ya kullo kofa yana kallon Haseenah cikin kwantar da murya yace "Me yasa kika taso Haseenah?" A mugun fusace tace "Bazan taso ba? Ta yaya zan sha wahala in tashi da asuban fari in mana girki ka debar ma yarinyar dake kwance tana bacci tun jiya da daddare?? Ko na ce maka ciki uku nayi ma breakfast din? It's just for me and you don ma kaji in gaya maka, Idan ba ma rainin wayo ba tsabar ka daure mata kugun ta raina ni yanda ta ga dama ta yaya ita bata tashi ta nema mana breakfast ba ni zan yi kuma ka debar mata?? Maheer tell me who does that??" Maheer yace "Amma fa jiya da na maki magana ce min kika yi kin fi so kiyi girkinki da kanki" Cikin daga murya tace "Toh sai nace maka har da ita zan yi ma girkin ko ita kuturwa ce da bazata nemi abinda zata ci ba a gidan? Maheer wllh na gaji da wannan walakancin daga yau na daina dauka sai dai duk abinda zai faru ya faru" Maheer yace "Ki daina daga min murya haka Haseenah, i am being patient all this days amma u are trying to push me to the wall" Ta mike tsaye tana huci kamar zata bangajesa tace "Har outside of the wall zanyi pushing dinka babu abinda ya sha min kai, wllh a duk duniya babu macen da zata dauki wannan abinda ake min in za a cire son zuciya, meyasa zan tashi da sassafe yarinya na bacci inyi wahala inyi breakfast ko bakina ban kai ba balle kai da nayi ma ka ci, zaka wani cika ma yarinya plate ka kwashi kwai ka lafta mata??? Duka duka irish din guda nawa na soya har zaka kwashe ka cika mata plate? Ko ita ta soya min??" Calmly Maheer yace "Toh ni bazan ci ba, ki cinye sauran tunda ba shi da yawa idan naje office zan nemi abinda zan ci, and you know