← Book details Mayrah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 145

Sashe 120

Mayrah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Badiyyah da sauri tana bata instruction din ta tashi tsaye cikin tsawa, tuni sauran lecturers din maza dake Hall din suma suka nufo Badiyyah, Badiyyah dake ta zazzare ido tayi kasa da hannunta ta cukuikuye wani takarda ta jefar kusa da Mayraah, Mayraah ta zaro ido tana kallonta a tsorace, tuni lecturers din suka zagaye seat dun Badiyyah, a tsakiyan Booklet dinta suka ciro papers cike da rubutu an linkesu neatly, Badiyyah ta fashe da kuka a tsorace tana nuna Mayraah cikin rawan murya tace "Wallahi ba ni kadai bace har da ita, we were passing answers to each other wllh tllh" Lecturers din suka kalli Mayraah da ta zaro ido, wani ya karasa kusa da ita ya durkusa ya dau takardan da ya gani yana instructing din Mayraah ta tashi tsaye, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah ta ma rasa abinda zata ce tsabar rikicewa, lecturer din ya warware takardan da Badiyyah ta jefa mata yana dubawa, tuni wani lecturer har ya yage envelope din mal-practice form jikinsa na rawa ya ciro biyu ya ajiye daya kan table din Mayraah, dayan kuma kan table din Badiyyah, wani student dake zaune bayan Mayraah ya daga hannu alamar zai yi magana yace "Wallahi sir jefo ma Mayraah takardan kawai tayi da taga an kamata, amma they are not together sir" Sai a sannan Mayraah ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Sir u can check d paper and my answer booklet if they correlate, wallahi i am not together with her" Wata security lady da ta ta karaso cikin Hall din ne tace "Malam naga fa duk abinda ya faru, ita wancan matar me satan amsan ce ta jefo ma yarinyar nan takardan nan da ta ga an kamata, i saw everything from outside.... Tun dazu nake noticing tana mutsu mutsu but i want to be sure with what she is doing first, sai gashi Malama ta kama ta, tun fara exams din nake mata kallon mara gaskiya shi yasa ban bar wajen da na tsaya ba" Still lecturer din bai yarda ba sai da ya bude booklet din Mayraah ya duba abinda tayi da wanda ke cikin takardan yaga babu hadi, sannan ya dauke mal-practice form din daga kan table dinta, Kuka kawai Badiyyah take don gaba daya an zagayeta sai ta cika Mal-practice form amma taki yarda ta cika, can dai ta daidaici kofa ta kwasa a guje kamar barauniya ta bar class din, Lecturer din da ta kamata ta dau pen ta cike mata form din don har ID card dinta na kan table ta bar shi, kowa a class din jikinsa yayi mugun sanyi da abinda ya faru, Mayraah ta ji gaba daya komai yayi Vaporizing daga kanta tsabar tashin hankali, har sannan jikinta bai daina rawa ba, Lecturers din suka ci gaba da invigilating dinsu bayan an cike ma Badiyyah mal-practice form kamar babu abinda ya faru, ba Mayraah kadai ba a lot of student sun kasa ci gaba da rubutun exams din barin kawayen Badiyyah, shkkn fa 5 years dinta ya tafi a banza kenan, don in dai aka bude sealed envelope din mal-practice form to magana ta kare kuma, Daga karshe Mayraah ta mike kawai don bata san kuma me zata rubuta ba ta tafi tayi submitting tayi sign out ta fita daga class din, har ta isa gida bata daina hawayen da take ba, don tasan da ba don wannan Coursemate din nasu dake bayanta da Security woman din nan ba Lecturers din nan ko me zata ce baza su taɓa sauraronta ba don marasu mutunci aka hada a class din dama, tana isa hostel ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya... Badiyyah na isa gidan Maheer bata ko kalli Haseenah da cousin dinta Ramlah dake zaune Parlon ba ta shige dakinta jikinta na rawa, ko handbag dinta bata dauko a exam hall din ba, don ma Allah ya rufa mata asiri yau bata kulle dakin nata da makulli ba tunda ba wani abun da zata boye a dakin, turamen atamfar da ga sato cikin akwatin lefen Haseenah dama har ta kai ma tailor dinta ya dinka mata, zaunawa tayi gefen gado tana share zufar da ke ƙeto mata har sannan gabanta bai daina faduwa ba, can ta kwanta ta lullube da bargo ta rufe idonta don har wani mugun sanyi take ji, ko tuna abinda ya faru bata son yi, gani take tunda har ta gudu bata cike form din ba to shikenan ta tsira, kuma fa Malamin nan yace lafiya zata gama exams har ma tayi passing duk courses din, to ya haka? Ya aka yi aka kamata bayan sai da yace baza a kamata ba ko da textbook zata shiga Hall din, taga dai kwanciyar nan baxae kara mata komai ba ta mike ta fito parlor, kilan in ta gaya ma Haseenah abinda ya faru zata fi samun sauki a ranta har a samo mata solution, Haseenah na ganin fitowarta tayi shiru, haka ma cousin sis dinta Ramlah, Badiyyah ta zauna gefen kujera har sannan gabanta na faduwa ta marairaice tace "Haseenah an kama ni da expo a school" Haseenah ta dafe kirjinta ta juya da sauri ta gwalo ido tana kallonta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, final exam din?? Garin yaya haka ya faru Badiyyah, ba kin ce min Musharraf din na baki Area of concentration ba?" Badiyyah ta fashe da matsanancin kukan tashin hankali tace "Wallahi an kama ni yau Haseenah" Haseenah ta gyara zama tace "Musharraf din na hall din kuma?" Cikin kuka Badiyyah tace "He is not among our invigilators today, Haseenah don Allah ki rufa min asiri ki gaya min ya zan yi? 5 years fa Haseenah" Haseenah tace "kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ga shi makarantar nan naku basu da mutunci har Allah Allah suke su kama mutum da mal-practice don a basu buhun shinkafa da man gyada, yanzu form din suka ciro a envelope suka baki?" Badiyyah ta silalo kasa tana rusa kuka tace "Don Allah ki taimakeni Haseenah, wallahi ji nake kamar zan mutu, ban taɓa shiga tashin hankali irin yau ba, ki gaya min yanda zan yi don girman Allah Haseenah" Ramlah dake sauraronsu ita ma cike da mamaki ta gyada kai tace "Tabdi, ae in dai jami'a ce to kinyi asaran shekaru 5 din nan wllh, babu wani abinda za a iya yi in dai dumu dumu aka kama ki" Haseenah tace "Gashi she is almost 33 yanzu fa Ramlah balle a sa ran zata fara daga farko, sau uku ana koranta a University fa, wannan duk mun sa rai zata yi graduating da muka ga ta kai level 500, duk fa mate dinta masters garemu yanzu" Badiyyah ta marairaice tana kuka tace "Ni dae ko Malamin nan naki zan kira in gaya masa abinda ke faruwa ko da abinda zai iya yi min" Haseenah ta zaro ido tace "Wani malami na? Ni kin taɓa ganin nayi harka da Malami Badiyyah? Ai bana harka da malamai, ban taɓa ba wallahi, to albishirinki dama don naga kwana biyu kina wani daɗɗaga min kai a gidan nan ne yasa na fita harkanki na kyale ki, wallahi kawata ta kirani tace ince maki ki fita sabgar malamin nan da ta hadaki ɗa shi ashe mayaudari ne ba malami bane, ya damfari jama'a ya gudu da kudadensu ya bar Zaria...." Badiyyah tace "Mutumin da yayi min aiki na kuma ga aikin yayi ne za ace ma mayaudari? Kinsan yanda muka fara zama close da Dr Musharraf kuwa yanzu duk sbda aikin da Malamin nan yayi min? To ke abinda baki sani ba last week da nace zan je Bichi da na samu intervals after our 4th paper a school, to Zaria naje wajen Malamin don ma ki ji in gaya maki" Sosai gaban Haseenah ya fadi, a ranta tace shikenan ta banu ta lalace, ynxu Badiyyah taje har gun malaminta kenan a Zaria, Badiyyah ta wani kyabe baki tace "Kuma kallonki kawai nake xaki wani ce min malamin kawarki ne bayan ashe malamin ki ne da shi kike harka, to har hotonki na nuna masa kuma yace min ae ke loyal costumer dinsa ce, yace min kun fi shekara bakwai tare yana maki aiki" Haseenah ji tayi kamar kasa ya bude ta shige tsabar yanda ta gigice har hakan bai boyu ba a fuskarta sai zare ido take, Ramlah dae ta kyabe baki tana kallon Haseenah irin maganinta kenan, Badiyya tace "To ni duk ba wannan ne a gabana ba, bari kawai inje in kirasa kar lokaci ya kure in shiga uku, don in har aka kore ni a makaranta komai zai iya faruwa da ni wllh, har fa Dr Musharraf yace min zai min hanyar samun aiki a babban asibiti as a Qualified Nurse, kafin nan ni kuma nasan duk yanda na bi muka yi aure, kuma yace min fa har kasan waje za a iya daukata aiki" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta mike ta wuce daki ta kulle kofa, Haseenah ta daura hannu a ka tana kallon Ramlah tace "Na shiga uku na lalace Ramlah, ban san iyakan me Malam Dauda ya gaya mata ba akan alakata da shi, na shiga uku na lalace" Ramlah na hararanta tace "Ba dai ke bakinki bai tsayawa waje daya ba komai sae kin yi surutu, maganinki kenan wallahi"
Chapter 120 · 0% Book details