Sashe 107
Mayrah Complete Hausa Novel · about 5 min read
zan auri Mimi in samar mata gidan da zata zauna to bring an end to all this...." Juyawa Ammi tayi da sauri tana kallonsa kamar yanda Usman ma ya daga kai yana kallonsa, Ammi na kallonsa da kyau tayi wani murmushi tace "Ba da yawuna ba, in kuma gaban kanka zaka yi i assure u baxa ka taɓa ganin dai dai ba..." Juyawa Usman yayi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Mayraah na zaune parlor kanta a kasa duk tana jin abubuwan da ake yi a dakin, banda murmushi babu abinda Haseenah take tana kallon Mayraah kasa kasa dom everything was clear kamar a gabansu ake yi, Mama Ladi dake rusa kuka ta mike tana kallon Maheer tace "Kawai ta hado kayanta mu tafi karaye Mashir, dama ka taɓa ganin inda barewa tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe??" Bata jira amsarsa ba ta fice daga dakin ta koma parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi maza ki tattaro kayanki" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Mama Ladi da manyan idanuwanta, cikin daga murya Mama Ladi tace "Baza ki tashi ba sai kin ga tana watsar maki da kayanki titi" Mayraah ta mike tsaye, Mama Ladi tace "Fita mu je, ai naga akwai sauran kayanki a gidan nan tattaro su gaba daya kawai ki zuba a akwatina" bin bayan Mama Ladi Mayraah tayi suka fita daga parlon zuwa dakinta, Mama Ladi ta bude inda sauran kayan Mayraah suke ta dinga kwasowa tana zubawa a akwatinta, ita dai Mayraah na tsaye tana kallonta kamar statue, Maheer ya shigo dakin looking so weakened and confused, Mama Ladi ta dago bayan ta gama cusa kayan a akwatin tana kallon Mayraah tace "Shikenan abinda zaki bukata kin wani tsaya kamar gunki kina kallona, ko baki ji abinda ke faruwa a gidan bane" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kallonta take, it seems like it's taking her too long to absorb the reality of what is happening, Maheer na kallon Mama Ladi a hankali yace "Tana da jarabawan da zata yi Mama" Yana fadin haka ya karasa ya kama hannun Mayraah suka fita daga dakin kawai, ita dai bin sa kawai take har suka sauka downstairs, Balcony ya fita da ita ya sa ta zauna, shi ma ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ganin abubuwan yake kamar a mafarki ya rasa wani tunanin zai yi, ita dai Mayraah kallonsa kawai take, can ya dago ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya kama hannunta yace "Mimi" sauke idonta tayi ta amsa, yaji wani tausayinta har cikin ransa, seeing her dry eyes ne ya kara daga masa hankali don yasan taji duk furucin Ammi tunda kofar dakin a bude yake ya kuma san ita din me saurin kuka ce amma ynxu bbu ko digon hawayen a idonta.... Haseenah bata taɓa shiga farin ciki irin na yau ba ko aurenta da Maheer bata ji irin wnn mugun farin cikin ba, gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune a part din Ammi don murna, babu kowa sai ita kadai a part din, aka bude kofar Parlon juyawa tayi da sauri ganin Abba ta sauko kasa tana sinne kai tace "Ina kwana Abba" a takaice ya amsa ya nufi dakin Ammi ya bude yaga babu kowa a ciki, fitowa yayi daga part din ya sauko downstairs ya tadda Ammi zaune a parlon fuskarta a murtuke, Abba na nunata da yatsa cikin bacin rai yace "Ke Hajarah, naga kamar baku san kawaici ba daga ke har mutanen ki, all this while ina ta bin ku a yanda ku ke so don kawai a zauna lafiya, to kun kai ni bango kuma yanzu i am not going to tolerate this nonsense any more, babu wanda ya isa ya gaya min yanda zanyi ko yanda bazan yi ba a gidana, it's my house not anybody's...." Ammi ta dakatar da shi tace "Ohh zagina da iyayena zaka yi akan Mayraah? No tell me zagina da iyayena zaka yi? Naga dai ba wani ya bani shawaran ince zan raini yarinyar nan har zuwa yau ba ko, ba kuma wani ya tursasa ni in riketa ba, sannan kai har kana da bakin magana yanzu? ka mance dauki ba dadin da muka yi da kai a kanta tana jaririya?" Abba yace "Duk wannan ke ta shafa, kuma baki isa saboda ke ko wani naki Mayraah taki zaman gidan nan ba, she remains in this house tunda ba gidan wani bane gidana ne, take it or leave it Hajarah babu inda Mayraah zata je...." Cikin tsawa Abba ya kare maganar, mikewa Ammi tayi tana wani murmushi tana kallonsa tace "Ohh i see, sai ka zabi ko ni ko ita, kuma tunda har aka billo min ta haka wllh wllh bazan ci gaba da zama da ita ba ko me zai faru kuwa, ai da can naga ba wani ya sa na zauna da ita ba, ynzun ma babu wanda zae sa ni in zauna da ita, don haka daga kai har 'ya yan naka da suka kai maka karata sai ku hadu ku zauna da Mayraah, su kuma su nemi wata uwar ba ni ba wllh" Daga haka ta juya fuuu ta wuce sama, Mama Ladi da ta sako da sauri jin hayaniya yayi yawa ta fashe da kuka tana kallon Abba bayan Ammi ta wuce sama tace "Kawai ka korata gida gun uwarta dake zugata su je can su karata Mamuda, ni dai ka gan ni nan babu ruwana bana goyon bayan rashin gaskiya tunda uwata ta haifeni wallahi" Abba da ransa yayi mugun baci ya juya kawai ya bar parlon, Maheer na jin duk yanda Abba suka yi da Ammi, likewise Mayraah dake gefensa, he never saw this coming, bai taɓa tunanin things will turn out this way ba, yasan Usman ne ya je ya samu Abba a part dinsa, ya kalli Mayraah dake ta kallon gate babu ko kiftawa, kawai ya jawota jikinsa, gathering every courage yace "Komai zai wuce Mimi" ta daga kai ta kallesa, sai a sannan ya ga hawaye a idonta, ya rungumeta lkci daya idanunsa suka kada shi ma, yana jin hawayenta na sauka jikinsa, cikin rawan murya yaji tace "Ina zan je yaya?"