Sashe 33
Mayrah Complete Hausa Novel · about 4 min read
"To wai yanzu kina nufin kin hakura Mayraah ta auri Lecturer din naku tunda kin tsira da gold?" Badiyya ta mata wani kallo tace "Na hakura?? Ashe ban cika Badiyyar ba kenan, wllh Haseenah in kika ga anyi auren nan to faduwa nayi na mutu murus, amma ina me tabbatar maki baza ayi auren nan da Mayraah ba matsawar in numfashi, ba boka ba Malam" Haseenah tace "To sai da ke za ayi auren kenan?" Badiyya tace "Aa ban ce da ni za ayi ba, ba sai an samu an lalata auren ba kafin in cusa kaina? Ai yanzu lalata auren shine babban aiki tukun... Akwai maganganu da yawa da nake son in gaya maki amma sai bayan naga an fasa auren don bana son soyayya dadi ya kwashe ki kije ki gaya ma Maheer ba tare da kinsan kin yi ba" Tana kai wa nan ta mike tace "Kin ga akwai wani gida da muke son zuwa yau din nan, mun fi sati muna kokarin gano gidan sai dazun nan da safe Allah ya sa aka gano, Haseenah tace "Wani gida kenan?" Badiyya tayi wani murmushi tace "Duk za a baki labari kwantar da hankalinki kawata, gidan ma ba daya bane ba biyu, gidaje kusan hudu ne, wallahi na kashe yafi dubu dari biyu wajen neman gidajen nan, yanzu haka bani da ko sisi a account dina, shi yasa nayi mugun farin ciki da samun gwal din nan" Haseenah na jijjiga kai tace "Baddieeeee" Badiyya ta wani juya tana dariya tana kas kas da chewing gum tace "Say it louder" Haseenah tace "Ai baki sani ba, ko da ace baki samo gold din nan ba na shirya daga dubu dari zuwa sama in baki contribution in dai akan ki lalata auren Mayraah ce, i will support u 100%, baki ga kullum follow up nake kan issue din nan ba, ai ba kiran banza nake maki ba kullum inji yanda ake ciki, A whole me fa Haseenah yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta tayi ma walakanci of the highest order a gidansu daga wai an kai ni in gaida uwarta, ai har yau da wannan abun nake kwana nake tashi yayi min mugun ciwo wllh, sannan har Maheer zai iya daukan gaba da ni a kanta for days, Wallahi ko da wasa bayan aurenmu da Maheer wataran ta shirya tace ta zo wajen yayanta sai na mata abinda har ta koma ga Allah bazata manta ba kuma a gaban yayan nata, babu kuma abinda ya isa yayi wllh" Badiyya tace "Ke naki duk me sauki ne Haseenah, bari in je Baddo na ta jirana tun dazu, duk yanda ku ka yi da masu siyar da gold din ki kirani ki gaya min" Haseenah tace "In sha Allahu" Daga haka Badiyya ta fice daga dakin Haseenah, mayafi babba ta yafa yau gudun fadan Maman Haseenah don matar ta fiye takura a cewarta. Yau Wednesday Mayraah na class suna rubuta test din wani lecturer dinsu, invigilators sun kusa hudu a ajin suna invigilating dinsu, suna shiga da some minutes Mayraah ta gama answering questions dinta duk da mugun wahalan da question din suka yi, Badiyya na class din sai satan amsa take a tsorace ta cikin wayarta da ta cusa a cinyarta, kamar daga sama taji ance "Stand up" duk ta gigice har sai da wayar ya fadi kowa ya juya yana kallonta with shock a class din, lecturer din da ya kamata ya duka ya dau wayar sannan ya kwashe script dinta yace "Get out" Juyawa tayi da sauri ta fice daga class din duk aka bi ta da kallo, Lecturer din yace "You will come back for this course in sha Allah, so let me see weda u will have another partner" Masu kokarin satan amsa dama duk suka shiga taitayinsu aka yi jigum, lokacin submitting nayi Mayraah ta mike ta taje ta yi submit din nata sannan ta fita daga class din, fita tayi outside the department don taga ko Dr Musharraf ya zo makarantar amma bata ga Motarsa a parking space ba duk da tasan monday da Tuesday kadai yake zuwa kuma week din nan duk bai zo ba, gashi basa wani magana sosai a waya yanzu, yawanci ma a kashe zaka ji wayarsa wani lokacin, sai in ya kunna ne yake kiranta suyi few minutes su a magana kuma shikenan, wanda hakan na damunta sosai, in just 2 days time bikinsu, kuma daga yau bazata sake shigowa department ba sai bayan bikin, duk da suna da test har biyu on friday amma duk lecturers din sun daga mata kafa za su bata make up test idan tayi resuming, dama iya test din yau ne ya kawota makarantar, don haka ko su Hamida bata tsaya yi ma sallama ba ta nufi gate din makarantar don samun adaidaita sahu a waje ta wuce gida za ayi mata gyaran jiki.... Mami ta sakko downstairs jin hayaniyar da ya cika parlor alhalin ita dai tasan daga ita sai mai aikinta ne a gidan, da mamaki take bin su Hajiya Halima da Mama Harira da kallo, yau har da matar yayan Abbansu Musharraf da bata ko zuwa gidan don banda ita ma aka kai lefe, Mami tace "Lafiya menene yake faruwa haka?"