← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 104

Sashe 8

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bude kofanshi da akayi aka shigo yasa yabude ido kadan ya kalli kofar, wata female Doctor ce mace kyakkyawan gaske doguwa tana sanye da atampa golden da dige digen pink ajiki, ta yana kanta dawani pink gyale chiffon plain bakomi ajiki saikuma lab coat dinta fari kal yasha guga sai kamshi take bazawa wajen aljihun ta an rubuta Dr Zee ajiki, maida idanunshi yayi ya lumshe ganin itace, karasowa ciki tayi taja kujera tazauna tace "Dr Helper koma Dr Charity zankiraka am here i need help too pleaseDr" dan yatsine fuska yayi alamun he's not into her silly talk, murmushi tayi tace "okay joke apart Dr Imam, I just came in, namanta da stethoscope dina agida kuma idan HOD yaganni wlh zansha fada, please kindly aramin naka kaji kasan Helper is your second name right Dr nice" tai maganan tana kallonshi tana murmushi cikada tsokana, ahankali yabude idanunshi kadan yadan kalleta saikuma ya yatsine fuska yace "wai why are all this intern Doctors not serious haan"? Dan murmushi tayi, hakan yasa yadaure fuska yace "ina magana kina murmushi, alright go and find stethoscope awani wajen not here" da sauri cikin kara narkan da murya kaman zatai kuka tace "no fa, ni wlh badakai nake ba" ganin yaki kulata saima wayanshi daya ciro yana kunnawa yasa tace "kasandai idan HOD yakamani bani kadai zaiyi scolding bako dan ai yasani akasan kane" dagokai yayi ya kalleta baison surutu idan kuma akwai macen dayataba gani aduniyan nan datafi kowa surutu is this girl, baimasan mesa HOD su yasata under him ba, dan gajeren tsaki yaja strictly yace "tashi kidau stethoscope daga that drawer and get out of my office Zeenat" yay maganan yana mata pointing drawer dake facing su a other side of the office wall, tashi tayi ahankali tai wajen drawer tana kara nanata yanda yakira full name dinta yau, ahankali ta sanya hannayenta taja drawer tabude taciro wani sabon stethoscope mai kyau blue tadauka sanan tamaida drawer ta juyo ta kallai gani datayi yasake lumshe ido kaman mai bacci yasa murya chan kasa tace "thank you Dr Imam" sanan tadaga kafa tai hanyar kofa harta murda kofan zata fita sanan yace "Dr Zeenat" da sauri tajuyo tadan bude manyan idanunta da mamakinta jin yakirata, folder yamika mata yace "this my patient tana Emergency, monitor her, I've written everything anan idan time yayi push d injections ma left hand veins dinta, i repeat left hand, idan any complications arise give me a call, idan kuma condition dinta yay stabilising move her to ward, zanje gida yanzu under no condition should u leave his hospital saikinga dawowana" kaman zatai kuka da sauri tace "waimena maka daga zuwana zaka hadani da irin aikin nan, yanzu harsaika dawo zan tafi? Inada bridal shower dazanyi attending fa by 5pm" tai maganan tana batarai sosai, dauke kai yayi yashiga tattare kayanshi tana tsaye tana kunkuni, lab coat yacire yarage dagashi sai kananun kayan dake jikinshi yadau wayanshi da car key dawani folder yazo zai wuce ya watsa mata wani mugun kallo, hadiye maganan tayi tareda sunnar da kanta kasa dan jitayi yacika mata ido bazata iya kallonshi ko cigaba da korafin ba yawuce yafita yabarta tsaye anan, takai kusan 2min dukan kirjinta bai dawo daidai ba sanan tasamu tabude kofan tafita har lokacin kamshin shi takeji.*
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍️M SHAKUR

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_

EPISODE 6️⃣

_FREE PAGE_
Fita yayi direct zuwa parking lot, motarshi yabude ya shiga yatadata yawuce yafita daga asibitin, agaban wani Baban gida a GRA yay horn ko sakan biyu ba'a dauka ba aka bude gate din yasa kan motar ya shiga ciki, packing yayi zai fito mai gadi daya rufe gate din yataho dagudu yace "angaida likita, Baban ka likita, Mamarka likita sannu ka da zuwa dan Alajin naira Alaji mai mutane nakowa" cikeda gajiya yasakamai key motarshi a hannu kaman zaiyi kuka yace "Ohhh i am not in for this your kirari Musa yau, ga key nan grab my things ka kawomin side dina and lock my car" yay maganan tareda juyawa yawuce abinshi, tsayawa Mai gadin yayi yarike kugu yakai yatsarshi daya kan kanshi yana tunani saikuma chan yanisa yace "wai ni da likita yaketamin yaren nan yadauka nima likitan ne yau, memawai yake nufi" "cha yayi ka kwashe kayan daya bari amota ka kaimai flat dinshi sanan karufemai mota" da sauri yajuya jin zazzakar murya na magana wata doguwar yarinya ce dabazata wuce 19 , 20ba, tana sanye da doguwan rigan atampa kanta a tsafe bama'a tajeba daga gani tsifa ake mata, harara mai gadin yaballa mata itama ballamai tayi tace "kazami kawai" da sauri yace "wlh saina hadaki da likita" gwalo tamai tajuya takoma flat dinsu shikuma ya shiga kwashe abinda akace ya kwashe sanan yawuce yay wani flat da shikadai ne daban agidan, sallama yayi tareda bude kofa yashiga ciki, falone hadadden gaske kal kal sai kamshi yake komi na dakin off whitene, shiga ciki yayi yana kalle kalle yace "dadina da likita akwai tsafta, kaga daki kaman nakara mai da yaji akai na ci tsabagen ban sha'awa" ijiye komi yayi kan centre table din sanna yawuce yafita yana kara waigen falon.

Sosai yabata lokaci sanan yafito yana sanye dawani short H&H 3quater milk color, yasanya wata black plain t-shirt, wanan karan babu glasses akan idanunshi hakan saiya kara bayyanar da kyawun kwayan idanunshi dasuke nan farare kal kwayan idon kuma bakake kirin, silipas yasaka sanan yabude kofa yafice, Baban flat din gidan ya shiga, wasu yan matane su uku ne a falon suna zaune suna kallo, suna ganinshi kowacce ta natsu atare suka gaidashi "Ya Imam good afternoon welcome" gyadamusu kai kawai yayi yace "how come banga ku fara shirin islamiyya ba" karaman cikinsu mai 19yrs din wacce ake kira da Rayyana ce tace "Ya today is Thursday fa" gyadakai yayi yace "oh okay, where's Ammi"? Kafinma subashi amsa sukaji murya datadan manyanta ance "anya akwai randa Imam zai iya dawowa gidan nan bai tambayi maman shi ba, ai kaga abinda yasa nafiji dakai kansu wa'è" tanuna babban cikin yara matan mai suna Rahma tace "su yaran Babansu ne" dariya yayi daidai ta sauko ya rungumeta hannunta takai kan cikinshi tace "zokaci abinci oya oya, cikin nan babu abinci cikinshi" dining takaishi tazubamai abinci a plate sosai yaci abincin yay nak sanan yafara mata hira, aduniyan nan Ammi kadai yake hirada ita kaganshi awani waje zaka dauka bai magana ko dariya.
Yatsine fuska yayi yace "Amma wlh nagaji da aiki at this government hospital, narasa maisa Dad baiso nai aiki a hospital dinshi" murmushi Ammi tayi tace "ai duk Dr dabai aiki a federal government hospital ba baida experience, watarana zakaga abinda yasa Babanka choose that 4 you son, banda haka is just the matter of time ko" yatsine fuska yayi yatashi yamika hannu yadau cup din fresh juice yace "Ammi bari naje nadan kwanta, by 5 kitadani pls, 6 zan koma clinic" binshi tayi da kallo yawuce falo, kannin nashi ya kalla yanda suka natsu suke kallon zeeworld yace " kunyi salla"? Kasa amsashi sukayi saidai kowannensu yashiga tashi ahankali gudun karya makesu sukai stairs da gudu, girgixa kai kawai yayi yawuce yafita daga flat din zuwa nashi.
****
Chapter 8 · 0% Book details