← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 104

Sashe 12

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali yasaki dan murmushi yana kallonsu yana tunani who ever says money shine happiness karyane, happiness kauna ce, just look at this father and daughter gwanin ban sha'awa. Kaman ance Baba yajuyo yaga Dr Imam tsaye da hannu Dr Imam yamishi alamu dayazo batare da Fatima ta gansu ba, tashi yayi ya ijiye plate din yace "ina zuwa Zara'u" hanyar kofa Baba yayi hakan yasa ta kalli kofan hada ido sukayi da Dr Imam da sauri ta dauke kai, abakin kofa Baba yasameshi yabashi hannu suka fara tafiya sukai hanyar waje Dr yace "Baba daman i wanted to see you kafin natafi ne, akwai abinda nakeson na tambayeka" da sauri Baba yace "menene likita"? Dan jim yayi kaman wanda baison yin maganan saichan yace "Baba naga tabon duka, fresh shaidan bulala ajikin Zara'u, waye yamata wanan dukan Baba?"

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_

Shiru Baba yayi yakasa cewa komi yama kasa cigaba da tafiya hakan yasa shima Dr ya tsaya kaman mai nazarin shi saichan ya nisa yace "Baba shirun dakamin ya tabbatar da kasan wanda yamata dukan kenan wanda nina tabbata bakai bane, ayanda naga kakeson yarka nasan bakaine zaka mata wanan dukan ba, Baba yarinyar nan bama wanan dukan bane na farkon dukan da aka mata ba dan jikinta da tabo dayawa, koma waye ke dukanta Baba hakkinka ne amatsayin ka na mahaifinta ka kareta, ka tsareta, mace ce tanada rauni sosai, abu kankani zai iyasa rayuwar ya mace yabaci dan haka dole ka kula, idanma rashin ji take bada duka zaku gyarata ba ai" ahankali Baba yace "bantaba ganin salahar yarinya mai biyayya irin Fatima ba, ko kadan batada rashin ji sai dumbin biyayya da girmama nagaba da ita" Shiru Dr Imam yayi yana kallon Baba ahankali yace "mahaifiyarta ke dukanta"? Girgizamai kai Baba yayi yace "batada mahaifiya" shiru Dr yayi saima yakasa magana, ganin haka yasa Baba yace "ni fulanin Maiduguri ne, mahaifiyarta buzuwar Maiduguri ce amman dukanmu dagani har mahaifiyarta rainon kauyene muba yan burni bane, a kauye mukai aure muka kuma tare cikin dangi da yan uwa da abokan arziki harta haifamin diyata Fatiman nan dakake gani ayau, bazan manta ba, lokacin Fatima nayar shekara biyu da watanni zan fita kiwo da safe tahau kuka zata bini, haka takemin and muddin tabini tosaina siya mata plantain chips da ake saidawa a bakin gari nadawo da ita gida sanan zata barni nafita kiwo, haka na dauketa nace bari naje nasaimata wanan plantains chips dinan abakin express sabida tanason abin sosai, kauyenmu nakan express road ne na zuwa asalin cikin garin Maiduguri, kuma masu saidawa anan bakin titin kake ganinsu (hawkers) na dauketa namata makawuya da nufin innaje nasayo mata mukoma nafita kiwo, muna fita bakin titi nakira mai plantain zan siya mata, na karba daya nasa mata a hannu nasa hannu zan ciro kudi a aljihu nabashi bangama cirowa ba mukaji wani irin kara da girgizan kasa dabansan lokacin dana dauki Fatima data rusa ihuba na kankame ajikina, kafin kasani naga ana ihu ana gudu, ga hayaki wuta natashi daga cikin dajin dana fito...." yadanyi shiru tareda lumshe ido, yanda Baba yay shiru yasa yagane end of the story, ahankali cikin wata murya dazai nuna asalin damuwa yace "Allah ya jikansu" ajiyan zuciya Baba ya sauke yace "Ameen, hadadden bomb yan boko haram sukai amfani dashi suka tada kauyenmu tass wai warning sukama gwamnati, dagani sai Fatima muka rayu a kauyen mu gabaki daya dasu bomb din yatashi dan safiya ne basuriga sun fita ba, nida Fatima mun wahala aduniyar nan, neme neman aiki, kwadago, da leburanci shine yakawoni nan Kano, inda nasami wata baiwar Allah matar nada kirki sosai tabani machine ina express tana tayani rainon Fatima dan tanason Fatima sosai matar Fatima ke kirada Baaba, yaranta duk suna waje, da aikin danake nasamu nahadu da wata budurwa dake saida mana da abinci a tasharmu na yan achaba Rukkaya, naji ina sonta namata bayanin kaina tace taji tanaso na, nadauki Fatima na kaimata tanason Fatima sosai, Fatima na yar shekara biyar mukai aure, Hajiya tabamu yarmu tabarmin machine din cewa zasubar Kano, ranan Fatima tai kuka amman ta hakura, a kasan waje take zama bata cika dawowa Nigeria ba, amman duk intazo Fatima na zuwa wajenta" ahankali yace "step Mum din Fatima tamata dukan nan"? Gyadama Dr kai yayi ahankali saikuma yace "da farko dana aure Ruka tana bala'in son Fatima sosai, dayake bata haihu dawuri saida mukai kusan shekaru biyu Fatima na shekara bakwai ta haifi Habib to daganan kaman asiri son datake ma Fatima yakoma ki, kodan taga son danakema Fatima mai karfine oho, bawai bansan sauran yarana bane a'a kawai dai son Fatima dabanne araina, sabida tun tana yar yarinya take wahala bata taso gidan gatan uwa ba kona kakanni duksun rasu, ina matukar tausayama Fatima, yanda kuma nake sonta haka Fatima take sona, ko ciwon kai yakamani yarinyar nan saikaga kaman zata haukace sabida damuwa, ina iyakan kokarina wajen kareta, ni kaina bansan da dukan ba sai dazu danaje gurin aikinsu d'ana Habib a samin iska a machine yake gayamin ai dukan da Mama ta mata yatada mata da ciwo" Ajiyan zuciya kawai Dr Imam yasauke sosai yaji Baba yabashi tausayi ainun, ahankali yamikama Baba hannu yace "Baba ka koma wurinta saida safe, gobe idan nazo taji sauki zan sallameku saita cigaba dashan magani, ka kulada ita" gyadamai kai Baba yayi Dr yawuce yatafi yabar Baba anan tsaye, Baba yadade tsaye awajen yana wani irin dogon tunani, da idan Ruka tama Fatima duka kowani abu yana tsawatar mata amman yanzu baya iyawa, dazu da Habib yafadi mai abinda yafaru ranshi yabaci ainun yatafi gida but yanazuwa daya kalli fuskarta kasa mata maganan yayi, ko kayan salla yace zai sayama Fatima tace mai bazaka siyamata ba zaiji rashin yabaci amman kuma saiya kasa mata magana, bazai kuma siyan ba, jiyayi kanshi na ciwo hakan yasa yahakura da tunanin yawuce yakoma ward.

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_

Kwance yaganta kan gado tana kallon kofa kaman dama shitake jira ya shigo tana ganinshi tawani sauke ijiyan zuciya mai karfi, murmushi yamata yakarasa yaja kujera yazauna yana kallonta yace "jirana kike daman? Nadauka kinyi bacci Zara'una" dan karamin bakinra tabude tace "a'a" shiru yayi yana kallonta, kallonshi tayi itama sanan tace "Baba rigan nan dakasaimin nada kyau sosai ina sonshi" ahankali yadan duko da kanshi zuwa saitinn kanta anatse yace "maisa baki gayamin dana dawo da daddare Mamanki ta dakeki ba eh"? Yadanyi maganan ranshi abace, ahankali tace "Baba" cikeda dan bacin rai yace "duk randa tasake dukanki ko aka miki wani abu baki gayamin agidan nanba sai ranki yabaci Zara" ganin yanda ran Baba yabaci yasa taji hawaye sun cikamata ido murya chan kasa tace "kayakuri Baba" ganin yanda tai wani iri yasa yay murmushi yace "yawuce, na gwada kiran lambar Baabar ki bata shiga bata kasar hala" gyadamai kai tayi ahankali, ganin har lokacin damuwa ne akan fuskanta yace "baki taba tambayana ya suffan mahaifiyarki yakeba Zara'una, ingaya miki"? Da sauri ta gyadama Baba kai, murmushi Baba yayi yace "Mamarki doguwar mace ce sosai dan tafini tsawo saisa nai mamaki yanda baki wani dauko tsawonta ba, kuma shine abu na farko danakeso game da ita, inason doguwar mace saikuma yahadu da sunanta danake so shima Surayya, Mahaifiyarki nada yar doguwar fuska kaman taki anan, sanan fuskar nada dan fadi, tanada wasu irin idanu exactly irin idanun nan naki, zakiga acikin mutane idanunta dabanne, idan ta kalleki ne zaki kara ganin tsabaragen kyawun idanun, tanada dogon gashi baki kirin sanan yanada cika, kinga yanda kullum bakison tsifa sanan akama samu kikayin baki iya tajewa balle ki kulle haka gasjinta itama yake, tanada dan goshi dakuma jan lebe inda kika banbanta da ita kenan, ke kin dauko lebena pink itakuma nata jane kaman tasa jan jambaki, mahaifiyarki batada losewan kumatun nan naki ni kika biyo da wanan, saikuma sanyin hali da hakuri dakuma juriya da kunya Fatima dukkin gado mahaifiyarki, saisa nake alfahari dake, dukmai hakuri da juriya yanacin riban rayuwa wata rana komin daren dadewa ki rubuta ki ijiye" ahankali tace "saisa bana fadamaka kome Mama tamin agida, Baba Mama tana matsayin uwace agareni, tabani kannai danake so sanan tarike ni cikinsu Baba bawai bazan iya fadamaka bane, kokuma bazan iya ina mata wasu abubuwan ko rashin kunya ko makamancin haka bane a'a, kariga ka koyardani hakuri dakuma juriya, banson tasanadiyata kana fada da Mama kullum, babu abinda nakeso aduniyan nan samada farin cikin ka, Baba kanada hawan jini banson abinda zai dagama hankali, kome nayi Baba nasan menakeyi wlh niba yarinya bane kawai kadinga mini addu'a kaji, nagama makaranta nafara aiki na kula dakai dasu Habib da dukanku" for the first time yau saiyaji Fatima tai magana kaman wata yar shekara talatin, hannunshi yakai kan kumatunta yana murmushi yace "Allah yacika miki burin ki, Allah yamiki albarka Zara'una, Allah yabaki miji nagari" murmushi tayi taja zani tarufe fuskarta tace "saida safe Baba kaina yafara ciwo mani" murmushi kawai yayi baisake cemata komiba idan sabone yasaba da kunyanta duk randa zai mat hiran aure ko magana suke karshen maganan yazo kenan dan guduwa zatayi.

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da saUran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_💫
Chapter 12 · 0% Book details