← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 104

Sashe 10

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_FREE PAGE_
Fita yayi direct zuwa parking lot, motarshi yabude ya shiga yatadata yawuce yafita daga asibitin, agaban wani Baban gida a GRA yay horn ko sakan biyu ba'a dauka ba aka bude gate din yasa kan motar ya shiga ciki, packing yayi zai fito mai gadi daya rufe gate din yataho dagudu yace "angaida likita, Baban ka likita, Mamarka likita sannu ka da zuwa dan Alajin naira Alaji mai mutane nakowa" cikeda gajiya yasakamai key motarshi a hannu kaman zaiyi kuka yace "Ohhh i am not in for this your kirari Musa yau, ga key nan grab my things ka kawomin side dina and lock my car" yay maganan tareda juyawa yawuce abinshi, tsayawa Mai gadin yayi yarike kugu yakai yatsarshi daya kan kanshi yana tunani saikuma chan yanisa yace "wai ni da likita yaketamin yaren nan yadauka nima likitan ne yau, memawai yake nufi" "cha yayi ka kwashe kayan daya bari amota ka kaimai flat dinshi sanan karufemai mota" da sauri yajuya jin zazzakar murya na magana wata doguwar yarinya ce dabazata wuce 19 , 20ba, tana sanye da doguwan rigan atampa kanta a tsafe bama'a tajeba daga gani tsifa ake mata, harara mai gadin yaballa mata itama ballamai tayi tace "kazami kawai" da sauri yace "wlh saina hadaki da likita" gwalo tamai tajuya takoma flat dinsu shikuma ya shiga kwashe abinda akace ya kwashe sanan yawuce yay wani flat da shikadai ne daban agidan, sallama yayi tareda bude kofa yashiga ciki, falone hadadden gaske kal kal sai kamshi yake komi na dakin off whitene, shiga ciki yayi yana kalle kalle yace "dadina da likita akwai tsafta, kaga daki kaman nakara mai da yaji akai na ci tsabagen ban sha'awa" ijiye komi yayi kan centre table din sanna yawuce yafita yana kara waigen falon.

Sosai yabata lokaci sanan yafito yana sanye dawani short H&H 3quater milk color, yasanya wata black plain t-shirt, wanan karan babu glasses akan idanunshi hakan saiya kara bayyanar da kyawun kwayan idanunshi dasuke nan farare kal kwayan idon kuma bakake kirin, silipas yasaka sanan yabude kofa yafice, Baban flat din gidan ya shiga, wasu yan matane su uku ne a falon suna zaune suna kallo, suna ganinshi kowacce ta natsu atare suka gaidashi "Ya Imam good afternoon welcome" gyadamusu kai kawai yayi yace "how come banga ku fara shirin islamiyya ba" karaman cikinsu mai 19yrs din wacce ake kira da Rayyana ce tace "Ya today is Thursday fa" gyadakai yayi yace "oh okay, where's Ammi"? Kafinma subashi amsa sukaji murya datadan manyanta ance "anya akwai randa Imam zai iya dawowa gidan nan bai tambayi maman shi ba, ai kaga abinda yasa nafiji dakai kansu wa'è" tanuna babban cikin yara matan mai suna Rahma tace "su yaran Babansu ne" dariya yayi daidai ta sauko ya rungumeta hannunta takai kan cikinshi tace "zokaci abinci oya oya, cikin nan babu abinci cikinshi" dining takaishi tazubamai abinci a plate sosai yaci abincin yay nak sanan yafara mata hira, aduniyan nan Ammi kadai yake hirada ita kaganshi awani waje zaka dauka bai magana ko dariya.
Yatsine fuska yayi yace "Amma wlh nagaji da aiki at this government hospital, narasa maisa Dad baiso nai aiki a hospital dinshi" murmushi Ammi tayi tace "ai duk Dr dabai aiki a federal government hospital ba baida experience, watarana zakaga abinda yasa Babanka choose that 4 you son, banda haka is just the matter of time ko" yatsine fuska yayi yatashi yamika hannu yadau cup din fresh juice yace "Ammi bari naje nadan kwanta, by 5 kitadani pls, 6 zan koma clinic" binshi tayi da kallo yawuce falo, kannin nashi ya kalla yanda suka natsu suke kallon zeeworld yace " kunyi salla"? Kasa amsashi sukayi saidai kowannensu yashiga tashi ahankali gudun karya makesu sukai stairs da gudu, girgixa kai kawai yayi yawuce yafita daga flat din zuwa nashi.
****

Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai tanadan yatsine fuska ganin haka yasa da sauri Baba dake zaune kan kujera gabanta yakai hannunshi kan kumatunta dakeda wani irin laushi kaman na jariri ya shafa taredakai fuskarshi yana leken idanunta datake kokarin budewa yace "Zara'una, Fatima Zara bude idanunki nine Babankine, ganinan taredake" ahankali take bude idanunta jin muryan Baba sama sama saikuma tabude idanun tass tadaurasu akan fuskan mahaifinta tanajin wani irin ciwon kai amman bakaman nadazu ba (safe). Jin hayaniya sama sama yasa taware idanunta duka da kyau ta kalli inda dake, karfe tagani da ledan ruwa kafin tabi igiyan da kallo taga yana hannunta sanan ta waiga tana kalle kalle ganin suna wani babban daki dake dauke da gadajen marasa lafiya guda goma side dinta biyar opposit dinta ma biyar, yanda take kalle kalle yasa Baba yace "kina asibiti ne an kwantar dake" juyowa tayi ta kalli Baba kafin tayi magana Dr Zee data gama duba patient din kusada gadon Fatima ne takaro fuskarta cikeda annuri tana kallon Fatima data bude ido tace "ahhh yar gatan Baban ta kin tashi"? Dayake Zee akwai surutu ta kalli Baba tace "Baba Zara'unka ta farka ka barni nahuta yanzu, kasa naduba maka ita ko baccin lafiya take dazu yafi sau dari" sanan ta kalli Fatima tace "Zara bara infada miki wani abu Babanki nasonki sosai sosai da ace haka iyayen kowa ke sonsu haka da yara basu wahala aduniyan nan ba daduk munji dadi" dan murmushi tayi dudda ciwon kan dake cinta murmushi yasa dimples dinta suka lotsa sosai dasauri tace "auuuuu Baba yarinyar ka nada mugun kyau jibi wani cute dimples dasuka bayyana akumatunta dudda batada lafiya, Baba kuyan wani garine dan Allah"? Tai maganan tareda juyawa taja kujeran next bed dake gaban na Zara takawo gaban gadonsu kusada Baba zata zauna dantaji labari taji andaka mata tsawa. "What do you think you are doing Dr Zee"? Ba Zee kadai ba har Baba, Fatima dama duka yan ward din saida suka dagokai duk suka waigo, Dr Imam ne, yana sanye da black cover, black trouser, sky blue short sleeve t-shirt daya bayyana muscles dinshi manya manya, idanun nan nashi sanye da fararen glasses, gashin sajenshi sunyi lub lub sai uban kamshi yake zubawa hannunshi rikeda lab coat bairiga yasakaba yana kallonta babu wasa ko daya akan idanunshi, tsit kakejin dakin kaman ba'ai hallitta awajen ba, ahankali tahadiye miyan dataji yabushi abakinta dakyar ta iya dauke idanunta akanshi ta kalli agogo 6 na yamma daidai maisa batai tunanin lokacin dawowan shi yayiba taketa surutu, kasa magana tayi ta tsaya awajen chak, nan kakejin kus kus awajen masu jinya na daman ta ishemu sai shegen surutu ga Oganta nan ai yashigo, wasu na kus kus suna su basu taba ganin likita mai surutu hakaba wasu na ai kaman yar makaranta ce batariga tazama likitan bama, jin kus kus din dayan ward sukeyi yasa yahadiye fushinshi dan baiso ya disgata as it is yanzu ma was so embarrassing balle kuma yamata fada hakan yasa yace "go and wait 4 me in my office" da sauri ta gyadamai kai ta tako har zuwa inda yake abakin kofa tawuce tabi ta gefenshi tafice.

Yadan dauki kusan 1min sanan yakaraso ciki yawuce gadon Fatima inda yaga Zeena ta tsaya alamun anan take, yana karasawa kafinma yay magana Baba yabashi hannu yace "barka da zuwa likita" "ina yini Baba yamai jiki ta tashi"? Da sauri Baba ya kalleta ganin idanunta a lumshe yakira sunanta yace "Zara'u tashi bude idanunki Dr yazo dubaki" adan hankali Dr Imam yace "barshi tukunna sai Nurses sun mata wanka an chanza mata kaya taci abinci sanan zanzo naduba ta, Nurse" yakira biyu daga cikin nurses din ward din yamusu magana da yaren da Baba bayaji sanan yawuce yafita, tadata sukayi cuka cire karin ruwan, kasa tsayuwa tayi hakan yasa suka gunguro wheelchair.

Sosai take cije lips kaman zatai kuka sabida yanda takejin azababben ciwon mara har suka kaita bayin, daya daga cikinsu ne tadawo tace "ina kayanta Baba" da sauri yanuna musu yar karaman jakan daya sawo mata kaya, dauka tayi tawuce bayin da taimakonsu tana bala'in jin kunya suka mata wanka da ruwan dumi suka gyarata suka saka mata wani sabon pant da pad, wani aikin sai nurses all hail to our hospitals nurses, you people rock, Allah yabiyaku ladan aikin dakukeyi Ameen!!!.

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
Chapter 10 · 0% Book details