← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 104

Sashe 56

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Assalamu Alaykum" "Sir we are calling in the respect of payment din dakayi na yaronka Khalid Muhammad dazun nan munason musan yaushe kakeson mu aiko maka dashi" da sauri cikin harshen turenci Baba yace "mene? Waye yabiya kudi? Da sauri Lawyer yacire wayanshi daga kunne ya kalli screen din, katse wayan yayi ya kalli number Baba dake kan laptop dinshi yagadai daidai ya dauki number Waziri dake kallonshi ne yace "ya akayi"? Ahankali yace "am coming sir" yasaka wayan a speaker yasake kiran Baba, Baba na dauka kafin ma lawyer yay magana cikeda masifa Baba yace "kaga bani nabiya kudin nanba kuma koma waye yabiya shiya sani, all I know is Khalid kowaye ma is not my son! I repeat he's not my son, he's just someone I helped and pick up on the street and shelter him that's why I use the boy to pay back my debt yayita zama agidan ku ai kaman charity kuke yanda kuke bada taimakon nan nasan zaku rikeshi, please I don't know him nobody should send him back to me because I will send him away, I am not his father, I have no blood ties with him, nabaku yaron, please since anbiyaku bashin ku wanda banmasan waye yabiya kinda Alhamdulillah amman that boy I hate hearing his name talk more of seeing him, thank you sir bye" sake kallon wayan Lawyer yayi sanan ya kalli Waziri yace "what kind of father is this"? Ahankali Otun yace "I don't blame him ance haka northerners suke ai, basu damu da yaransu ba saisa ma suke kaisu almajiranci, they hate their children yet sunfi kowa haihuwa" juyowa Otun yayi ya kalli Mai Martaba dayay shiru duk yakejinsu yace "what do we do with the boy now" kafin Babanshi yay magana Tobi yace "Dad I want the boy, he should keep working for me but every month zamu dinga bashi salary shi a hannu yatara later he can use it for something tunda ubanshi doesn't want him again, i want my Boy" tunda yafara maganan Babanshi ke kallonshi sanan ahankali yace "why do you love that Boy so much Tobi, I've never seen you love anyone like that" dan murmushi yayi yatashi yay hanyar fita, yace "just keep my boy for me if his Dad don't want him ni I want him, zanma dawo dashi side dina nabashi daki daya awurin yabar bangaren Guards, love you Dad" yawuce yafita, ahankali Babanshi yace "love you too" sanan yakalli Otun yace "the Boy states with Son tunda yana sonshi" gyadamai kai Otun yayi ya kalli lawyer yace "that boy is soIm lucky, prince loves the boy he will take him u can go" tashi yayi lawyer yawuce yatafi abinshi.
7/5/21, 8:45 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍🏾M SHAKUR

EPISODE 4️⃣3️⃣
Wuraren Magrib yay parking agidan ya sauko ya wuce ciki bai ganta a falo ba hakan yasa yawuce sama ahankali yatura kofan bedroom din ya shiga, kan carpet din dakin yaganta tana salla sanye da daya daga cikin hijaban daya siyo mata dasuka tsayamata aciki, jingina yayi da bango yay folding hannu yana kallon yanda take sallan harta sallame sanan tajuyo hijabin yamata kyau sosai bana wasaba, juyowa tayi ta kalleshi sanan ahankali tace "good evening" batare daya kalletaba yace "stand up let's go back home" gyadamai kai tayi gabanta nafaduwa tamike tsaye, wajen yan kayayyakin daya saimata yayi ta tattare yarike sanan yatsaya yana kallonta yace "let's go" akaro nabiyu ganin tsoro take, kito dinta tasaka sanan ta tashi batare data cire hijabin nanba suka fice har zuwa mota, a boot yazuba kayanta sanan yabude baya wani leda yabude yaciro p-cap sanan ya tsaya gabanta, hijabin jikinta ya kwabe mata gashinta suka zubo, ahankali yakoma ta bayanta ya tattare gashin da hannunshi dayaji santsi sanan ya tupke da kyar danbai iyaba yanadai ganin idan Anty Ayobami nama Princess sanan yasamata p-cap din yabita da kallo tana sanye da riga da wando har lokacin yace "enter" shiga motan tayi ahankali tazauna gabanta nafadi sanan ya ijiye hijabin kusada ita yamaida kofan yarufe yawuce gaba yazauna yatada motan mai gadi namusu bye suka tafi gabanta sai dukan uku uku yake.

Har cikin gidansu ya shiga yay parking wurin parking guards sunzomai sannu da zuwa yace suwuce su bashi waje, suka tafi sanan yabude kofar bayan motan yamika mata hannunshi ahankali takama hannunshi yaji hannunta zufa sosai, saukowa tayi yakai hannunshi p-cap din ya gyara mata duk yakareta daga jikinshi sanan yarike hannunta suka fara tafiya dadan sauri sauri duk set din guards din dazasu zo gaisheshi kafinma suzo zaimusu hannu cewa bayaso cikin ikon Allah sukai flat dinshi har sama yakaita sanan yabude mata wani daki dake facing nashi yace "this is your room henceforth always stair indoors, if anybody comes dayake yaganki maybe Dad or mum wear your stuff suna cikin wardrobe din dakin kafin kifito ki gaidasu kina komawa saiki cire" gyadamai kai tayi ahankali saikuma ahankali tace "thank you Sir, May Allah bless you" juyawa yayi kawai ya sauka yana murmushi itakuma ta kalli dakin, dakin yahadu sosai bana wasaba bakin gado tasamu tazauna sai gashi ya shigo da kayanta tabishi da kallo harya wuce yafita tana mamakin mesa yake fama da ita haka he's so good.

Wuraren 9 taji anyi knocking saikuma aka bude kofan yashigo yana rikeda tray, daga kofa ya tsaya batare daya shigo cikin dakinba yace "come" tasowa tayi ahankali cikeda kunya dan babu dan kwali akanta harta karaso gabanshi ta tsaya, batare daya bata abincin ba cikin murya yar karama yace "se ooje amala"? Da sauri tadaga fuska ta kalleshi dan this is the first time ever dadai take taredashi taji yay yare, kowaye zai mishi magana da turencin nan nashi mai dadi yake reply, yanda take kallonshi haka yake kallonta shima hannunshi daya yazare daga tray din ahankali yakai saitin idanunta dasauri ta lumshe idanun tasaki dan karamin murmushi ahankali tace "I didn't hear what you say sir" murya chan kasa kaman wanda zaimata whispering abu yace "open your eyes lemme tell you wat I said" gently tasake bude idanunta dasukadan kankance tadaura akanshi, wani irin yirrrrr yaji amman yadake, dawata kalan calm voice yace "I said zakici Amala"? Gyadamai kai tayi ahankali batare datai magana ba hakan yasa yabata tray din ahankali takai hannayenta ta karba sanan yace "gud night" gyadamai kai tayi yawuce yafita tareda rufomata kofa.

Komawa tayi ta zauna taga amala ne ewedu dakuma pepper soup sai ruwa da drink, sosai taci dantaji babu yaji abin yamugun bata mamaki ya akayi babu yaji tass tacinye ta tashi tashiga bayi ta wanko hannunta taji dadin dakin sanan tazo tasaka sakata akofan tashiga bathroom din dataga anzuba mata kayan wanka dakomi harda cream ba Neutrogena, tai wanka sai kamshi take sanan tafito ta kwanta tadanyi bacci har zuwa 2 ganin takasa bacci kalaman Baba sai mata yawo suke akai yasa tasake tashi ta zauna tabuga tagumi tana tunani takasa yarda ita ba yar Baba bace bayan ance suna kama, ganin damuwan zai dawomata sabo sai kawai ta shiga tadauro alwala tazo tafara salloli, sai wajajen 3 darabi bacci yakwasheta, bata sake tashiba sai six alwala tashiga bayi tadauro tafito tai sallan sanan tazauna tai azkar kafin tafata karanto Al'Qurani daka dan bataga Qur'aniba.

Kaman amafarki yaji wani irin kira'a mai dadi na ratsa kunnenshi hakan yasa yabude idanuwanshi tass, tashi yayi yazauna yana saurara dudda bada karfi takeji but yana jinta sama sama, ahankali yasauka daga gadonshi yawuce yashiga bayi, for the first time arayuwanshi yau baiyi wanka ba kawai alwala yadauro yafito ya shiga closet yadauki dadduma yafito yahaukai yay salla sanan ya sallame yatashi ahankali yabude kofa yafito, knocking kofar dakinta yayi, tanakan dadduma taji anyi knocking hakan yasa ta tashi tana sanye da hijabinta bude kofan tayi suka hada ido saukar da idanubta kasa tayi tace "good morning Sir" batareda ya amsa ba yace "zan fita jogging, stay inside okay" gyadamai kai tayi ahankali yawuce yatafi ta maida kofan tarufe takoma kan dadduma tana zaune tacigaba da karatu taji yabude kofanshi yafito ya sauka kasa yabude kofan falo yafice, tashi tayi dagakan carpet din ta shiga tattare dakin da babu abinda yasame shi sanan tazaua tai shiru, tunani tayi ai babu mai shigo part dinshi da safe barinma yanzu da ansan yatafi jogging bari taje ta gyaramai bedroom dinshi, bude kofa tayi tafito sanan tashiga dakinshi bayi tafara shiga dataga yay messing up tahau gyarawa saida ta gyara bayin tsafa tagoge komi tai mopping dinshi kal sanan tafito tashiga closet dinshi hakanan takeji now morethan ever she want to work for him she wants to make him happy, sabida yanada kirki he helped her, he helped her life, yarufa mata asiri, one bye one take tattare kayan dataga duk yazubo dasu daga hanger kasa kana ganin kasan wasu kayan yake nema saisai yay messing dakin up haka, ita mamaki abin yake bata gashidai dan gayu amman babu abinda ya iya, tayi nisa sosai agayaran tana arranging kayan nashi da kusan dukane yazubo dasu kasa taji anbude kofan bedroom dinshi anshigo muryan mace na. "Hey Babe, I've been calling you boyfriend baka dauka wayana ba" shiru tayi tabi dakin da kallo ganin babushi aciki, gadai gadon ahargitse, tana sanye da digon stock jean blue daya kamata sosai dawani riga mai spaghetti hand fari datai zanzaro da jean din asamanta tasaka belt, kayan sun amsheta kafanta sanye da dogon heal tana kamshi sosai, tasaka braided wig dasuka zubo har waist dinta tai kyau sosai tana rike da expensive Hermès handbag dinta da iPhone 12 pro max dinta a hannu tana kalle kalle, shigowa tayi ta zauna akan gadon tasake daga murya tace "baby are you in the bathroom come out, can't wait to kiss you" .....

Sosai gabanta kewani irin faduwa jin muryan mace wacce batasan kowaye ba, ahankali ta ijiye riganshi dake hannunta batare datai making any movement ba tafara kalle kalle tana neman inda zata boye, closet din wandonshi ta kalla dayafi kowani closet tsawo sabida a tsaye ake sagala wandunan batare da an linkesu ba, dasauri taje wajen tahau ta shige tareda tsugunnawa taboye bayan wandunanshi tana taushe bakinta sabida tsabagen tsoro......
......
Chapter 56 · 0% Book details