← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 104

Sashe 5

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_FREE PAGE_
Wuraren karfe uku wani mugun azababben ciwon ciki yatadata, da farko tazaci mafarki take amman sai taga ba mafarki bane, wani irin murda wa da cikinta da maranta sukeyi kaman ana murda hanjinta kanta na shegen sarawa, kokarin tashi tayi daga kwancen datake amman takasa sabida komi najikinta wani irin ciwo yake mata, ahankali tasaki wani wahalallan kuka mara sauti..... cikin bacci kaman daga sama Habib yaji sheshekan kuka tashi yayi yabude idanunshi, dayake yanada wata yar karaman tocula hakan yasa ya kunna ya haska Fatima dake kwance idanunta sun kumbura sunyi jajir sabida kukan datasha jiyada daddare gakuma bacci, karasawa yayi kan katifarta da sauri, murya chan kasa gudun kar Mama tajisu yace "Ya Faty menene kike kuka"? Yay maganan yana kai hannunshi saman goshinta wani irin zafi dayaji yasa da sauri yadauke hannunshi yace "innalillahi Ya Faty bakida lpy in tada Baba"? Girgizamai kai tayi, cikin muryanta da ba'aji sosai tace "dagani na zauna" hannunta datake mikamai yakama yadagata ta zauna da kyar tana share hawaye tana cizan baki, sosai yaji tabashi tausayi, yanason Ya Faty kaman ba gobe dan tamafi kulada su kan uwarda tahaifesu, tun suna yara itane komi nasu, duk in yanajin yunwa saidai in Ya Faty batada kudi amman saita bashi yaje yasai wani abin, idan basuda lpy, Mama nafita kome sukeso saita dafa musu suna gamawa su wanke tukunya ta yanda Mama bazata saniba, ganin yanda hawaye yakasa dena zuba daga idanunta yasa yakoma kusada ita ya zauna kanshi ya daura kan hannunta yafashe da kuka ahankali gudun kar ajisu murya chan kasa yace "Ya Faty kiyakuri kinji Allah na sama yana kallo wata rana sai labari, Mama batada kirki kuma batason ki amman kinga duk ranan dana girma zan daukeki daga gidan nan nasai miki wani gida nasai miki mota nasa police nace musu karsu bari Mama ta shigo balle ta dakeki kota saki kuka, I promise idan na girma ko maganan banza babu wanda ya isa yafada miki kinji, kidena kuka, bari na girma kiga abinda zai faru kidena kuka" yay maganan yana share hawayen dake zubomata, danne kukan tayi takai hannunta ta sharemai hawayen shi shima tana murmushi tace "ninasan kanina soja ne, Habib dina, nasan idan Habib ya girma ko kallon banza babu wanda ya isa yamin, Habib dina sojana toko tubambale mayen abinci" dariya yahauyi kaman bashine ke kukaba, murmushi tamai tace "jeka koma baccin ka kaji" da sauri yace "kinji sauki"? Gyadamai kai tayi alamun eh, tashi yayi yawuce ya kwanta awajen shi yace "dazaran yacigaba ki kirani kinji" Tom ta amsashi ahankali, kwanciya yayi tareda kashe toculan, sai alokacin taji ashema hiranshi rahama ne agareta wani mahaukacin ciwone yakamata dayasa taji kaman zata kurma ihu amman ta daure tarasa inda zata saka kanta taji dadi, har aka kira asubahi idanunta biyu, har aka tashi tanaji Baba yabude kofa yafita yadawo amman takasa koda motsi.
**

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

Wuraren shida nasafe Habib yaji wani irin nishi da sauri yabude ido ganin gari yay haske yasa ya kalli katifar ta da sauri ganin Ya Faty kwance tana wani irin nishi kaman wacce ake fizgema numfashi yasa yawani irin kwala ihu. "Ya Faty!!!" yatashi da gudu yay kanta, ganin jini akan gadonta yabaci jikinta yabaci Ya Faty dabaka ganinta babu hijabi amman wanan karin zaninta wuri guda, yar under skirt dinta baki iya cinyan ta ne kadai yarage ga fararen cinyoyinta sun baci da blood yasa Habib ya kwalama Mama kira. "Mama! Mama! Baba! Babaaa!!" dawani irin sauri Abba yadiro daga gado dagashi har Maman suka fito jin yanda Habib ke kwala musu kira, Abba ne yariga shigo dakin Mama biyeda shi, kafinma Abba yay magana ganin Fatima yasa yay kanta da sauri yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, maiya sameta Habib? Ke Zara'u, Zara'una Baba"? Gabaki dayama batasan inda kanta yakeba daukanta Baba yayi yasata ajikinshi yana jijjigata yace "ke Zara'u, kallen, nine nine meke damunki"? Cikin kuka Habib yace "tun cikin dare naji kukanta, jikinta yay zafi tahanani tadaku ni bansan meke mata ciwo ba" dagokai da sauri Baba yayi ya kalli Ruka dake tsaye inda take yace "Ruka huramin wuta kisa ruwa tai wanka mutafi asibiti" hararan shi tayi tace "ai hala kasayo itace ne" da sauri yace "to saman mini awajen makota dan Allah" tsaki tayi tace "kaima kasan abinda banyi kenan rokon makota saidai ni suzo suyi maula wajena, Um ni kaga tafiyata ku karata" tawuce tasakin musu labule tai gaba abinta, rasama abinda zaiyi yayi ganin haka yasa Habib yace "bari naje wajen Maman dadi" "yauwa Habib" da sauri Habib yatashi yafita bucket yadauka yay kitchen din gidansu wajen wata mata dake kitchen yaje direct cikeda tashin hankali yace "Maman Dady dan Allah ki tsammana ruwa Ya Faty batada lpy wanka zatayi mutafi asibiti" da sauri Maman Dady tazuba mai aroba tace "ayyah Allah bata lpy" karban ruwan zafin yayi yaje bakin rijiya ya sirka ruwan yadauka yakai bayi sanan yadawo daki, lokacin daya shigo yaga har lokacin tana jikin Baba daidai tabude ido, ahankali Baba yace "meke miki ciwo Zara'u"? Murya chan kasa tace "ciki da kai" Habib daya tsaya kansu yace "Baba nakai ruwan bayi" ahankali Baba yace "zaki iya tashi tsaye ki chanza kaya"? Gyadamai kai tayi tashiga kokarin tashi da taimakon Baba da Habib tamike tsaye, zani Baba yanemo mata yasamata a hannu yace "cire kayan ki daura wanan saiki kirani zomu fita mubata wuri Habib" fita sukayi shida Habib dakin Mama ya shiga yasame ta zaune tana bama Abida nono, cikeda damuwa yace "dan Allah zoki taimakawa yarinyar nan tai wanka kinga suma taketayi Ruka" wani kallo tamai tace "gaskiya kayakuri amman bazan iyaba kuje chan ku karata" jin karan fadin abu timm yasa dagudu daga Baba har Habib sukai dakin itane tazube akasa asume tacire kayan amman bata gama daura zanin da kyau bama. "innalillahi wa innailaihi raji'un kawomin ruwa Habibu" Baba yay maganan yana daukanta yana gyaramata daurin zanin tareda fitoda ita falo, daidai Habib nakawo ruwa, shafa mata a fuska yayi ta farfado kaman zai mata kuka yace "sannu kinji, Habib biyoni da soson wanka" tama kasa tafiya daukanta Baba yayi har zuwa bakin bayi yama rude yarasa yanda zaiyi kallonta yayi yace "zaki iya wanka"? Gyadamai kai tayi idanunta dabasa buduwa da kyau, da sauri Habib yace "Baba wlh bazata iyaba kartaje tafadi tasume abayi" hayaniyan su da Maman Dady taji yasa tafito daga kitchen ta zagayo hakanan tanason Fatima sabida natsuwa da kunya da girmama na gaba da ita, tana kallon jikin mahaifinta yanda yabaci da jini tagane meke damunta tace "assha sannu Fateema, kawota nan Baban Habib bari natayaku" da sauri Baba yamika mata Fatyma, karbanta tayi ta shigar da ita bayi babu ko karfi daya ajikinta, sanan ta turo kofan tsayawa Baba da Habib sukayi suna jiransu, basu wani dadeba Maman Dady tafito da ita tace "dauketa Baban Habib zata iya zubewa Allah yasawake" da sauri Baba yadauketa yace "nagode Allah ya sakada alkhairi" wucewa da ita Baba yayi shikuma Habib yadauki bucket da so so Maman Dady tabisu da kallo bakaramin tausayin Fatyma takeji ba, daga ita har Mahaifin nata da aka gamada shi, bata shiga harkan Maman su sabida wlh zata iya mata dukan tsiya kan fatyma dan arayuwanta ta tsani zalunci, tadade tana tunani saikuma kawai tawuce ta shiga dakinta, always ta dauko tasaka a leda dawasu sababbin pant da mijinta yasayo mata na jegon Dady dabatai amfani dasuba dan sunmata kadan, kullewa tayi a bakar leda, sanan tafito tai sallama gaban dakinsu fitowa Habib yayi bashi tayi tace "gashi kabama Baban ka yabama Fatima" karba yayi yakoma ciki itakuma tawuce abinta.
Chapter 5 · 0% Book details