← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 104

Sashe 72

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin karan tana wanke wanke yasa Mum ta kalli Granny tace "Hajiya kinga wanke wanke take akwai mai aiki fa" murmushi Granny tayi tace "ki barta, aikin nan datakeyi zaisa ta watsake" gyara zama Dady yayi yace "ina credentials din nata"? Jakanta dake kan kujeran datake ta dauka tacirosu a file, sanan ta bashi ya karba yana dubawa, yace "yes tanada waec dinta tsaf duk taci science courses din, saidai batai jamb ba" anatse Granny tace "ai akwai schools din dazata iya farawa kafin next year yazo tayi jamb intaci saita fara University, inason nai keeping nata busy ne" gyadamata kai yayi yace "akwai friend dina dake running Private Health School, though anriga anyi admission, zan bashi inyaso saiya bata any course taje tafara, but dole a hostel zata zaune" dasauri Granny tace "a hostel"? Gyadamata kai yayi yace "eh, most health schools lectures dinsu suna farashi very early everyday, sanan suna karatu harda na hauka, kinga kuma wanan dasun fara lectures definitely ana bata admission dole tazauna tai karatu sosai dan an wuceta, kibarta tazauna a hostel din babu abinda zai sameta babban school ne sosai achan karshen Abuja yake, inyaso duk Friday zamu dinga tura direba yana daukota tai weekend agida, ranan Monday da sassafe takoma" kallon Mum Granny tayi tace "ke Mamarta to kin yarda da shawaran mijinki"? Murmushi sosai tayi jin karan da Granny tamata tace "eh na yarda duk weekend zata dingayi agida Hajiya, kinga yanzu idan taje tana xama a hostel cikin student zata waye ta kile, sanan tadage da karatu duk wanan kunya da kas kallon mutane zata dena, idan yaso 1week din dayace mubashi zamuyi amfani dashi mu mata siyayyan school dakuma dinkuna ko Kaka, ni akwai ma wasu atampopina dazan bata" sanan tajuya ta kalli mijin tace "Dady zaka bamu kudi muje muyi shopping ko" gyadamata kai yayi yace "gobe tunda Saturday ne ba work saiku je dukanku" murmushi duk sukayi Granny tace "Allah yamuku albarka, shikuma lukuti na yaushe zasuyi hutu yadawo gida"? Dariya duk sukayi Mum tace "just last week yakoma sunyi resuming first term, shida dawowa gida ba yanzu ba saidai mujemai visit, Granny yasu Dr mara kiran mutane" dariya tayi tace "wanan ai kinga halin mijinki yadauko dan haka karma kiga laifin jikana ehe" dariya duk sukayi daidai Zara tafito rikeda hannun Amna, Mum tace "sannunku to da aikin daban sakaku ba" sauke kanta tayi Granny ta tashi tace "bari muje muyi wanka muyi salla, muje Zara" bin Granny sukayi suka wuce suka fita Mum tabi Zara da kallo, sanan ta kalli mijinta bayan nan tace "Dady wlh na tausayama yarinyar nan sosai at her age dai taga rayuwa" murmushi kawai yayi yace "such is life kowada kaddaran shi, dazaran tafara school tasaki jiki zata manta dakomi and move on" gyadamai kai Tayi tace "hakane" sanan suka cigaba da hiransu.

Bangaren Granny shima hadadde ne agidan, amman shi ba duplex bane sabida rashin lafiyanta bata cikason hawa bene ba, but hadadden flat ne nagaske, ga durmemen TV afalon da speaker, ga kitchen ga dinning, saikuma wani corridor, da dakuna uku keciki, daya daga cikin kofar dakunan tabude, hadadden dakine ga gado da aka gyara royal bed, ga sip din bango, ga bayi ga ac ta kalli Fatima tace "wanan shine dakin ki, kinaso ko kinason achanza miki wani abu"? Dasauri ta girgixa kai tace "inaso, Allah saka da alkhairi Baaba" bayanta Granny ta shafa tace "kidinga kirana da Granny kinji, yanzu shiga ciki kije kiyi wanka akwai komi abayi kihuta, kekuma kibarta tahuta" tai maganan tana kallon Amna dake rikeda hannunta, raurau da ido tayi zatai kuka da sauri Zara cikin sanyin muryanta tace "dan Allah kibarmin ita Granny" murmushi Granny tayi tana kallon Amna dahar lokacin shirin kuka take tace "shikenan to" hakan yasa tafashe da dariya tanajin dadi, Granny tace "toku shiga" shiga sukayi suka maida kofan suka rufe itakuma Granny tasauke ijiyan zuciya tawuce tashiga nata dakin.

Haka ranan tawuni ko kadan Amna bata barta tahuta ba, surutu surutu, bata barta tai tunani ba, ta makala wayanta a chaji tanata kallon wayan har cikin ranta taji dadin wayan dan bata taba wayaba sai wanan, bayan Magrib suka wuce suka tafi flat dinsu sukaci abincin dare as usual tasake gyara dinning tawanke kwanukan dasukaci abinci dashi sanan Amna tajata sama zuwa dakinta tadinga mata surutu, sai wajajen 10 sanan Granny tamike ta kwala ma Zara kira, saukowa sukayi still Amna namakale da ita, ta kalli Mamanta tace "Mum ni i will sleep in grandma's place" tabe baki Mum tayi tace "agais dakansu zasu kadoki parrot" binsu tayi suka wuce side dinsu duk suka shiga Granny ta kulle kofan falo takashe wuta sukai balcony sanan tabisu har dakin Fatima tace "makesure kinyi wanka sanan kiyi nafila saiki kwanta kinji Zara, gobe zamu sayo harda kayan bacci" gyadama Granny kai tayi, sanan Granny ta kalli Amna tace "tsabagen azarbabi bamaki riko pajamas dinki ba" bari nakira Babanki yakawo miki" Kaka tai maganan tana fita zuwa falo itakuma ahankali Fatima tabude bayin ta shiga, dayake yanzu tasan kan irin bayukan yan gayun nan sabida xaman lagos yasa ta kunna heater tafito ta kalli Amna tace "zomuje namiki wanka" dasauri ta tashi riganta tacire mata tana kokarin cire mata pant Granny tashigo rikeda kayan baccinta, sanan dawani kayan baccin a leda tamikama Fatima tace "ungo kema Mum dinki ta aikomiki da sabo" murmushi tayi ahankali sanan takarba tace "thank you" Granny tace "kina gama komi ki kashe wuta ki kwanta" gyadama Granny kai tayi ahankali, Granny tace "saida safen ku" atare suka mata saida safe, sanan tawuce bayi ta tahada ruwa tamata wanka da hadadden shower cream din dake bayin sanan suka fito ta shiryata cikin kayan baccinta ta kwantar da ita akan gado taja bargo tarufa mata ahankali tace "nima bari naje nayi" bayin tawuce tai nata wankan da ruwan zafi sosai tana karajin dadin jikinta sanan tadauro alwala tafito daga bathroom din tana kallon Amna dataga tai bacci, dan murmushi tasaki taje tabude kayan baccin, normal pj ne dogon wando da riga mai kamada t-shirt amman gajeren hannu yanad taushi sosai, hijabin dake kan sallayan tai tahau tai nafila sanan ta tashi ta linke dadduman takarasa takashe wutan saiga hasken wayanta dakuma ringing atare hakan yasa ta kalli screen din wayan dataga an rubuta Imam ajiki.

_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu

Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp

_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHuMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
7/6/21, 11:57 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

✍� M SHAKUR

EPISODE 5️⃣7️⃣

Saida gabanta yafadi dasauri takarasa gudun kar wayan yatada Amna tazare wayan daga chargy tama rasa mezatayi kawai tadaiga tai picking call din taga alamun yana kirga mata secs, ahankali takai wayan kunnenta tai hannunta nabari jin shiru yasa tacire wayan ta kalla ganin har lokacin call din nanan yasa takara kai wayan kunnenta ahankali tace "h......hello" tai maganan tana tashi ta kwanta akan gado ahankali tanajan bargo tana rufe kafanta, dan lumshe ido yayi yana gyara zama akujeranshi na office dan night yake, ahankali yace "Fatima" murya chan kasa kaman mai tsoron magana tace "uhm" saikuma tai shiru jin yayi shiru yasa ahankali tace "ina yini" ahankali shima yace "ya hanya? Kukai lafiya"? Murya chan kasa tace "lafiya lau" saikuma suka sakeyin shiru for so long hartana ciro wayan daga kunnenta ganin still call din is on yasa murya chan kasa tace "Thank you" ahankali taji yasauke ajiyan zuciya yace "for"? Alamun tambaya dan yanaso yasatai magana, only magana ne zaisa tasaki jikinta ta manta d past life dinta, murya chan ciki kaman tana tsoronshi tace "for bringing me to Baaba" tai shiru saikuma ahankali kaman tana shakkan fadi tace "and for giving me a family" murmushi yayi dahar saida taji sautin murmushin yace "you are welcome Fatima" suka sakeyin shiru saikuma chan yace "kinga Baffa na, da Mum da Amna" murya chan kasa tace "eh" saikuma chan tace "sunada kirki" dan murmushi yayi yace "ina Amna"? Ahankali tace "gatanan" murmushi yasakeyi yace "I guess kinyi sabon kawa kenan, saikin gaji da magana" dan murmushi kadan tayi dayasa yaji dadi dan yaji sound din murmushin, ahankali yace "take care, jeki kwanta" kaman yana ganinta ta gyadamaikai sanan ahankali tace "nagode Ya Imam" lumshe idanu yayi sanan yabude su ahankali tareda katse wayan.
Chapter 72 · 0% Book details