← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 104

Sashe 46

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rarrafe tafara tajawo basket na kwashe kayan dattinshi ta shiga tattarewa tana sakasu a basket din tana kuka sosai mara sauti ko kadan, saida tagama tattare kayan tass sanan takama bathtub dinshi zata mike tsaye dan ihu tayi mai kara takoma ta tsugunna da gudu sabida yanda kirjinta yayi, lallabawa tayi tai kaye kayen bayin a tsugunne batare data iya ta wanke bayin ba, takara jingina da bango tana nishi sama sama, saikuma ta daura duka hannayenta biyu akan fuskanta kaman mai addu'a ta shiga kuka sosai, ita karan kanta she don't know abinda zatama kanta kirjinta ya daure ya rike, maranta ya rike, asalin kirjinta na mata zafi yana mata ciwo kaman wacce keda matsalan ciwon kirji na ulcer, ganin koma menene gwara tabar aikin taje dakinta ta kulle kanta tacire wanan silkin dake neman yasa numfashinta yadauke taita birgima akasa tana jinyan kanta da dandan sarki yagano wani abu game da ita anan, tun yanzu gwara tafice kafin ya farka daga bacci, tunanin haka yasa da rarrafe tazo ta murza hannun kofan sanan ta rarrafo tafito batare data kallo cikin dakinba ta daga hannu zata kama handle din kofan ta maida kofan tarufe kenan taji muryan prince yace "Boyy" awani zabure tajuyo ta kalleshi suka hada ido yana zaune bakin gado, ihun datayi abayi yatadashi yatashi ya zauna sai gashi kuma tafito, ganin yanda yake kallonta ganin rarrafe take yasa dawani irin sauri ta yunkura zata mike kirjinta yawani amsa yakafe kaman takasa wani igiya na kirjinta boobs dinta suka shiga mata wasu irin unbearable zugi, numfashinta yawani rike kaman mai asma takasa numfashi da kirji tafara wani irin neman numfashi tana wani irin nishi tana kokarin faduwa kasa kaman mai asma, da sauri Tobi yatashi yace "Boy!!!" Kafin yakarasa ta idasa zubewa flat akasa agaban bayin tana wani irin bude idanuwanta kaman wacce ke shirin mutuwa tana yi yi yi yi yi..... tana wuntsila hannu trying her best to breathe but takasa, dawani irin sauri yadagota yariketa yasa kanta kan cinyanshi yana kallon idanunta dasuka bude sosai tana kallon sama yace "Boy dama u are asmathic ne, do you have inhaler? Subhannallah whats wrong with you Boy" yay maganan yana gigixashi, da kyar idanunta suna neman kullewa tai grabbing hanannunshi tana kallon sama har lokacin takai hannunshi_ tai placing akan chest dinta tawajejen boobs dinta trying to tell him ya kwance mata abin nan karta mutu, karta mutu.
7/2/21, 9:10 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍🏾M SHAKUR

EPISODE 3️⃣3️⃣

Kallon fuskarta yayi sanan ya kalli inda ta daura hannunshi sabida kaman yaji dan tudu da alamun wata kalan fata dabata jikin mutum ba akirjin nata, sanan yasake kallon fuskanta yanda lips dinta ke kokarin motsi amman takasa gayamai metakeson cewa, takasa furta maganan datakeso tayi tana wani irin nishi idanunta na kullewa suna neman kafewa tana bubbuga hannunshi dake inda ta daura tana kokarin nishi takasa, dawani irin sauri ya daura hannunnashi kan kirjinta da kyau trying to understand abinda boy din is trying to tell him ya shashafa kirjinta tundaga ciki har wajen boobs din but baiji komiba sai fata wacce take kaman fatan takalmi ba fatan jikin mutum ba, saikawai yadage black rigan dake jikinta sama gaba daya zuwa wuyanya yaga wani brown silkin doki da yardin mai bala'in kauri da nauyi daure ajikinta tai wrapping kanta dashi, kirjinta ya kullu ya tamku gam gam da daurin dayaga kaman shiya hanata nishi danta daure kanta dayawa ahakama yana ganin yanda chest dinta ya matse, dawani irin sauri ya shiga kwance kullin kafin tashi daya dawani irin karfinshi na namiji ya fizge silkin futttttt yawani cillar sama daidai manya manyan boobs dinta dasukai jajir abunku da fara suka tamuke tsabagen kullesun da akayi suka bayyana before his eyes, dawani irin sauri yasaketa gabaki daya akasa yakoma baya kadan tsabagen shock!!!.

Wani irin nishi tayi tareda juyawa gefe ta kwanta ta side dinta har lokacin tana wani kalan nishi that is very strange dan numfashinta bai dawo daidaiba saikuma amai, waaaaaa ta kwaro aman duka biscuits da chocolate din dake cikinta tun jiya anan kasan carpet din tana wani irin nishi kaman ranta zai fita. Da sauri yatashi batare dayay komiba kawai key motarshi ya sunkuta yazo inda take take nishin har lokacin bata denaba dan she's really finding numfashi difficult, hannunta yadaga yakamota ta taho luuuu babu karfi kodaya ajikinta tai yaushi, kumatunta yabaci da amai harda kunnenta, kulle idanunshi yayi gam sake ganin boobs dinta akaro nabiyu dayayi, sai kawai yakai hannu yaja riganta daga wuyanta zuwa kasa ya dauketa kaman wata yar jaririya tai lakur akirjnshi ko'ina nata na lilo iska na kadashi sabida tsabagen rashin karfi, ko kadan bai damu da aman fuskanta daya share tass a kan pyjamas dinshi ba, yaki fuskanta ajikinshi ya rungume ta tsam ta yanda babu wanda zai gane wani abu gameda ita yawuce yafita hatta fuskanta nakan kirjinshi, ya sauko kasa da ita yana mamaki yanda ko kadan batada nauyi kaman ya dauki paper, sanan yakarasa yabude kofa yafito guards dinshi duk suka zube akasa suna gaidashi suna kallonshi sabida yanda sukaga ya dauki Boy a hannunshi dudda basa ganin fuskan boy din sunsan shine dan fuskanshi na kife a kirjinshi sai kafafunshi dake lilo akan hannunshi ko amsasu baiyi ba yawuce wajen motarshi baya yabude ya shimfideta abaya har lokacin tana wani irin nishi idanunta na juyawa, sanan yatashi ya maida kofan yarufe yakoma gaba da sauri yatada motar yafice lokacin babu wanda yatashi a family su danko 8 nasafe bataiba, yaja motar yafita daga gidan, agaban wani private asibiti yay parking yafito yazo baya yabude yadauketa chak yana kallon fuskanta har lokacin yay cikin asibitin da ita yana shouting Dr, Dr, wasu nurses dawata macen Dr dasuka fito daga wani dakine suka tareshi tanakan jikinshi likitan takai yatsunta wuyanta sanan tai ihu. "Get a bed her pulse is very weak" turo gado sukayi da sauri ya sauke musu ita akai ya kwantar da ita sanan Dr tace "just stay here, who are you to her"? Shiru yayi yakasa magana Dr tawuce tabisu ciki da sauri tana gyara stethoscope din dake hannunta tana makalawa a kunnenta.

Ahankali yasami waje yazauna yay shiru he don't even know what to think idan yace "a girl" saikuma da sauri yace "no he's a Boy, kawaidai hala yana growing breast tissues ne due to small health related condition, tsoron stigmatization daga mutane yasa yake kullewa yana boyesu" saikuma yace "how?" Shiru kawai yayi ya dakatar da tunanin yana zaune awajen har almost 2hrs saikuma Dr tafito kallo daya tamai tadauke kai tace "follow me to my office" tashi yayi kaman wani abu yamutu acikinshi yatashi yabita ahankali, yana shiga yasameta a zaune hakan yasa yamaida kofan yarufe yajuyo ya kalleta, cikeda fada sosai tace "kuna kallo sister ku na neman maida kanta Tomboy kunyi shiru kun kyaleta" dan ware ido yayi yana kallonta yana kokarin maimaita abinda Dr tafadi cikin harshen turenci dayamai kaman baigane ba tsabagwn yanda tai maganan, sister? Saikuma tacigaba da masifa tace "wanan wani irin musiba ne yasami Nigeria, mata naso su koma maza maza naso su koma mata irin su Bobrisky, James brown da sauran su, how could u allow this girl small girl that i don't even think she's up to 20yrs tana neman tamaida kanta namiji eh?" Ahankali yace "a man, a girl"? Sounding so confuse, gyadamai kai tayi with full assurances tace "yes, though dai banga asalin abinda ta kulle breast dinta dashi ba, but her breast sun matse iya matsewa, kanta tasaka bald cap damuka cire yanzu kaji yanda kanta ke wari infact I told d nurse su tsefe kitso su wanke kan kafin nazo namata suction, tissues din breast dinta ta matsesu sun danne suna neman hadewa with her chest wall saisa she was having serious problem da breathing, wlh idan dabaka kawota dawuri ba ko bata cire abinba dasaita mutu tass cikin few minutes, dole we have to do suction for her mufito da boobs dinta back to normal shape dinsu muyi freeing any tissue and veins na nonon yadawo yanda yake ada, yanzu everything ta mannesu nonon yafara building block of blood da yanzu idan muna suction zamu narkar dasu" ahankali Tobi dayay mutuwan tsaye yakasa koda motsi yana kallon Dr dake koromai bayani, yace "is she a girl are you sure"? da sauri Dr tace "yes she is, why am I a Consultant idan I cant differentiate man from a woman? Infact she's even on her period, abinda duk yakara mata ciwon kenan, tana having serious menstrual pain, though yanzu mun mata allulori" wani irin fadawa kujeran dake wurin yayi yazauna yama rasa mezaiyi kome zaice, ahankali Dr tace "baka santa bane" murya chan kasa yace "I know her just that all this while I thought...." yakasa karashe maganan, Dr tace "you thought she is a man all this while" tabe baki Dr tayi tace "Allah ya shirya mana yaran this days, but abin babu dadin ji, babu dadin gani, me mata ke sha'awa akomawa namiji? Hakama me maza ke sha'awa a komawa mace? Inbadai so suke suma kansu illa ba da lot of complications babu wani abun kirki aciki, gashinan yanzu tana neman kashe kanta yanzu wahalan dazata sha saiyafi karfinta na suction din dazamu mata sabida nonuwan sunyi tsami sosai tsabagen kullesu ko nanesu datakeyine oho, is like she has done that for a very long time, yanzu kirjin da nonon sunkai elastic limit dinsune saisa suka kasa jurewa, anyways go make this payment, suction kadai dazamu mata muna charging 250k for it, sai kudin magunguna da kudin bude mata kati da sauran su, idan kabiya sai mumata idan bamuyi ba kirjinta baxai dena ciwon nanba dayake yi, and xata dinga having difficulty in breathing" karban takardan yayi ahankali sanan yatashi yafita yana tafiya ahankali yakasa daina tunanin Boy macece, Boy wai, innocent Boy dayasani, he wants to see her yakara tabbatarwa yes mace ce, fita yayi yaje motarshi yana addu'a Allah sa wallet dinshi na ciki danbabu kosisi ajikinshi, yana ganin wallet din yadauka yaje yabiya kudin da POS sanan yakaima Dr takarbi komi sanan suka fito tare yawuce ya zauna.
Chapter 46 · 0% Book details