← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 104

Sashe 55

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHUMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR

EPISODE 4️⃣2️⃣

Jefi jefi yake dan satan kallonta, bata iyacin abinci ba but yanda takecin indomie zaisa ranka yabiya gashi sunyi dogaye tana jansu everything datayi looks damn cute and childish to him kodan baida kanine saisa yake ganin abinda takeyi yana shiga idanunshi oho, tashi tayi tawuce kitchen din saikuma tafito tataho wajenshi kasa daurewa yayi karya kalleta yajuyo yazuba mata idanu harta karaso gabanshi ahankali tace "banga knife a kitchen ba" danjim yayi saikawai yatashi yace "am coming" binshi da kallo tayi yawuce sama saikuma ba'a jimaba yadawo da wuka gda daya yamika mata yace "be careful" gyadamai kai tayi ta karba tawuce kitchen, fridge din kitchen din tabude, Allah ma yasan tanason girki duk in suka hadu da Maryam ta karbi wayanta Facebook take zuwa direct tana kallon videos ma girki, wani spaghetti datagani takeso ta dafamai, dako tabude fridge taga akwai komi na girkin ita tana mamakin yanda suke dumping kayan girki a fridge kaya harsu gaji dayin kankara basa dafawa, kifi taciro saidin guda biyu ta ijiye tana jiranshi kankaran ya narke sanan ta wanke hannunta ta shiga slicing su Ball peppers, yellow green da red sanan tafara wani irin girki.

Yana zaune a falo but kamshi ya isheshi hakan yasa kawai yatashi he want to see what this small girl is doing dayake shiganmai hanci haka, agaban kitchen din ya tsaya ya rungume hannunshi yana kallonta uta kadai sai murmushi take tana girkin kana ganinta kasan she drives happiness in cooking, indai hakane koda jagwalgwalone zai dinga barinta tana dafawa just so that she will forget everything and smile like this, yana tsaye awajen yaga takashe gashi din tagama saman yaga ta juya tana kallon wani cabinet da anan taga an jera plates da tray konata ma mai gadi yaciro mata dan yay tsayi kuma batada tsawo. Shigowa kitchen din yayi da sauri tajuyo ta kalleshi daidai inda take yazo ya tsaya ta bayanta yace "wat do you need Miss Chef" wani irin washe baki tayi tamai murmushi this is the second smile datakemai bayan na lokacin dayakira mata Baba, chak ya tsaya yana kallon fuskanta smile dinta yay gripping heart nashi staring at his small small set of white teeth, her pink lips da dimples dinta. "Plate with a tray" data fadi yasa yadawo hayyacinshi ahankali yamika hannu dudda shima saida yadanyi dage dan bawani tsawon azo agani yakeda shi ba sanan yaciro yabata yawuce yafita, wankewa tayi tashare ta tsane ruwan jiki saman tazubamai abincin that looks yummy and inviting yaji kifi, sanna tadaura a tray ta ijiye a gefe, juice data hada na apple da cucumber tasaka a fridge tadauko ta daura jug din da mug akan tray din sanan tafita dashi harzuwa inda yake zaune a falo ta tsugunna tadaura akan stool sanan tadan dago kanta hada ido sukayi ahankali ta tashi tawuce kitchen dan gyara komi, abincin ya kalla sanan ya kalli juice din dat look a lil bit greenish shidai baisan dame akayiba, baison yaci abincin dan shi idan yana Nigeria abincin mamanshi kawai yakeci, but tunanin dayayi idan baiciba she will feel bad bayan shitamai yasa he just decide bari yayi koda one spoon ne, fork din wajen yadauka yadebi taliyan datai kyau bata wani nuna tai lugub ba taji su carrot da peas ga kifi yala yala yakai bakinshi ahankali dan ware ido yayi tastebuds dinshi sukai motsi danko hasidin iza hasada yaci abincin yasan yay dadi, cewa yayi bari yakara one more spoon kartaji haushi baiciba ahaka yatada abincin nan tass, shida baicin abinci dayawa saida yatake duka abincin harma kari yake nema sanan yadebi juice din mai sanyi yakai baki Omg baitana shan juice mai dadi irin wananba, is so refreshing and calming kanasha zakaji yana ratsa ko'ina a brain dinka da heart, OMG he enjoy every bit of this food wlh, gashi babu karnin kifi ko kadan, yakasa daina murmushi sai mamaki yake shine yaci abinci dayawa haka dudda yay breakfast agidan su Ayoka dudda tea kawai yasha. Shiru yayi yana tunani duk idan su Dami sunyi girki koda babu dadi inhar Dady zaidau spoon yaci koda one spoon ne saiya musu kyautan kudi dudda baisan menene the technique behind the money ba samin kanshi yayi da tura hannunshi a aljihu luckily yanada wrap nayan 500 sababbi fil yarike kudin a hannu yana kallo daidai lokacin tafito daga kitchen tagama gyara kitchen din, ganin yagama cin abincin tmya cinye tass juice dinne yarage kadan yasa ta taho ahankali gabanshi ta tsugunna tadauki plate din tasa a tray da jug din da mug zata dauki tray din ta tashi yamiko mata kudin, da sauri ta kalli kudin saikuma ta kalleshi murya chan kasa yace "take" ahankali tasa hannu ta karba jin yayi shiru yasa tasake kallonshi taga yamaida fuskarshi kan TV, ahankali tace "the money is for what"? Batare daya kalleta ba yace "for Za.....raaaa" sake kallonshi tayi looking a bit confuse, ahankali yajuyo yazuba mata Idanunshi sanan ahankali yace "thanks for the food, is amazing" samin kanta tayi dasakin wani irin murmushi da sauri yadauke kai murmushin ta nasa zuciyanshi yabuga he don't even know, kallon kudin hanunta tayi tagane tukwuici yabata na girkin datamai, ahankali ta tsugunna cikin siririyan muryanta da hausa intonation dinta tace "Sir the money is too much, I can't take it" batare daya kalleta ba yace "you can throw it away i don't care" shiru tayi kanta na kasa, saikuma ahankali tace "thank you Sir, May Allah bless you" samin kanshi yayi da dan lumshe ido sanan yabudesu yaga harta tashi tadauki tray dakomi tawuce yabita da kallo harta kusan shiga kitchen kaman daga sama taji yakirata ahankali kaman baison yakirata. "Zaaaaa.....raaaaaa" idan yakirata kaman yaron dabai iya kiran sunan ba dan saiya raba sunan gida biyu kowanne yaja hakan saiya karama sunan wani irin dadi, tsayawa tayi chak sabida yanda gabanta yafadi takasa juyowa batasan mesaba, chan kasan makoshi yace "you are a good cook keep it up" sake murmushi tayi tawuce kitchen, ijiye kudinta tayi a gefe sanan tawanke komi ta kifa kafin tafito tai hanyar stairs rikeda kudinta, daki tashiga tazauna agaban gado tana taba kudin 500 sababbi kal kal, tunda take bata taba ganin kudi masu yawa haka a idoba, zata boye taba Baba idan takoma gida, da sauri wata zuciyan tacemata Baba? Wani Baban wani gida kuma? Har yanzu taki gasgata abin takuma yi alkawari zata nemi waya takira Baba daga ita saishi hala ranan ranshi abace yake saisa yagaya mata maganganu haka kwanciya tayi abinta tanata juya kudin kaman yar baby har bacci ya kwasheta kudin akan jikinta.

Wajajen 3 maigadi yadawo yacemai yadawo yatura kudin hakan yasa yaja motarshi direct zuwa gidansu, koda yay parking shida inba wani abu yakaishi ba shidai dakanshi baya daga kafa yaje fadarnan, yana shiga guards suka zube suna gaidashi Babanshi yabishi da kallo da waziri da sauran mutanen dake fadan, kusada Baban nashi yazauna batare daya gaida kowaba ashagwabe yace "Daddddd" washe baki Babanshi yayi yace "ya akayi OluwaTobi" kwantar da kanshi yayi a hannun Baban nashi yace "Dad I just feel like coming to your place and do this" gyaramai hannun yayi da kyau tareda shafa kanshi daidai lokacin guards suka shigo da wanan babban lawyer dan tsohon nan yana sanye da suit, Otun na ganinshi yace "kubarshi" shigowa yayi ya kwashi gaisuwa, Otun yabama sauran mukarraban fada sufita daga dakin, hakan yarage dagasu sai lawyer da Tobi a fadan, Otun yace "meya kawoka nan"? Ahankali yace "actually Sir daga gidanka nake akaxe kana nan" Otun ne ya kalli Dad yace "this is the head lawyer representing the north, sanan shike handle account din biyan bashin yan north" gyadakai Dad yayi yana kallonshi yana shafa kan Tobi dake hannunshi har lokacin. Otun yace "meya kawoka" laptop mutumin yashiga budewa yace "Sir anbiya kudin daya daga cikin yaran dasuke aiki anan dazunan bada dadewaba the sum of 3million naira ya shigo account dinmu" gyadamai kai Otun yayi cikeda gamsuwa yace "that's nice wani yaro kenan" sake daddanna laptop din yayi yace "Khalid Muhammad shine yaron da aka biyamawa" da sauri Otun yakira sarki yace "wow that's Tobi errands boy" da sauri Sarki ya kalli Tobi yace "Son anbiya bashin Errand boy dinka" tashi zaune yayi saiya yatsine fuska yana kallonsu baice komiba. Otun ne ya kalli Lawyer yace "call the father yafada maka yaushe za'a aika mishi da danshi" gyadamai kai yayi sanan yay dailing number shi daya dauka daga computer under details na information dinshi sanan yakira Baba.
Chapter 55 · 0% Book details