← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 104

Sashe 74

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE 5️⃣8️⃣ & 5️⃣9️⃣
Shopping sukaje mata mai suna shopping ba muna shopping ba, sun saimata tsadaddun kaya kowani atampa ko lace ko material zasu saimata saisun sayamata gyalenshi da takalmi da jakanshi, jaka irin na yan mata ba manya manyan nan ba hadaddun gaske, gyaluluwan ma na yan mata medium itadai binsu da ido take Mum da Grandma ganin basu siyamata hijabai ba, manyan akwatuna suka saimata na kayanta na lv, sanan akaje bangaren undies aka saimata bras size dinta da pant da kayan bacci but irin decent kayan baccin nan dazaka saima yarka mace yawanci masu dogayen wanduna, saikuma masu short wanduna iya guwiwa da gowns, saikuma suka sainata abaya kala biyar awajen UMNA ABAYA, hadaddu sanan suka gama shopping kayan sawa, saikuma akaje bangaren school materials hadadden school bag na goyo, math mathset, calculator, jakan byro da pencil, sanan suka saimata mattress size na gadon makaranta, buckets plate spoon babu abinda basu saimata ma har jeep dinsu yakasa kwasa saida suka hada dawata motar haya dasukai shatta, sanan Mum ta tsaya tasai musu ice cream itada Amna da some other pastries ko saloon din barinshi akayi dan 3 tayi suka tafi gida, aka sauke komi gateman na kwasansu zuwa bangaren Granny, duk suka tafi ciki sukai salla sanan saiga Mum tashigo bangaren Granny, Granny kadaice a falo tanajan charbi Mum tace "Granny ga telan nan zuwa" ko gama fadi baiyiba taji ana sallama mai gadi zai fadi bako yazo tafita tace "ashigo dashi" shigodashi akayi har side din Granny, sanan Granny ta kwalama Zara kira, Auwal Tela shine maima gidansu dinki baya wasa dasu dan suna biyanshi biya na haukama saisa dazaran Mum takrashi yake zuwa, Zara tanunamai tace "Auwal y'ata nakeso ka dingama kaya, nasan kayan dayawa bazaka iya gamasuda wuriba but please kayi dayawa this week sabida makaranta zata tafi idan kagama sauran saika kawo suma" da sauri yace "to Hajiya" Mum tanunamai Zara tace "aunata, kowani kaya kamai style din daya kamata idan riga da skirt ne kokuma doguwan riga kawai kafitomin da yarinya" dasauri yace "angama hajiya" tape dinshi yafito dashi daga aljihu sanan yazo inda Fatima take ya shiga aunata yana rubutawa a book saida yagama tass sanan Mum tace "kawomai kayan Zara" fitoda manya manyan jakunkunan tayi one by one guda biyu dake cikeda kaya Auwal ya karba, Mum kuma tabashi 100k tace "kafara" har kasa yayi yana godiya yace "nagode Hajiya, sai anjiman ku" yawuce yafita yana murna sosai, Zaara kuma itama ahankali ta tsugunna gaban Mum da Granny dake zaune kujera daya tace "Granny, Mum, nagode dakomi Allah yasaka da alkhairi" kanta Mum tashafa tace "kidena min godiya, idan Babanki dai yadawo kije ki godemai".

Ance wayansu bala'u nafaruwa dakaine idan akwai alkhairin dazai faru dakai, yanzu Fatima take ganin ashe zata taba haduwa da mutane dake sonta haka, Mum tamaida Fatima kaman yarta kuma bawai sone dan taga Granny ba kodaya sone kawai Allah yadaura mata sabida taga yarinyar nada natsuwa gason aiki barinma girki, saisa duk rand zatai girkin yan gayu zata aika tazo suyo tare dan taga yanda zatayi Granny kuma bakaramin jin dadi tayiba, tuni Auwallu tela yakawo mata dinkunanta about kala 15 agoge, da Mum tasa tagwada sun mata cip cip dadas ajiki takusan sumarda Auwalu dakudi yakara mata alkawari nanda next week za'a gama duka.

Abangaren Imam kullum saiya kirata dare da safe yatadata tai salla, dudda bawani magana takemaiba but yakan tambayeta abu, Amna nason Zara ko abin kaman magic itama Xara nason yarinyar sosai, Kaka dai hankalinta kwance yanzu kawai Ibrahima suke jirada admission letter ta.

Karfe biyar yau Dady yashigo gidan parking yayi yafito, bangaren mamarshi yawuce direct, Granny yasamu a falo da matarshi suna hira ganinshi yasa sukai shiru da hiran dasuke Granny tace "kadawo Maza" akan kujeran datake yazauna sanan yabude file din hannunshi yaciro wani takarda da aka rubuta admission letter akai sanan yamikama Granny yace "amshi Grandma saiku shirya mata komi, ranan gobe da yamma zamu kaita makaranta sabida ranan Monday dasafe tanada class, anbata admission na national diploma a Health Information Management, sune suke managing all hospital record, suna coding and indexing, suna statistics da sauran su, idan tagama ND zata iya amfani da result din tai applying direct entry tashiga university idan kuma batason course din xata iya next year tasake jamb, but course din nada kyau shita samu" da sauri Granny tace "yo ai babu course din banza aduniyan nan, barinma bangaren lafiya data samu, Allah maka albarka Ibrahima Allah sa kagama da duniya lafiya" tai maganan tana bama Mum admission latter tace "yarki fa sai university, su Zara andawo yanmata" tashi Dady yayi yace "nasa anmata registration dakomi kawai kuhada kayanta gobe 4 saina kaiku, lemme go and shower" yawuce yafita sosai Granny da Mum sukai murna, Mum ta kwala mata kira. "Fatima, Zara Zara" daga kitchen ta ansa da naam sanan tafito tazo har gabanta, tana sanye dawata doguwan rigan atampa sabuwa dayay mata kyau sosai, tace "gani Mum" takardan Mum tamika mata tace "ga admission latter ki, ance ranan Monday kinada ma lectures gobe sai tafiya school" kaman amafarki taji ankira mata admission latter, saikuma ahankali tadaura idanunta kan takardan tamanta when was the last time tai farin cikin nan batasan lokacin data fada jikin Mum ba saikuma tafashe da kuka sosai tana "Mum nine zan fara school, university, Mum dan Allah da gaske kodai wata maisuna Fatima ce baniba" yanda take kuka tamakusa saka Mum kuka, itadai Granny tai murmushi kawai tana kallonsu, cirota daga jikinta tayi tace "kece Fatima bawata ba, wani private health school kika samu sun vaki health information management ND, shekara, biyu idan kika fara in bakiso kisake jamb next year, idan kin gama u can apply direct entry, idan kinaso zaki continue kiyi HND, so stop crying yanzu kin dawo university student ba secondary school ba kuma, now zakije daki kihada kayayyakin k tsaf a box, wanda auwalu yakawo miki, mukuma zamu hada miki su foodstuff, gobe dasafe sai muje saloon awanke kanan amiki kitso sabo kitafi school fess" gyadama Mum kai tayi tana murmushi sosanan tajuya ta kalli Granny dake kallonsu tai tagumi tana murmushi, sanan ta tashi dagudu tana share kwalla tana bama Granny admission letter din tace "Granny zan fara school" ahankali Granny tace "Alhamdulillahi natayaki murna diyar kirki" rungume grandma tayi zata sake kuka tace "nidai abinci na wuta" saikuma tai dariya tabata takardan tace "rikemin Granny" tawuce kitchen dasauri duk suka bitada kallo.

Saida sukaci abincin dare bayan tagodema Dad shima sanan suka shiga tayata hada kayanta a akwatunan dasuka saya mata, itadai Granny na zaune tana mata parking dambun nama a jars din dake wajen, daya cikeda cincin, daya da alkaki sai wanda ke hannunta datake zuba dambun nama ciki. Mum da Amna na hadamata kaya kowani kaya a set dinshi take saka mata a box da gyalensu, da kayan bacci sai wajen 10 da rabi suka gama komi sanan kowa yatafi daga ita sai Amna adaki, sanan tawuce taje tai wanka dan Amna tai bacci tai salla takashe wuta, tana kwanciya as usual yakira, dakata tayi ahankali tace "ina yini" murmushi yayi dataji sound dinshi tace "congratulations students, sai makaranta" murmushi tayi da shima yaji batare datace komiba, ahankali yace "idan kinje class on Monday, look for the most decent a aji ki karbi note dinta, either you snap kokuma ki ara ki kwafe abubuwan da aka muku, banda tara kawaye, keep your heads down, just do abinda yakaiki kina fitowa direct to the hostel, za'a sakaki a haddan su Amna, idan kika dawo gida on Friday, xaki dinga zuwa haddansu Saturday and Sunday kuna dawowa one, your life now will be very busy, just arrange and compose yourself anything dabaki ganeba idan nakiraki saiki gayamin, naso nazo this weekend but work yahanani, just take care okay" ahankali tamai nodding kai sanan tace "nagode" gyadamata kai yayi yace "toki kwanta tun yanzu you have alot to do gobe saida safe" gyadamai kai itama tayi tace "bye" sanan ya katse wayan ta ijiye ahankali agefenta tai shiru ko Allah yasan she is super happy akan makarantan nan, itama zataje school tafara karatu kaman kowace yarinya, but deep down she feels so empty babu randa bazatai tunanin Tobi ba, babu randa bazatai kuka da daddare ba sabida shi, she just wish xata iya ganin face dinshi kod sau dayane and tell him tasami admission zata fara school, ita kanta batasan meke damunta ba but she can't help yanda take tunanin shi, harji take kaman yadawo nan Abuja yay zamanshi kawai, duk idan ita kadaine afalo saitadau remote tasa tashar kwallo tadinga addu'a Allah sa taganshi a TV amman bata ganinshi, Granny intaganta atashar kwallo tace "kekuma taki kenan kina mace kwallo kike kallo a TV sabida kin rasa film, nidai sakamin kwana chasa'in" haka zata chanza, tunani kala kala da kuka ahaka tai bacci.

Dasafe shine yatadata still tatashi tai salla tai addu'a tafito ta gyara gidan ta kunna turare sanan tahada kari, saida tagama komi sanan tawuce dakinta tai wanka tafito tazauna tashafa sabon man da Mum tasiya mata daya karbi fatar jikinta sosai, sanan tasaka kwalli dayama idanunta kyau, tadauko wani riga da skirt na vlisco atampa da takalmin shi da gyale dan haka Mum tahada mata kayan, atamfan bakine da ruwan toka, hakan yasa gyalen yazamto mai ruwan toka sanan tadan fesa turare bodyspray kadai tafito, dayake Granny ne kadai da Amna yasa Granny tace "kallabin fa" zama tayi tace "idan zamu tafi saina daura" Granny tace "ni banjin zan bikuba fa sonake nai bacci nahuta anjima saina biku mu kaiki makaranta" gyadamata kai tayi, suka gama breakfast ta kwasa takai kitchen Granny tace "karki wanke wanken nan zata aiko yar aiki ta wanke kuku wuce ku tafi, Maman ku ta shirya, jeki dauro dan kwalin kidauko jaka kifoto" daki tawuce ta tsaya gaban mirror ta daura dan kwalin da kyar sanan tadau gyalen tayafa tanajin wani iri bata sababa sanan tasaka takalminta mai kyau flat tadauki jakan tasaka wayanta aciki tafito, tai wani irin kyau kaman diyar shugaba Buhari, hannunta Amna tarike tace "kinyi kyau Ya Zara muje Mum na mota" bye sukama Granny databisu da kallo tace "adawo lpy" sanan suka fice.
Chapter 74 · 0% Book details