← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 104

Sashe 2

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwance wani magidanci yake akan gado wanda duka duka bazai wuce 45 to 50yrs ba yana lullube da zanin gado yadaura hannunshi abayan keyanshi yana kallon fankan dake kadawa ajikin silin din dakin, kana ganinshi kasan yayi nisa a tunani gyara labulen kofan tayi ta tsige dan zanin datake daure dashi tahau kan gadon tadaga zanin gadon ta shige takai hannunta kan joystick din ta taba jin ya kwanta yasa ta kalli fuskarshi, turo baki tayi saikuma ta shiga mannewa cikin jikinshi sabida tasamu ta tayardashi sucigaba, cikin dan fushi yatureta kaman jira yake yace "Haba Rukayya ke ina cikin babban matsala bakida damuwa, kinjefani cikin matsalan keko ajikinki, kawai kin kirani gida baki barni wajen nemana ba kawai nazo gida naita miki wanan abin uwa banda wani aikin yi" yay maganan cikeda dan takaici, yace "wai sabida kinga ina sonki saisa kikemin hakane Ruka? Miliyan uku fa Rukayya ina naga hanyar miliyan uku yanzu iyye nanda sati daya zasu zo kuma, idan ban basu ba kinsan mizasuyi, kuma kekika turani naciyo bashin nan bakisa na tsinana komi dashi ba saidai kikasa nazo na kama wanan gidan hayan dayafi karfina, na saya miki kayan daki harda TV bango kikasa muka saya da fridge da katifun mu na daki yara da wanan rantamemen gadon dana siya miki kaman na amare, inda ace nai sana'a dashi da nasan inada at least wata hanyar biya amman bandashi kuma ko ajikinki, ke kawai daga safe har dare ki ganni manne dake kaman da tarayyan zamu biya bashi" cikeda kulewa tace "ya za'ayi kace ban damu da bashin da ake binka ba? Kanata wani cewa nasa ka kashemin kudin, naga aidai kaima kasai galleliyar machine wayyo kudina kana paparazzi akan titin gandujiyya, kai bakajin dadi yanda yan gidan nan suke bautamana mune yan uwan yan gayun gidan nan fa, yau taliya gobe farfesu, kullum ina jefar da ledan tsiren daka sayamin a tsakar gida suna gani, ga fridge ga TV, irin namasu kudin nan, kai bakaga yanda suke maula wajena ba, komi Maman Habib kai bakajin dadi? Babu abinda fa ba'a rokonmu, karka damu kudi zaizo zamu biya bashin sati daya ai akwai lokaci" cikeda fada yace "waini kika maida yaro Ruka? Tsafi zanyi dazan sami miliyan uku acikin kwana bakwai? Wai inama adashin dakika dinga karban kudin kina zubi kince min kwasa dubu dari biyu at least koshine nasamu nabasu wani abun" turo baki tayi tace "ni titini na kwasa nayi hidima da ita, nasoma yima Abida tari ne" wani kallo yamata yace "Abida ko Fateema"? Dauke kai tayi tace "nidai nasan kajini da kyau kakemin wanan tambayar Abida nace nafara ma tarin kayan daki, kana duba karkashin gadon nan zakaga abubuwan danasiya ma" wani irin kallonta yake saikuma yanisa yace "Abida dako shekara biyu batayi ba kokuma nace ko yayeta ba'ayibane kikema tari bama kiyi tunanin auren Fatima ba idan wani tsayayye yafito" dan gajeren tsaki taja tace "wanan batada farin jini har yanzu ko mashinshini batada shi, gwara Abida ma tun yanzu makota sun fara booking ma yaransu"

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍🏾M SHAKUR

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

EPISODE 2️⃣
_FREE PAGE_
Ganin yanda ya maida ita kaman TV yana kallo yasa tacigaba tace "Inda kaga kayan dana saya dabakai korafi ba Baban Habib Mom Afreen Pre-order collection na shiga fa, nabiya kankanin kudi tayomana order gangariyan kaya tundaga kasan waje, wallahi bantaba ganin irin design din tukwanen da flask din dana sayaba har yanzu, wasu irin designs ne nadaban dan kayan danama Abida order babu irinsu agarin nan sai agidan masu kudi, ko masu kudin ma sai daidaiku, babu abinda zancema Maman Afreen sai Allah ya sakamata da alkhairi, gashi order kaya awajenta babu tsada, farashinta nada mugun rahusa kaga kaya kaman baka akayi kyauta, jira nakema wasu kudin su shigomana mukara yo order kaya daga kasan waje daga wajenta inyaso saimu bude shago ko Rabinraina mudinga saidawa" tunda tafara maganan kallonta kawai yake cikeda takaici matarnan tasashi amatsala Babba amman kuma ko ajikinta, ita batasan rigiman dasuke cikiba sai surutun banza takemai, abinda ke kara cimai rai yanda bai iya mata fada kaman an kullemai baki. Ganin yanda yake kallonta bayako kyaftawa idanunshi sun cikada hawaye sosai yasa sai jikinta yay mugun sanyi, ahankali tadaura kanta kan kirjinshi tana shafa kan nonon shi da hannunta tace "kayakuri Baban Habibu kaji, komi lokacine zaizo ya wuce kaman ba'a yiba, kudi zaizo In sha Allahu kaji zamu biya bashin nan kanka farau, ai ba'a kanka aka faraci ba, nidai kawai na hanaka karka sake kaje kana dako salon yan gidan nan sugano mekakeyi sudinga min gori, karka damu zan maka tunanin abu kaji" gyadamata kai kawai yayi sanan yadan tureta yatashi ya zauna yana mika hannu yana daukan jallabiya shi dake gefen gadon yasaka sanan yasauka daga kan gadon, dogone fari fat kana ganinshi kasan duka yaran falon nan dashi sukai kama, Maman cema baka, binshi da kallo tayi dudda taji haushin yanda baimata abinda takesoba amman saita share tace "muje naraka bayin daganan naduba yarinyar nan naga girkin" baice mata komiba Hijabi tadaura kan daurin kirjin dake jikinta suka fito tare, matan gidan na tsakar gida tana fitowa tawani dagakai kaman bata gansu ba tabi bayanshi da sauri dan yamata nisa kanshi akasa bai masan ko akwai mata a tsakar gidan ba danshi baya kallon matan wasu yay hanyar bayi itakuma kawai sai tai kitchen koda ta shiga gani tayi Abida ma tayi bacci itakuma Fatima na fifita wutan wutan daya kama dan har sanwan ma natafasa bama tasan an shigo kitchen dinba sai fama takeda wutan idanunta sunyi jajir sabida hayaki, balla mata harara tayi tace "inkin gama ki fifita wutan kije ki kwantar da ita adaki" kai kawai ta gyadama Maman nasu dan batason tace wani abu takara kwafta mata zagi, juyawa tayi zata tafi saikuma kawai tai tsaki tazo ta bayanta tace "bani y'ata" takai hannunta zuwa saman kirjinta zata kwance zanin runtse idanunta tayi amugun firgice hakan yasa Mama ta tsaya tana kallonta da mugun ban haushi saikuma ta dakamata tsawa tace "dalla kwantomin y'ata kina rurrufe idanu kaman mai surkulle" har wani ajiyan zuciya ta sauke tace "uhn to" sanan ta kwance Mama ta karbeta suka fita itakuma tacigaba da girkin.

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_
Chapter 2 · 0% Book details