Sashe 69
Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Afalo yasami Granny da Abban shi Ammi na kitchen dayar aikinsu yace "mutafi" gaba yayi suka biyoshi abaya suka shiga mota yajasu har zuwa unguwan su Baba, har kofar gidansu sukai parking dukansu su ukun suka iso, daidai lokacin wani yaro yafita daga gidan da sauri Granny ta tareshi tace "kai jekace ana sallama da Malam Muhammad" da sauri yaron yace "Baban su Habib"? Gyadamai kai Dr Imam yayi yaron yajuya da gudu yay cikin gidan, ba'a wani dauki lokaci ba saiga Baba yafito yaci gayu abinshi yay kyau kaman bashiba yana sanye da jallabiya fara mai kyau yar kanti, ganin Granny yasa yabude idanu cikeda mamaki yakaraso wajen yace "Hajiya, marhaban dasu lale" murmushi sosai Granny tamai tace "Malam Muhammad daman rai kan ga rai" dasauri yace "aikona kiraki baya shiga" anatse tace "wani ciwo nayi da aka hanani amfani da waya kwata kwata" "assha Allah sawake" yay maganan yana bama Abba hannu yana kallon Dr Imam irin kallon bana gayamaka karka kara zuwa gidana ba, ganin kallon yasa tace "jikana kenan Imamu, ga mahaifinshi nan" tanuna Babanshi tace "dashi da kanninshi na Abuja saikuma yata dake UK ne Allah kadai yabani aduniya, wanan ma a Abuja suke ai katuna lokacin yanda nake yawan zuwa Abuja basu wani dade da dawowa kano ba, asibiti babanshi yabude anan, idan kuma ina Abuja ina gidan kanninshi ne kasan anhanani zama ni kadai sabida ciwo" gyadamata kai Baba yayi saikuma ya murmusa yace "bismillanku ai bana barku anan tsaye ba" yay cikin gidan suna biyedashi har zuwa falonsu da babu kowa gashinan agyare kaman yasani yanzun nan yagama gyarawa dan ya tsani datti yara kuma duk sun tafi aiki banda Abida dake bacci da mamanta adaki, Granny ne tabishi tashiga falon Abba da Imam suka tsaya kasancewansu maza dole sai anbasu izinin shiga ai zasu shiga, da sauri Baba yadaga labulen yace "ku shigo dan Allah" sallama Abba yayi yashiga tareda Imam suka sami waje suka zazzauna shikuma Baba yashiga ciki da sauri yadan daddaki Mama dake bacci tana sanye da doguwan riga yace "tashi Ruka munyi manyan baki" da sauri tanude idanunta ta kalleshi, murmushi yamata yadauki hijabi yabata yace "Hajiya ce data taba bani achaba nai aiki aikin ganeta lokacin damuna amarya dani dake da Fateema muna zuwa wajenta" daure fuska tamau tayi tace "Baabar Fatima" da sauri yace "eh" kwafa tayi tanunashi da yatsa tace "saura inga anmaka maganab Fatima kafadi abinda bai kamata ba" daure fuska yayi yace "nace kidenamin maganan yarinyae nan" murmushi tayi tareda sauke ijiyan zuciya ranta fess ta karbi hijabi tasaka sanan ta sauka dagakan gadon, suka fito falon Mama tana kwasan pure water a hannu cikeda kunya kaman na gaske Mama tace "wanake gani haka Baabar Faty ido kanga rai dama" murmushi Mama tamata tace "Rukkaya" anatse tace "naam ina wuni ina gajiya" sanan ta gaida su Abba tace ga ruwa kusha duk sukace sun koshi sun gode akai shiru, sanan anatse Granny tace "Malam Muhammadu wata maganace muhummiya takawoni wajenka" anatse ya gyara zama yace "too too ina jinki Hajiya" gyara zama glass din kan idanunta tayi dake karamata karfin gani sanan ta kalli Baba takoromai bayani tundaga farko har karshe wanda Imam yafadi mata sanan tanisa tace "dudda abinda su mutanen lagos suka bama Imamu labari kace bakason yarinyar, da still yanda kafadima Imamu shima dayazo nemanta saisa nima natako takanas takano dannazo naji da kunnena dan yanzu ahak yarka na gidanmu babu lpy, kuma ayanzu babu abinda yarta ke bukata irinku iyayenta after wahalan rayuwa datasha ayan watannin nan na kimanin watanni shidda dabata gida koba hakaba" tunda tafara magana take kallon Baba ganin yanda ranshi kenan abace yay kini kini darai daga fara ambaton sunan Fatima datayi harta gama, kasa magana yayi Granny tace "kayi shiru" cikeda rage murya trying to suppress his anger yace "Hajiya mun dade muna tare kuma kinsan inajin magananki, amman kinga wanan yarinyar dakike magana nifa ba y'ata bace, kawai nagayamiki y'ata ce sabida nina tsinceta da bomb yatashi agarinmu naganta tana walagigi akan titi, amman nidai ba y'ata bace" da sauri Granny tace "mekake cewa hakane? Idan bakaine ubanta ba waye uban nata Malam Muhammadu? Kamannin dakukayi da itafa"? Cikin dan fushi yace "kama ai ta Allah ce, nataimaka mata nabata abinci nabata sutura tun tana yar tatsitsiya aikam zata iya kamadani, ni Wlh Hajiya ko kadan banson inji kina ambaton sunan yarinyar nan jinake raina yana baci matuka, ni Fatima ba y'ata bace aikoshi wanan yaron" yanuna Dr Imam, "dayazo neman aurenta cemai nayi niba ubanta bane yaje chan yanemo ubanta yabashi aurenta babu ruwana alamarin yarinyarnan bansan komi nataba, bankuma son komi nata" yanda yake hargowa kaman ba salihin mutumin datasani kwanakin bayaba dako magana bayayi mai kunya yasa itama ta tsinke dama Allah yahore mata iya fada, tace "dubanni nan da kyau Muhammadu, kabar ganina da karamin jiki ko d'ana nabiyu kanin wanan....." tanuna Abban su Dr Imam, tace "koshi ya girmeka, ahaihuwa nayi kaman ka, biyu dan bakada wani babba anan dazai tsawatar maka toni na isa, ka saurareni nan dakyau, koda wasa karka sake furta abinda kake fadi, yarka ba yar iska bace, bayar shaye shaye bace ballema ace wani mugun hali takedashi yasa ka tsaneta, a'a, salihar yarinya, baiwan Allah ga dumbin ilimi both na addini da islama ne kakema haka kana cewa ba yarka bace, watakeda shi? Bakuda kowa anan garin, kauyenku gabaki dayama ya bombe kowa yamutu sanan kace zaka wulakanta yarinya, kamaida y'a namiji sabida karufama kanka asiri bayan kasan koyin da Ma'aiki rasulu yahana haramun ne abinda kayi, yanzu kuma an samu an ceto yarinya kuma kace bazaka karbeta ba itaba yarka bace, kaza kaza kaza, wlh kaji tsoron Allah, hakkin marainiyan Allah nan bazai barka bacci ba" tashi Baba yayi idanunshi sunyi jazur yace "hajiya tundadai nabaku girmanki baki bani nawaba kitashi kibarmin gida" dasauri kowa na falon ya kallai, Abba zaiyi magana Granny tadagamai hannu tace "karka sake kasa baki anan barni da fitsararren yaron nan" tajuya ta kalli Baba tace "baza'a fitaba ka daukeni ka fitar dani nace Muhammadu inka isa, kadaukeni kafitar dani inka isa kaji" tai maganan tana kumfan baki itama, baba dayaga tafishi iya hauka saiya koma yazauna tace "kuma anjiman nan zanzo dakaina nadawo maka da yarka, ta zauna akarkashinka" wani kallo yama Mama yace "Hajiya barganin kin taimaki rayuwata, ko Allah ma yasan I appreciate duk abinda kikamin saidai wanan ba huruminki bane, kuma wlh wlh wlh kinda kindaiji rantsuwata sau uku ko, na rantse miki da girman Allah duk randa kokuma ince duk randa yarinyar nan zata taka kafa gidan nan saina koreta saikuma namata illa, Fatima ba y'ata bace, bansonta, bankuma kaunar ganinta har abada, yarinyar nan is nothing but a bad luck, ta lalata rayuwana yanzu da bata rayuwa tamin siga ina aiki, dan haka karki tunanin kawota ma dan wlh ko kafa bazata saka adakin nanba, nafada nakara niba ubanta bane, niba ubanta bane, niba ubanta bane, duk yanda zakuyi da ita kuyi ai bance kowa ya riketa ba, itama yarinyar nafadi mata niba ubanta bane, harnabar duniya banson kara ganin Fatima arayuwata, tajechan duniya tayi duk yanda tagadama da ita, ta tagaiyara, ta kaskance ta wulakance niduk ba damuwata bane yarana biyar maza hudu mace daya wacce take abida su kadai garen" yafada rai abace dayasa jikin Granny sanyi, takai hannu tashare hawayen daya zubomata tasake kallonshi tace "to kasha kuruminka indai inada rai, sanan indai yaran nan nawa na nan, kagansu nan da Muhammad, da Iburahima na Abuja dakuma Aishata ta UK inhar suna raye kodani bana raye wahalan Fatima yazo karshe namaka alkawarin nan, xamu maida Fatima mutum, Fatima zata koma zatai makaranta, zata zama wani abu zakazo zaka cije yatsa sanan zakai dana sani, kadaice Fatima ba yarka bace ko"? Dasauri Baba yace "nafadi nasake, zankuma kara yanzu, Fatima Zara'u ba y'ata bace, karkuma tasake amfani da sunana as surname dinta, niba ubanta bane ehe" murmushi irin mai ciwon nan tayi tace "shikenan, Alhamdulillah natako da kafata nazo naji da kunnena, lawyer na zaizo harnan gidanka yanzun nan yabaka paper kai signing cewa kaiba ubanta bane, dagayau nine uban Fatima, custody dinta yadawo wajena, rayuwace zaka gani Malam Muhammadu" tamike tsaye azuciye ta kalli su Abba da jikinsu yay sanyi tace "kumutashi mutafi" tashi duk sukayi, Granny ta kalli Mama datai dariya tace "ke y'a mace ce, kuma kituna d'a nakowa ne, thank God kinhaifa" dasauri Mama tatashi tace "ahhhh nanfa daya tunda kuka fara abunku kinji nasaka muku baki? Nime ruwana dakike neman yima yarana baki ba gaira ba dalili hajiya haduwan kan titi" dasauri Imam da tuntuni Baba kehanashi magana yace "Granny let's go pls" tabe baki Mama tayi tace "yoo kuyi zancen ku chan ni bani aciki, uba yace ba yarshi bace mekikeso nayi? Yarana ma kadai sun isheni balle nakara da wata daba yar mijina ba" Granny zata kara magana Abba yakamata yawuce yafita da ita Imam yamare musu baya, suka bude bayan mota suka sakata Granny tafashe da kuka sosai, Abba yahsiga baya yana lallashinta, Dr Imam kuma yakoma gaba yaja motar.
Cikin kuka Granny tace "what a cruel world we live? How can a father abandon his 19yr old daughter haka da yanzu tana tender age idan ba'a kulada tarbiyanta ba anything can happen eh? Wanan wani irin abune, giyan wake yasha ne komene, wlh xan nunamai waye ne, har abada bayi kara ganin yarinyar nan, Muhammadu kiramin lawyer mu kabashi sako yaje gidan" babu musu Abba yakira lawyer danshima ranshi abace yake yabashi sakon saida yagama tass sanan tashare hawayenta tace "Muhammadu da yarinyar nan zan koma Abuja tai zamanta dani awajen nasaman mata University tafarayi" faduwa sosai gaban Imam yayi, Granny tacigaba tace "banmaso ta cigaba da zama agarin nan ballema taji tanason zuwa ganin ubanta, zaisha mamaki wlh" gyadamata kai Abba yayi yace "hakan nada kyau, zan kira Ibrahim muyi maganan" babu wanda yakara cewa komi a motan buni buni tana share hawayen datakasa denayi tsabagen tausayin Fatima har sukakai gida.
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
Cikin kuka Granny tace "what a cruel world we live? How can a father abandon his 19yr old daughter haka da yanzu tana tender age idan ba'a kulada tarbiyanta ba anything can happen eh? Wanan wani irin abune, giyan wake yasha ne komene, wlh xan nunamai waye ne, har abada bayi kara ganin yarinyar nan, Muhammadu kiramin lawyer mu kabashi sako yaje gidan" babu musu Abba yakira lawyer danshima ranshi abace yake yabashi sakon saida yagama tass sanan tashare hawayenta tace "Muhammadu da yarinyar nan zan koma Abuja tai zamanta dani awajen nasaman mata University tafarayi" faduwa sosai gaban Imam yayi, Granny tacigaba tace "banmaso ta cigaba da zama agarin nan ballema taji tanason zuwa ganin ubanta, zaisha mamaki wlh" gyadamata kai Abba yayi yace "hakan nada kyau, zan kira Ibrahim muyi maganan" babu wanda yakara cewa komi a motan buni buni tana share hawayen datakasa denayi tsabagen tausayin Fatima har sukakai gida.
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._