Sashe 71
Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sundanyi nisa sanan tadauki ledan wayan tabama Granny ahankali tace "Baaba Ya Imam yabani" dasauri takarba tace "masha Allah menene aledan" tai maganan tana cirowa daga kwalin Samsung wayace mai kyau A72 sabuwa gal, murmushi Granny tayi tana bata back tace "iyye Yaya Imamu yasaima y'ata waya, to akashe lafia enjoy your phone, bansan ko kadan ina ganin damuwa kan fuskarki kinji" tai maganan tana kamo kanta tareda daurawa kan cinyanta tace "kwanta" kwanciya tayi ahankali, Granny tashiga shafa kanta tace "zan rikeki amana Fatima, nine mamanki nine babanki, banson komi kina boyemin kome kikeso komeyake damunki kidinga fadamin, I mean komenene kinji, banson ina ganinki so sad, kinga inda zamu gidan Ibrahima ne matarshi nada kirki sosai kuma tanama fita aikin ta, shi datake rikakken dan bokone yara biyu kacal ya haifa, first yaronshi is just 15yrs old yanama boarding house, SS2 yake, sai yarshi tabiyu tanada 7yrs Amna ita kuma tana primary six ta iya surutu, so you will not have any problem with them, idan mukaje ma bakison gidan inada my own personal house dina saimu koma, dama Doctors ne suka hana ina zama nikadai sabida ciwukana, ga diabetes, ga hawan jini, gakuma asma, saisa nake zama da yarana but yanzu ma naji sauki sosai Dr's din UK na sun iya aiki I hardly have attack yanzu, so I want you to be happy, idan kina murna nima I will be fine hankalina ya kwanta nasan cewa ban tauyeki dakomiba, muna kaiwa zankira telana adinko miki kayayyaki kala kala, zamu fita shopping, muje dunes kisai jakunkuna da takalma da gyaluluwa sabida ki shirya fara school kema ki shiga cikin yaran manya ki more yanmatakan ki kaman kowace yarinya of your age kinji" gyadama Granny kai tayi ahankali, fuskanta Granny tashafa tace "to yimin murmushi mana Zara na" batason matan tadamu hakan yasa tamata murmushi bako karamin Dady Granny tajiba haka tadinga mata hira har bacci ya kwasheta Granny na shafa kanta tana kallon fatarta tace "suna isa kaduna zata mata order su scrub glow oil dasauran kayayyakin Glow & Go naturals, sabida hasken fatarnan nata dayadan dishi yafito tadawo da kyanta gashinta zatakaita saloon gobe awanke ayaryada mata kitso, zata gyara yarinyar nan this is just her promise zata zuba kudi ajikin yarinyar nan zasuga yanda yarinyar nan zata dawo, saima tafara makaranta tafara ganin yanda sa'onninta ke gayu sosai zata kara kilewa ne.
Saida suka shiga Abuja sanan Granny ta tadata tace "tashi ki kalli Abuja" tashi tayi tajuya tana kallon waje ta glass harsukakai wani anguwa locust agaban wani dankareren gida dayamafi nasu Imamu girma taga sunyi horn, aduka yaranta Baban su Imam Dr nema wanda baida kudi sosai dudda yanama mallakin private asibitin kanshi, gateman taga yafito yana ganin Granny yakoma ciki dagudu yabude kofa suka shiga cikin katafaren gidan, daidai anbude kofan flat wata cute yarinya fara sol tafito tana sanye da short gown nayara, hannunta rike da sweet mai tsinke tanasha tana hango Granny tabuga uban ihu. "Mummy Granny is here" sanan tataho da gudu tana tsalle. "Oyoyo Granny, oyoyo grandma" daidai lokacin Granny tafito tabude mata hannu aiko yarinyar tadaka tsalle sai jikinta ta kankameta tace "Granny am happy u are back, what did you bring for me" tai maganan tana kallon Zara data fito daga mota, murmushi Granny tayi tace "many things, ya akayi aka miki tsifa rabi akabar rabi"? Kaman zatai kuka tace "Granny tsifan Mummy zafi naki wlh babu" dariya Granny tayi tace "to gobe zan miki saina bada dukanku dakeda Anty Zara akaiku saloon" dasauri yarinyar tace "who is Anty Zara Granny" nunamata Zara dake gefenta tayi tace "ga Anty Zara nan" ware manyan idanunta tayi tana kallon Zara data kakalo murmushi tasakinma yarinyar tace "Granny is she from the Arabs irin na makka damuka je? She looks like them, is she from there"? Dan dariya Granny tayi tace "no she's not from there she's from Maiduguri" baki tabude zata sake magana sukaji murya. "Can you please allow my mother to rest and go to your own mother" yanuna kyakkyawan matar dake kusada shi da akalla zatai 38 ko 39 tana sanye da hadaddiyar atampa tana murmushi, dariya duka akayi banda ita data turo baki tasaki Granny ahankali takama hannun Zara tarike tace "then I will go to my Anty Zara" zuwa mutumin dazaiyi 57 yayi ahankali ya rungume Granny, ahankali yace "welcome home sweet Mum" itama matarshi har kasa taduga tace "barka da zuwa Hajiya, munyi kewanki sosai wlh" dagota Granny tayi tace "how are you Mariya" ahankali tace "fine" kana ganin yanda suke kaga educated couple, har kasa Zara ta tsugunna tace "ina yininku" da sauri Maman Amna tadagota tace "you must be Zara right" gyadamata kai Zara tayi ahankali, fuskarta tashafa tace "welcome, feel at home kinji, take me as your Mum and Dady as your Father" tanuna Baban Amna, sanan tace "let's all go inside and eat, Hajiya namiki fankasau na alkama da miyan taushe" shiga flat din sukayi, yahadu iya haduwa gawani hadadden kamshin turare dake tashi daga dakin, duk sukai dinning while mai gadi na kwasan kayan Granny zuwa side dinta, zama sukayi mijinta tafara zubama abinci sanan tazubama Kaka finkasau din data mata, ta kalli Zara tace "Zara mezakici ke" akunyace kanta akasa tace "anything Mum" murmushi daga Granny har danta Ibrahima sukayi, ita kanta saida Maman Amnan taji wani bala'in dadi yanda takirata tace "alright daughter bari nazuba miki abinda zanci ba boring abincin Granny ba" dariya duk sukayi Granny tace "oho dai" ta kalli Amna daketa kallon Zara da kanta ke kasa tace "kekuma lafiya kiketa kallon diyata" murmushi yarinyar tayi tace "Granny wlh I like her, this Anty Zara" duk dariya akayi Zara tadago kai ta kalli yarinyarnan hakanan taji tanason yarinyar kodan batada kanwa mace data girma hakane oho, da hannu tamata alamu tazo hakan yasa ta taso dagudu tabar kujeran datake kusada Mumy ta tazo wajen Zara tazauna hannunta Zara takama tarike tana kallonta batare datace komiba, Amna tace "Granny maisa bata magana wai" Granny dahar tafaracin abincinta tace "kinga haka take Amna, ni aikinma dazan baki kenan kidinga koya mata surutu dan Allah" daidai nan Mumy tamikoma Zara abinci a plate, hadaddn jollof rice da salad ne agefe sai pepper chicken, karban abincin tayi anatse sanan tace "nagode Mum Allah ampana" hakanan gabaki dayansu saida ransu ya sosu da yanda tai godiyan tabasu tausayi saidai suka daure babu wanda yanuna mata, Mum ta kalli Amna tace "small Madam keme zakici" turobaki tayi ashagwabe tace "nina Anty Zara zamuci tareko" gyadamata kai tayi tadauki spoon dinta tabata sanan ita tadauki wani duk akai shiru aka faracin abincin, dudda batada apatite but surutun Amna da yanda taketa wasa tana raba musu abincin yasa suka cinye tass, Dady ne yafara tashi yatafi falo, Granny ma tawuce yarage Mum ce kawai dasu a dinning din tashi tayi ahankali ta kalli Amna dake kallonta, adan hankali batare dakowa yajiba tace "where's kitchen Amna"? Kofar kitchen dinsu Amna tanuna mata hakan yasa ta shiga tattare plates din dasauri Mum tace "mekikeyi daughter" ahankali tace "zan kai kitchen ne" baki Mum tabude zata hanata Granny tace "Mariya ba'a hana d'a aiki, Zara ba bakuwa bace tazama yar gida" murmushi kawai Mum tayi batasake cewa komiba, Zara ta tattare plates din zata kwasa Amna tamika mata hannu tace "nima Anty Zara" guda daya tabata sanan suka wuce kitchen suka ijiye kafin sukara dawowa lokacin Mum tagama ta sake hade plate din tawuce dasu, Mum kuma tawuce falo, sanan tasake dawowa itada Amna ta gyara dinning din tass kaman ba'aci abinci akaiba sanan tawuce kitchen Amna nabinta kaman bindi tashiga wanke wanke......